'Yan Kasar Ghana na Zanga-zanga Saboda Tabarbarewar Tattalin Arziki

Zanga-zangar kan matsalar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki a Ghana ta shiga rana ta biyu a daidai lokacin da jama'a daruruwa suka yi cincirindo kan tituna domin nuna rashin jin dadinsu kan halin da kasar ke ciki.

A cewar rahotanni, wata zanga-zanga ce ta kwanaki biyu karkashin jagorancin kungiyar masu fafutuka ta “Tashi Ghana,” da nufin yin Allah wadai da matsalolin tattalin arziki.

A halin da ake ciki dai an yi arangama tsakanin 'yan sanda a Accra da daruruwan masu zanga-zangar, wadanda suka fice daga hanyar da aka amince da masu zanga-zangar.

 ‘Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa da harsasan roba da ruwan zafi domin tarwatsa fusatattun jama’a, wadanda suka kauce wa hanyoyin da aka tanada domin gudanar da zanga-zangar, a cewar Arise Ghana.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post