FG ta yi Alkawarin Gyara Wutar Lantarkin Jihar Borno Nan a Makonni 6

Zulum

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa nan ba da jimawa ba za a maido da wutar lantarki Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da mataimakin shugaban jami’ar jihar Borno, Farfesa Umar Sandabe ya jagoranci tawagar gudanarwar jami'ar a wata ziyarar ban girma da suka kaiwa ministan.

Ministan, a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a Abuja, ya ce ana kokarin dawo da wutar lantarki a Maiduguri.

Ya kuma umurci Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara da ta binciko hanyoyin da jami’o’in jihar za su ci gajiyar manufofin samar da aaji na gwamnatin tarayya.

Yayin da yake ci gaba da jagorantar gudanar da ayyukan hukumar samar da wutar lantarki ta Najeriya (NESI), Aliyu ya ce ana kokarin dawo da wuta a Maiduguri.

Aliyu ya kuma kara da cewa ana sa ran kammala hakan nan da kusan makonni shida.  

A nasa bangaren, Sandabe ya ce tun a shekarar 2020 jami'ar ta kasance babu wutar lantarki a jihar saboda tashe-tashen hankula a jihar.

Mataimakin shugaban jami’ar ya ce ana gudanar da jami’ar ne ta hanyar amfani da janareta kuma hakan yana matukar lakume kudin asusun jami'ar.

Ya yi nuni da cewa, janaretoci, duk da cin makudan kudade, ba sa samar da isasshiyar wutar lantarki da ake bukata domin samar da wutar lantarki a jami’ar.

Ya bukaci ministan da ya tabbatar da cewa an maido da wutar lantarki a jami’ar sannan ya yi alkawarin cewa hukumar za ta tabbatar da duk wasu ayyukan samar da wutar lantarki a cikin harabarta.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post