[Book] Yar Garuwa Complete by Hawwa Muhd Usman

Yar Garuwa

Title: Yar Garuwa

Author: Hawwa Muhd Usman

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 858KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2018

Description: Labari mai taba zuciya da tsantsar soyayya muka kawo muku. Sauke littafin marubuciya Hawwa M.U mai suna "Yar Garuwa" complete hausa novel a text document don karantawa.

Book Teaser: *S*allama take tayi tun daga k'ofar gidan,amma ko tari ba ayiba,ga rana dake dukan kanta...

 Banda maik'o babu abunda take,jin ank'i ansawa,yasa ta d'aga allonta dake hannunta ta d'ora akanta,don kare ranar da ta addabeta...

 Zuwa can ta sake maimaita yin sallamar,nanma dai shiru aka mata babu amsa....

 Hakan ne yasata tsugunawa,ta cire silifanta ta zauna akai kamar mai d'aukan darasi.....

 Tun daga nesa dattijon dake tahowa,yake kallonta,sauri ya K'arawa k'afarsa dan tabbatar da zatonsa....

 Daf da ita ya k'araso,tare da fad'in *"NANA KHADIJATU*, Uwata me kikeyi a cikin wannan ranar da kowa yake gudunta???"

 'Dagowa tayi da saurinta jin muryan mahaifinta dake tsaye,da murnarta ta kalli mahaifin nata tana fad'in "Abba na dawo ina sallama,ba a amsaba shi yasa na zauna anan ban saniba ko ba kowa a gida"....

 Banda abunki kuma uwata sai kizo cikin wannan ranar ki zauna kamar an miki dole...

 "Tashi maza mu shiga ciki,kar kuma ki sake zuwa ki zauna kinji ko,wannan ai sai wani ciwon ya kamaki"...

     Fad'in abban *KHADIJATUL KHUBRA*.....

 Hannunta ya kama suka kama hanyar shiga gidan....

Tun daga bakin k'ofar gidan yayi sallama,jin shiru ba a amsaba,yasa abban yaci gaba da kutsa kai cikin gidan had'e da sake yin wata sallamar....

Abunda ya matuk'ar bawa abba mamaki bai wuce ganin da mutum a tsakar gidanba.....

K'arasawa yayi yana k'are mata kallo,kafin ya iya furta ‘’ladiyo dama kina zaune muke sallama,amma amsawa ta gagareki‘’....

Fuska ta yatsina (tamkar kayan miyan da yaso lalacewa).....

kafin ta bashi amsa da cewa ‘’ina ji sai me??

ko kuwa cewa akayi an ajiyeni ne dan na amsa muku sallama?''......

Ganin zata kunyata shi gaban y'arsa yasa yabar maganar ta hanyar fad'in ''Allah ya kyauta''......

Bud'ar bakin ladiyo sai cewa tayi ''ya kyauta abinda yafi haka''.....

Bai kuma tanka mataba,ya juya yana girgiza kai,ya shige d'akinsa.....

Duk wannan budurin da ake a gaban KUBRA ake,kanta na k'asa sai hawaye dake tsiyayowa daga ciki......

Ganin abbanta ya bar gurin itama ta juya da niyyar barin gurin....

Sai dai muryar ladiyo ta rigata k'arasawa bakin k'ofar d'akin,ta hanyar mako mata mula²n zagi......

Da sauri ta k'arasa shigewa,gabanta na dukan 9²....

Can ku'ryar D'akin ta nemi guri ta zauna,tana jiran gawon shanu....

Cikin d'akin da baida wadataccen haske,take zaune,tayi shiru sai kalle² take tamkar wata bak'uwa,ko wacce ta fara rayuwa inda bata saniba,haka taketa fama ita kad'ai,a haka bacci yayi awon gaba da ita.......

Wani k'ayataccen guri ta hango mai kyan gaske....

Also Download: Dan Mace Complete by Hawwa Muhd Usman

Sauri take ta k'arasa gurin,amma duk da haka ta kasa k'arasawa gurin,saima gajiya da tayi......

Haka ne yasata neman guri ta zauna,tana k'arewa gurin kallo ko zata hango inda ruwa yake.....

Rashin ganin alamar ruwa yasata,juyawa ta kalli hanyar da ta biyo.....

hanyace mik'ak'kiya wacce ko farkonta bata ganiba,bare k'arshenta,hakan yasata kifa kanta ta fara rera kukan rashin Madafa....

Tun daga nesa ta fara jiyo hayaniyar mutane had'e da wani daddad'an k'amshi da yasata saurin d'ago kai,tana bin hanyar da hancinta.....

Ayarine na mutane da suke da mayuk'ar yawa suke shirin giftawa ta kusa da ita......

Da sauri ta mik'e tabisu duk da suna kan abun hawa,hakan bai hanata shiga gabansuba,tana fad'in

  "Dan Allah ku taimakamin"....

Babu wanda ya saurareta,sai zagayeta da sukayi suka ci gaba da tafiya......

Da gudu² ta sake shiga gabansu,tana rok'onsu.....

Wannan karon kam saboda haushi da ta bawa wasu daga cikinsu yasa su yi mata tsawa....

A firgice,jikinta har rawa yake saboda tsoro take kallonsu,wani k'ato da yayiwo kanta d'auke da bulala yasata fara kuka....

tana bashi hak'uri,d'aga bulalar ya d'aga da niyyar sauke mata a jikinta......

Kafin ya k'arasa ida nufinsa,wata siririyar murya daga bayansa take fad'in kada ka kuskura ka aikata abunda kake k'ok'arin yi .....

Da hanzarinsa ya juya don ganin mai magana,sai dai ganin fuskar wanda yayi maganar yasa shi kaucewa daga kusa da ita,jikinsa na kad'awa tamkar Mazari.......

Kyakykyawan matashi ne ya bayyana daga inda ya kauce,yana sanye cikin fararen tufafi,tafiyarsa cike da k'asaita,har ya k'araso Inda suke.....

Kallon k'aton yayi kafin ya bud'e baki,har ya rigashi cikin ladabi da girmamawa yake fad'in ''tuba nake ranka ya dad'e''......

Hannu ya d'aga masa,ba tare da ya sake yunk'urin yin maganaba,ya juya da nufin barin gurin............

DOWNLOAD BOOK

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post