[Book] Alwashi (Labarin Hafsat) Complete by Ummi A'isha

Alwashi

Title: Alwashi (Labarin Hafsat)

Author: Ummi A'isha

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 515KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Ina daukacin masoyan marubuciya Ummi A'isha? Ku sauke cikakken littafinta mai suna "Alwashi" complete hausa novel document wanda ta sadaukar da shi ga marubuciya Miss Xoxo. Za ku iya daukarsa yanzu. 

Book Teaser: Gidane na marayu mai d'auke da tangamemen gate sannan ga katanga babba zagaye da gidan wanda tsawonta ma abin kallone,haka shima cikin gidan yake wawakeken gaske mai dauke da gine gine masu yawa wadanda suka hadar da ofisoshin ma'aikatan gidan da kuma wurin kwanan marayun da kuma duk wani abu na bukatarsu,

Duk inda ka hanga yarane zaune sunyi group group, masu wasa nayi sannan masu hira sunayi yayinda wasu kuma suke yan aikace aikacensu na yau da kullum,

Wasu yanmata ne guda biyu acan gefe su kadai wadanda akalla shekarunsu zasu kai shekaru 23,

Daya daga cikinsu tayi tagumi tana sanye da kodadden hijabi da wata kodaddiyar atamfa ajikinta haka itama dayar kayan jikinta duk sun gajiya,

"Hafsat wai wannan tagumin da kikayi na menene? Yau naga gaba daya yanayin naki sai ahankali tamkar wata marar lafiya..." Daya daga cikin yanmatan tafada bayan ta dafa kawar tata,

"Amina wallahi lafiyata kalau kawai dai ina tunanin makomar rayuwarmu ne acikin gidan nan, ba kasafai mutane suka fiya kulawa damu ba, hatta gwamnati tayi watsi da rayuwarmu sai lokaci zuwa lokaci take tunawa damu..." Wadda aka kira da suna hafsat tayi magana cikin karyewar zuciya,

"Amma dai hafsat wannan ai ba bakon abu bane awajenmu duba da tsawon shekarun da muka diba acikin wannan gida gashi har yau Allah bai kawo wanda zai daukemu ya fitar damu daga cikin gidan nanba ko muma mazamo yaya kamar kowa.."

Also Download: Alheri Danko Ne Complete by Ummi A'isha

"Amina kenan tayaya zamu zamo yaya kamar kowa alhalin babu wanda yasan asalinmu, Allah ne kadai yasan tushenmu dan haka kinga maganar amaida mu 'yaya ma bata taso ba.."

"Hmmm babu komai koma dai yayane Allah yana tare damu..."

"Kai yanmatan nan kutaso kuzo muje.." Muryar daya daga cikin ma'aikatan gidan marayun ta ratsa kunnuwansu wanda hakane yayi sanadiyyar katse musu hirar da suke yi,

Mikewa sukayi suka karasa inda take,

"Yawwa kuzo muje, wannan bawan Allahn ne yauma yakawo muku agaji kamar yadda yasaba..."

Batare da sunyi magana ba suka bi bayanta, gaba daya an tattaro yaran gidan antarasu wuri guda gefe kuma wata babbar motace anata sauke kaya daga kanta wadanda suka hadar da buhunhunan kayan abinci da tufafi,

Wuri amina da hafsat suka samu suka tsaya suna kallon irin uba uban kayan da ake saukewa,

Kowacce acikinsu addu'a take acikin zuciyarta kan Allah yasakawa koma wanene wannan mutumin da alkhairi domin yajima yana yi musu hidima,

Kayan da aka sauke daga kan wannan katuwar motar ba dan kadan bane domin bayan kayan abinci da kayan sawa harda barguna da katifu,

Suna nan zaune sunyi tsuru suna ganin tulin kayan da aka kawo musu har aka kammala sauke kayan nan wakilin wanda yabada kayan akawo ya mike yadanyi jawabi,

_Kamar yadda muka sani kuma muka saba, wannan bawan Allah Wanda mukafi sani da suna baya goya marayu akoda yaushe yana iya kokarinsa wurin ganin ya kyautatawa rayuwar marayu sannan kuma ya sadaukar da dukiyarsa wurin taimakon musulunci, kamar yadda nadade ina fada muku shi wannan bawan Allah matashine ba tsoho ba kawai dai Allah ne ya albarkaceshi da halin manya dan haka muyita yimasa addu'a akan Allah ya albarkaci rayuwarsa da dukiyarsa da kuma iyayensa...._

"Amin..." 

Dukkan jama'ar dake wurin suka amsa cikin farin ciki domin wannan bawan Allah ba karamin taimako yake yiba saboda kusan agarin ma shine lamba daya wurin taimakawa rayuwar marayu.

Saida aka gama rabawa marayun kayayyakin da aka kawo musu akan idon wakilin wannan bawan Allahn dake basu gudun mawa wanda suka dade da rada masa suna da baya goya marayu,bayan gama rabon kayan tsaf sannan wakilin baya goya marayu yatafi, sukuma yaran kowa ya kinkimi kayanshi ya nufi wurinda zai adana su, haka suke gudanar da rayuwarsu cikin wannan gida wanda a lokuta mafiya yawa sukan shafe sama da watanni biyu batare da sun samu wani tallafi ba indai ba wannan bawan Allahn ne ya aiko musu ba gashi kuma duk wannan hidimar da yake yi musu basu taba ganinsa ba balle har su gane kamanninsa.

***

Kamar bazai taka k'asa ba haka yake tafiya, sanye yake cikin jar t shirt mai dogon hannu yasha d'amara da jar belt wadda ke d'amare ajikin bakin trouser din dake jikinsa, duk da wai ahakan sauri yake amma baisashi sauya salon tafiyar tashi ba,bak'in face din dake idonshi yadan gyara bayan ya maida hankalinsa kan agogon azurfar dake d'aure a tsintsiyar hannunshi, kamar koda yaushe fuskarshi babu alamun fara'a atare da ita,

K'ofar da zata sadashi da falon mahaifiyarshi ya bude ya shiga fuskar nan kamar zaice wayyo Allah dan tsananin fushi,

Ganin babu kowa aciki yasashi kara yin gaba, awani tsararren falo wanda aka tanada musamman domin hutawa ya isketa, tana zaune saman kujera daga ganinta bazata haura shekaru 45 ba aduniya, farace jajur mai dan jiki, tana sanye da wani leshi mai tsadar gaske, wuyanta da hannuwanta gamida kunnenta duk gwala gwalai ne sai walwali suke, haka yan yatsun hannunta ma duk sunsha zubunan gold,gefenta kuma wata yar matashiyar budurwa ce wacce zata kai shekaru 23 tana kwance tayi tashi da cinyar matar,

Sallama yayi wadda ba lallai su iya jiba domin aciki ciki yayita,

DOWNLOAD BOOK{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post