Sharon Mbabazi, Matashiyar da ta Kammala Digirinta da Aikin Leburanci

Sharon Mbabazi

A kasar Uganda ne aka samu wata matashiya wadda ta ciri tuta ta hanyar yin digirin digirgir da taimakon aikin leburancin da ta ke.

Matashiyar mai suna Sharon Mbabazi ta yi nasarar kammala karatunta a jami'ar Mutesa 1 Royal a fannin sadarwa.

Kamar yadda ta ke bada labari, an haifeta ne a garin Masoli da ke Gayaza Wakiso na kasar Uganda. Kuma mahaifinta 'ya'yansa biyar da mahaifiyarsu wacce ta rasu tun Mbabazi na yar jaririya.

Mbabazi ta ce ta sha fama da kalubalalluka iri-iri yayin tasowarta kasancewarta yar marasa abin hannu.

Kazalika, Mbabazi yar shekaru 22 ta matukar shahara a wurin da ta ke aiki, inda a kullum ta ke hada bulo siminti dari takwas zuwa dubu. 

Yayin da manema labarai ke zantawa da ita, ta bayyana musu cewa ita babban mafarkinta shi ne ta zama mai gabatarwa a gidan talabijin.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post