Bauchi Poly ta Dakatar da Lakcara Kan yi wa Tunibu Kamfen a Watsapp

ATA Bauchi

Makarantar Abubakar Tatari Ali Polytechnic Bauchi ta dakatar da wata babbar ma’aikaciyarta, Raliya Kashim bisa zargin sa hannunta a harkokin siyasa, wadda hakan ya saba wa dokar ma'aikatun gwamnati.

Kakakin kwalejin, Maimako Baraya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Bauchi.

Mista Baraya ya ce an dakatar da Mrs Kashim ne saboda yi wa wasu dan takarar shugaban kasa, Tunibu, kamfen din siyasa a watsapp group na malaman makarantar.

Allah shi kyauta.


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post