Allah ya yi wa Mai Gadin Kabarin Annabi Rasuwa a Birnin Madina

Agha Muhammad Habeeb Al-Afari

Wani bawan Allah, wanda ke gadin kabarin fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (S.A.W) ya rasu yau sha uku ga watan yuli, 2022.

Agha Muhammad Habeeb al-Afari na daya daga cikin tsofaffin masu gadin masallacin madina. Haka kuma shi yana daga cikin masu gadin kabarin annabi (S.A.W).

Kamar yadda shafin Haramain Sharifain ya wallafa a dandalin sada zumunta na Facebook, za a yi jana'iyar Agha Muhammad bayan magriba a masajidul Nabawi.

Allah ya jikansa.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post