Autan Sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero, ya Auri Mata Biyu a Rana Daya

Allah mai yadda ya so, a kuma sa'in da ya so. Yau muka samu labarin auren dan marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Autan mai suna Mustapha, shi ne auta a cikin 'ya'ya 61 da marigayu Alhaji Ado Bayero ya haifa.

A jiya lahadi, 20 ga watan June, 2022 aka daura auren Mustapha da amarensa guda biyu.

In mai karatu bai manta ba, Mustapha kani ne ga Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, kazalika kani ne ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Kalli hotunan bikin gasu nan a kasa:


Allah ya sa albarka ga wannan aure.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post