[Book] Akan So Complete by Lubna Sufyan

Akan So

Title: Akan So

Author: Lubna Sufyan

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 859KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Dauki sabon littafin marubuciya Luban Sufyan mai suna "Akan So" complete dinsa. Hausa novel ne mai dauke da soyayya zallah.

Book Teaser: Coffee dinta take hadawa hankalinta a kwance tana kallon NTA don tana son shirin da MTN suke yi na tabo rayuwar mutane. 

Yarinyar data fi burgeta "Yusra fari" ta karbe show din da fadin. 

"Yau muna samu wata wasika ne datai matukar bamu mamaki ta kuma taba zuciyarmu. 

Bamu taba cin karo da abin mamaki ba irin wannan"

Hankalinta ta sofi ta mayar kan t.v din tana cakuda coffee dinta da cokali. Aka soma karanta wasikar kamar haka:

*NEMAN MOH DA GAGGAWA*

*Kai babana ne!!!*

Bansan abubuwa da yawa ba akanka.Nadai san sunanka Fu.ad. Kuma kai dan wasan kwallon kafa ne saidai bansan ko wanne club ba.

Sannan da jimawa kana shaawar wasannin mota na stunts. Mutane suna kiran ka Moh.

An gayamun bakasan dani ba. Ancemun zan fahimta wata rana.

Ni nawa mai sauki ne.

Wannan shine : shekarata goma sha biyu. Mutuwa zan.

Nasan mamata ba zata taba jin dadi ba. Inaso inganka kamun in mutu.

Wata rana zata gane. Har yanzun tana sonka sosai.

Also Download: Alkawarin Masoya Complete by Rukayya Ibrahim

Moh idan ka karanta wannan dan Allah ka dawo. Ba ma saika zama babana ba. Ba saikace kana so na ba ko kabani hakuri.

Kawai kazo kaganni. 

Ina jira amman banida lokaci sosai.

*Nana*

*

Ana gama karanto wasikar mug din coffeen dake hannunta ya subuce ya fadi ya ko tarwatse ko ina na kitchen din.

"Nanaaaa..........."

Sofi ta kwala mata kira cikin tashin hankali.

Ji tayi kafafunta basu da kwarin daukarta. 

Tsugunnawa tai ta jingina da locker din kitchen din tana maida numfashi.

"Ya Allah! Me nana taje tayi ne?"

Ta furta a fili.

"Mumy.......

Ta juya ta sauke idanuwanta cikin na nana data kira sunanta da yanayin tambaya da shakku.

Kallon ta take sosai. Jeans ne a jikinta blue sai riga itama blue mai haske. Kanta sanye da hular data lillibe askakken kanta.

Duk da ramar da tayi sosai. Bai hana kyawun nan nata fitowa ba. Hawayen dake cike da idanuwan ta ya zubo.

Lkaci daya sofi taji zuciyarta ta karye. Hannu ta mika ma nana alamar taje.

A hankali ta karasa ta rike hannunta sannan ta zauna kusa da ita.

"Nana zaki bata kayanki. Tashi kigani na zubda coffee a wajen"

Kaman bata ji mai tace ba ma ta riko hannunta.

"Mumy kiyi hakuri. Kawai ina so ingan shi ne ko sau daya"

Sauke ajiyar zuciya sofi tai tana kokarin tarbe hawayen dake zubo mata.

Ta ina zata fara ce ma Nana tun wata biyu da haihuwarta tai kokarin nemo Moh amman a banza.

Ta gaji ta hakura. Haka ma da yanzun shi ne karshen zatonta akan samun saukin Nana din.

Bata san duniyar da yake ba. Bakuma tasan inda zata nemo shi ba. Haka ta yanda zata soma gaya ma nana.

"Nana bana son ki daga zatonki akan nemo shi ne. Karkizo ba.a ganshi ba"

Hawayenta nana ta goge sannan tai mata wannan murmushin dake siye zuciyar mutane.

"Ko ba a ganshi ba. Bazanji kaman banyi kokarin nemo shi ba"

Murmushin sofi ta mayar mata hadi da fadin.

"Badai naso ki kwallafa rai. Oya tashi daga cikin coffee din nan. Ki wuce ki sake kaya ki kwanta."

DOWNLOAD BOOK{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post