Yanzu: Wasu Yan Bindiga sun yi Garkuwa da Dagaci da Dansa a Bauchi

Umar Sanda

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dagacin kauyen Zira, Yahaya Saleh da dansa Habibu Saleh a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya tabbatar da sace sarkin kauyen.

Ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari kauyen Zira da ke kan iyaka da jihar Filato a daren ranar Asabar da ta gabata inda suka yi awon gaba da dagacin da dansa.

Wakili ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Umar Sanda ya aike da tawagar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa yankin yayin da tuni aka umarci  DPOn karamar hukumar da ya fara bincike don ceto wadanda aka sace.

Ya ce, “yanzu haka mutanenmu suna kewayawa a cikin daji domin neman wadanda aka sace kuma muna son mutanen yankin su sani za a kubutar da wadanda abin ya shafa da ransu.

Rundunar ta kuma yi kira ga mazauna garin da su baiwa ‘yan sanda bayanai masu amfani tare da rokon jama’a da su kwantar da hankalinsu.

Harin na ranar Asabar ya kara dagula al'amura a yankin.  Mazauna garin na cikin damuwa kan karuwar satar mutane a garin Toro inda suke kira ga hukumomi da su dauki matakan da suka dace domin dakile yaduwar cutar.

Satar na baya-bayan nan dai na zuwa ne kwanaki biyar bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu tare da raunata wasu uku a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post