Kanal Musa Shehu, tsohon gwamnan jihar Rivers da Filato ya rasu

Yanzu-yanzu mu ka samu labarin rasuwar tsohon gwamnan Jihar Rivers da Filato a zamanin mulkin soja, Kanal Musa Shehu da safiyar yau lahadi.

Kanal Musa ya rasu ne a birnin tarayya Abuja. Kazalika, za a yi jana'izarsa da misalin karfe 2:00PM na rana a masallacin unguwar yan majalisun da ke Apo, a Abuja.

Muna fatan Allahu ya jikansa da rahama, ya kai haske kabarinsa ba don halinsa ba.


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post