[Book] Adade Ana Yi Sai Gaskiya Complete by Zainab Idris Makawa

Adade Anayi Sai Gaskiya

Title: Adade Ana Yi Sai Gaskiya

Author: Zainab Idris Makawa

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 1.1MB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Ku dauka tare da sauke sabon littafin marubuciya Zainab Idris Makawa mai suna "Adade Ana Yi Sai Gaskiya" complete hausa novel document daga shafin nan yanzu-yanzu.

Book Teaser: School bus din St Paul's High School ya tsaya daidai bus stop din Sarita Vihar, Yanmata biyu suka sauko daga bus din, kallo daya zaki musu ki san cewa 'Yan Makaranta ne, sanye suke da Uniform doguwar riga wanda da kadan ya wuce guiwa, ko waccen su rik'e take da Jakkar makarantar ta (School bag) da kwandon Abincintab(Lunchbox) wasu daga cikin 'yan Bus din suka lek'o ta Window suka ce da yanmatan da aka sauke "Alvida Kaveri, Alvida Najwa" (Goodbye Kaveri Goodbye Najwa), Kaveri da Najwa su ka daga musu hannu suna Murmushi har Bus din ta k'ule da ganinsu, da6i'ar su kenan, duk wacce aka sauke sai an mata wak'ar bankwana.

Najwa da Kaveri 'yan unguwa daya ne, tun suna Kg suke zuwa Makaranta tare har yanzu da suke High School 11th class. Shekarunsu ba zasu wuce Sha bakwai zuwa sha takwas ba.

Sun gangaro cikin unguwansu daidai gidansu Kaveri suka tsaya, suka rungume Juna Kaveri tace "NAJWA Kala milathe hai'n (Najwa sai mun hadu gobe)" Najwa ta kalli k'awarta Kaveri da murmushi har kumatunta na lobawa tace "Sighra Milate hai'n Kaveri (sai mun sake haduwa Kaveri)" suka dagawa juna hannu ko wannen su yayi hanyar Gidansu.

Ba tayi taku 15 ba ta isa gidansu, kamar kullum maimakon ta shiga gidansu sai ta tsaya a shagon dake daidai gidan, daga waje take k'walawa mai shagon kira "Vijay Bhaiya main bapaas aa gaya hoon(Brother Vijay, i'm back)" bata tsaya jin me zaice ba ta shigewarta gida, Lek'owa Mai shagon yayi ta windown Shagon har ta kusa shiga gida ya bude murya yace "ghar me svaagat haai Najwa(Welcome Home Najwa)".

Ta k'arasa ciki daidai k'ofar Tag ne mai dauke da sunan Babanta a jiki SADA ABU, hannun k'ofar ta murda ta shiga da Sallama, ba amsa,kutsa kai tayi inda ta san zata ga Mahaifiyarta, kamar yadda take zato hakan ne, tana dakin Yayanta gaban tamfatsetsen Hoton Yaron da ba zai wuce shekaru goma zuwa sha daya ba, ajiyar zuciya ta sauke, ta k'arasa gun mahaifiyarta tare da dafa kafadunta, firgigit ta juyo a lokaci daya ta goge hawayen da ke sintiri a idaniyarta gami da k'ak'ulo murmushi.

"Maa, kukan kikeyi kuma?" Najwa ta fada cike da damuwa, da Sauri Mahaifiyarta ta girgiza kai tana murmushi tace "Aa Najwa ba kuka nikeyi ba wani abu ya fada min a ido".

Najwa tayi murmushi bata son jan zancen tabja hannun Maa suka bar dakin, ranta ba dadi, duniya in akwai abun da ta tsana be wuce hawayen Mahaifiyarta ba, kuma tun da taso da wayonta take ganin Hawayen Mahaifiyarta sakamakon wannan hoton da ke mak'ale a dakin Yayanta.

Bayan Najwa tayi wanka ta shirya cikin kaya Riga da Wando na Indiyawa ta yana gyalen a kanta ta fito k'ofar gida wurin Vijay Bhaiya,yana zaune a cikin shagon yanabganinta ya fadada murmushinsa, ganin fuskarta yayi ba walwala, cike da damuwa yace "Kya huwa Najwa?(Meya faru Najwa?)" ta rausayar da kai tace "Meri Maa abhee bhee phir se ro rahee hai(Mamata na chan na kuka kuma)" cike da tausayawa yace "ki mein chitr abhee bhee use rona bana?(Hoton nan na sata kuka har yau?)" tace "vah hamesha ke lie jab tak vah us tasveer ko dekhata hai rona hoga(Har abada zata cigaba da kuka in dai tana ganin hoton nan)" da sauri yace"ise door le jao(to a dauke mana) tace "yah aasaan nahin hai(ba abu

mai sauk'i bane)" yace "prayatn(ki k'okarta)" ta sauke ajiyar zuciya mai k'arfi ta mik'e sannan tace "theek hai, main koshish karoonga(Okay zan k'okarta)".

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Abu Cikin Duhu Complete by Zainab Idris Makawa

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post