[Book] Bintu Diyar Bayi Ce Book 2 Complete by Khadija Sidi

Title: Bintu Diyar Bayi Ce Book 2

Author: Khadija Sidi

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 93KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Khadija Sidi mai suna "Bintu Diyar Bayi Ce Book 2" complete hausa novel a text documen daga shafin nan namu.

Book Teaser: Daga cikin Masallaci aka fara abinda ya had’a jama’a a

wannan masarauta, wato d’aurin aure, in da aka umarci

waliyin Ango da Amarya su matso kusa. Waziri ne ya fito daga

6angaran Sa’ayrasa, Fabarusa kuma Sarki Abdulrahaman ne

ya nuna kan sa a matsayin waliyi.

Daga waje Khalil ne ke ta yiwa Yarima Barde hira, amma shi

ina hankalinsa na ga Gimbiya K'amariyya, Allah Allah ya ke a

shafa fatiha ya tafi garera don jin soyayyar ta ya ke har ransa,

bare kuma yau gabar da ke tsakanin Masarautasu za ta kau, za

su yi soyayyarsu a zahirance ba tare da wani shakku ba. Jin an

shafa fatiha Yarima Barde ya tashi ya na mai fad’in.

‘’Alhamdulillah tunda an amra sai ku tashi mu tafi ko?’’

Har Khalil da Jafar sun tashi, tuni su ka tsaya cak jin marok’a

na fad’in

‘’An d’aura auren *Yarima Abubakar BARDE* tare da *Gimbiya

Fatima* akan sadaki (50000 CFA)"

Yarima Barde da sam bai lura da abinda su ka ji ba tsabagen

hankalinsa ba ya wajan, a hasale ya kai kallonsa ga

abokannasa ya na mai fad’in

‘’Me ku ke jira ne? Mu tafi, Allah Allah na ke na gana da

Gimbiyata.’’

Su kuwa marok’a ba su fasa shela ba. Khalil ne yayi k’arfin hali

ya ce

‘’Da ma kai ne Barde?’’

Cikin rashin fahimta Barde ya ce

‘’Ni ne wa?’’

‘’Angon da aka amrawa amren.’’

Jafar ya bashi amsa a tak’aice. Kai Yarima Barde ya girgiza

cike da murmushin irin ban son rainin hankali fa. Khalil ya ce

‘’Saurara ka ji Barde’’

Nan kuwa muryar wani marok’i da ya zo giftawa ta dafda su ya

doki kunnan Barde, fad’i ya ke

‘’An amra auren Yarima Abubakar Barde da Gimbiya Fatima....’’

Nan ya ya tsaya cak tamkar wanda aka zarewa rai, su kansu

abokannasa sun girgiza kwaran gaske.

Daga cikin masallaci, ana gama d'aurin auren, inda kowa ya ke

mamakin sauyin al’amura da aka samu, musammam jama’ar

Sa'ayrasa, shi kuwa Aisar tunanin hanyar fita daga cikin jama’a

yake, domin zuwa neman Bintu ba tare da Junaidu ya ankare

ba. Bayin Sa'ayrasa ne d’auke da farantin goro da alawa, su ke

bin kusirwa kusirwa in da suke mik’a farin tin jama’a na d'iba

san ran su.

Bawan da ya zo kusurwar da su Aisar su ke, Aisar ya fara

mik’awa, in da ya girgiza masa kai alamar ba ya buk'ata, har

bawan zai wuce, nan idanun Aisar su ka sauka bisa yatsun

bawan, me zai gani? Zobensa da ya bawa Bintu ne cikin

yatsun na shi, bai ankara ba sai ji yayi Aisar ya damk’o

hannunshi, a tsorace bawa ya saki farantin hannun sa dan ko

shakka babu ya san tawagar shugaban k’asa ne

gabansa.Hakan ya dawo da hankalinsu Junaidu da sauran ‘yan

tawagar garesu. Aisar na mai duban idanun bawan ya furta

‘’Ina ka sami wagga zo6en? Menene dangantakarka da mai

zo6en? Ina Bintu d’iyar bayi?’’

Babban gida kuwa 6angaran Jakadiya, Bintu na zaune tare da

su Jakadiya sai ga Gimbiya K’amariyya ta shigo, ta yi kyau

kwarai cikin jajayen kaya, ta d’aura alkyabba ruwan zuma bisa

kayan, ga bayi nan biye da ita. Ta zo kar6ar mabudin wajan aje

baki na musammam domin kar6ar Yarima Barde.

Ta na zaune ta na jiran Jakadiya ta shiga ciki dan d’auko mata

mabud'in, su ka ji an shigo 6angaren Jakadiya an gud’a. Tuni

hanjin cikin Bintu ya kad’a don kuwa ta san ta faru ta k’are an

yiwa mai dami d’aya sata, aure dai an aura. Tuni ta fashe da

kukan da dama ya tsaya k’asan mak’ogaran ta.

Jakadiya ta fito d’auke da mabud’i, yayinda Ladiyo ta shigo jiki

na rawa, sai tafa hannu ta ke cikin salati da sallallami.

Jakadiya ce ta tambaya ko lafiya, yayin da hankalin kowa ya

koma gareta.

Cike da ladabi Ladiyo ta durk’usa gaban Jakadiya ta na mai

fad’in

‘’Yau na ga lafiyar Allah Maigari gauro talaka da mata hud’u.’’

Cikin k’aguwa Gimbiya K’amariyya ta ce

‘’Me ya faru ne Ladiyo?’’

‘’Wato Allah shi taimaki Gimbiya, ji da gani dai ba ya k’arewa

sai randa kurman bebe ya makance, Sarki Abdulraman na

Fabarusa cike ya ke da abin mamaki, wani lamari sai shi.....’’

‘’Yo to wani abin mamaki? Ya ce ya fasa ne?’’

Jakadiya ta tambaya cikin rashin fahimta. Kana Ladiyo ta ce

‘’Eh to ya fa fasa be kuma fasa ba, da ya tashi yin bazata, sai

ya amrawa d'ansa Barde Bintu.....’’

Hakan yayi daidai da ihun da Gimbiya K’amariyya ta kurma ta

na mai zubewa k’asa sumammiya. Nan da nan aka yi kanta.

Bintu kuwa yanda maganar ya doki kunnenta ta tabbatar ta

zama kurma, don kuwa ba ta jin hayaniyar da ake gabanta

‘’Ya amra ma d’an sa Barde Bintu....’’

Maganar da ke ihu jikin kunnenta kenan.

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete by Khadija Sidi


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post