[Book] Alkawarin Masoya Complete by Rukayya Ibrahim

Alkawarin Masoya

Title: Alkawarin Masoya

Author: Rukayya Ibrahim

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story, Fiction

Doc Size: 1.04MB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Download Rukayya Ibrahim's latest novel entitled "Alkawarin Masoya" or 'Lovers Promise" complete hausa novel document. Dauko shi daga wannan shafi namu.

Book Teaser: Safiya ce da misalin karfe 7:10pm Ahlin gidan tsohon minister ne, zaune Akan daining babba mai d'auke da kujeru sama da 12 karyawa suke kowa ka gani cikin shirin sa yake na zuwa aiki koh makaranta inka cire matan gidan, Abba ne zaune a kujeran daining inda ke tsakiya, zaikai Akallah  shekara 65 

sai  hajiyoyin dake zaune akan kujerun gefensa,  manyan matane masu ji da aje naira da izzah,  sanye suke cikin shiga na atamfa dukansu.

 mamu uwar gida  akallah zata kai 50 sai ummu Amarya mai shekaru 40  sai babban d'ansa Anwar d'an mamu ne  zaikai shekara 35 zaune yake cikin shigar office(doctor).

sai mai binsa shareef mai shekara 31 shima yana sanye da suit baki (lauya), sai umaima dake sanye cikin dogon rigan kanti da gyelen sa, daga kaga irin wankan ta kasan yar jami'a ce, zata kai shekara 25 dukan su d'akinsu d'aya ne.

 sai babban d'an ummu uzaifa da zaikai 20 yana sanye da jamfa da riga da wando  na shadda, kansa babu hula(student).

Also Download: Akan So Complete by Lubna Sufyan

sai  munira mai shekara 17 sanye take da uniform tare da kanwarta zulaihat mai shekara 15 ita tana sanye da uniform, Abinci suke ci hankali kwance yayinda kujeru uku yakasance empty babu kowa akansa.

Addayiya dake zaune a tsakiyar falo ta mimmike kafa tsohowace sosai Amma jin dadi ya boye shekarun nata, sanye take da zani da riga  sai d'an kwali data aje a gefe bata d'aura ba tulin gashenta daya rine zuwa fari a bayyane,  Abinci take ci kwai ne da Arish sai tie ga bread a gefe, cin Abincin ta take hankali kwance.

Turo kofar da akayi shiya ja hankalin kattafanin su dake falon harda daining Area, duk da kamshin turaren sa ya sanar dasu wake shirin fitowa, Amma hakan bai hanasu juyawa don tabbatar wa kansu shin da uniform ya fitoh koh Ah ah.

Fitowa yayi a kofar, wow masha Allah watoh in Anace maka black is beauty, bazaka tabbatar ba sai kaga wannan Hallintar koh shakka bazakayi ba, bakine mai sheki irin bakikkirin nan, fatar nada masifar laushi har maiko-maiko fatar keyi sanye yake da wando  baki, mai roba a kasar wandon, pencil ne ya kamasa sosai bai rufe masa idon sahu ba.

sai boot fari tas baisa wa kafarsa socks ba,  hakan yasa ana kallon idon sahun nasa, t-shirt ne a jikinsa white sai rigan da ya daura akai mai hula da dogon hannu, Amma ya bude zip in wanda yasa ake kallon rigar ciki.

ga wani d'an iskan Aski dake kansa ya raruke gefe yabar sakiya da yawa, gashine mai laushi da yawan gaske irin na fulani, ga kwancecen sajensa mai hade da gemu, duk da bai cika masa fuskar ba, Amma daga gani Ana ji da gemun irin na tsiran farkon nan ne na tashe balaga.

Bakin sa pink ne mai kyau dan kankani,  hancin sa mai tsahone sosai ga idanu manya kamar na mata, kwayar idanunsa bakine sosai wanda ke matukar rikita mutune a duk lokacin da ya zare maka su yayin da mabi da kwayar ya kasance fari tas gashin giransa mai yawane  blutooth ne fari makale a kunnensa d'aya.

Yana da tsawo sosai Amma ba irin har shan innan ba, gashi da kira mai kyau duk da yanzun yake tashen sa, Amma kallo d'aya zaka masa ka gane za'ayi namiji, baxai wuce shekara 18 ba.

Taku yake irin na isasun yaran nan masu ji da lokacin su hade da kuruciya, duk da ya gansu zaune a falo, Amma hakan baisa sa ya nuna ya gansu ba nufar kofar falo kawai yayi.

Addayiya dake zaune a tsakar falo tana cin kaza da romonsa wanda yar aiki ta aje mata, ta mike kafa.

da gangan ya nufi ta saitin da take zaune kamar baiganta ba, ya d'aga kafarsa kamar zai taka kafarta da sauri taja abinta cikin masifa take kallon Lahab.

Amma yaron nan Anyi jarabebbe kai in gari ya waye baka sani surutu ba bakajin dadi, nida gidan mijina da d'ana, bani da sakat sai in baka nan, toh yau duk bala'inka bazan kulaka ba, d'an-banza kawai.

yi yayi kamar baisan ma tanayi ba tafiyarsa yaci gaba dayi.

DOWNLOAD BOOK{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post