[Book] Autar Hajiya Complete by Zee Maman Khady

Title: Autar Hajiya

Author: Zee Maman Khady

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 141KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2016

Description: Maziyarta, ku sauke cikakken littafin "Autar Hajiya" complete hausa novel document wanda marubuciya Zee Maman Khady ta rubutashi. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Kwance take kan d'an madai-daicin gadon mahaifiyarta, hannunta ri'ke da waya, kirar tecno H³ wani game take me matukar sanyata nishad'i, Ta tattara hankalinta duka ya koma kan wayar.

Muryar Hajiya ta tsinkayo tana kwalla mata kira, da sauri tasanya pause a game d'in domin zuwa kiran mahaifiyar ta.

"Hajiya gani, tafad'a bayan ta d'an rissina gabanta, Alamar girmamawa, matar da takira da Ahjiya ta d'ago ta kalleta, tace "ki shirya inaso in ayke ki yanzu, tace "ina? Tace "kije ki shirya mana koma inane ay zakiji.

'Daki tanufa ta cire kayan jikinta, tayi d'aurin kirji, sannan, tafito ta cika bokiti da ruwa ta nufi toilet.

Bayan ta she'ka wanka, tafito tanufi d'akin dai daya kasance nan ne na mahaifiyarta Wanda da Alama itama nan take, kwandon kayan shafarta ta d'auko ta ajiye gabanta, Wanda babu abinda babu aciki, tafara d'and'asa kwalliya, takai kimanin awa d'aya tana kwalliya, bayan tagama ne ta tashi' tanufi wadrope ta dauko wata  green d'in atamfa, me zanen  ganye golden, nd yellow, wacce akayima ado da yellow Codeless d'inkin zamani riga da zani pieces.

Bayan tasaka kayan, sun kuma kar6i jikinta, dan ba 'karamin kyau saukayimata ba, sun fiddo da duk wata kya'k'kyawar halitta da Allah yabata.

Fara ce, Amma ba irin tass d'innan ba, farinta dai-dai misali, tanada manyan idanu Wanda akoda yaushe idan ta kalleka, sai kayi tinanin kashe maka su takeyi, amma ba haka bane haka yanayin kallonta yake, ga dogon hanci Wanda ya 'kara fito da anaifin 'kyawunta, bakinta d'an karami, hakoranta farare tas, sai wushiryar data 'kara fito da kyawun su, gefen kumatunta ko magana take yana lotsawa, barantana kuma idan tayi dariya, wannan dimple ba karamin 'kara fiddo da 'kyawunta yake ba.

Also Download: Alhini Complete by Zee Maman Khady

Bayan tagama shirinta tsaf, ta dauko hijab d'inta, kalar golden, ta Sanya tiare ta dauko ta feshe jikinta dashi, sannan ta d'auko plat shoes shima kalar golden, ta Sanya, tanada tsayi shiyasa bata damu da takalmi me tudu ba.

Fitowa tayi tsakar gida, inda mahaifiyarta ke jiranta, tace "gani Hajiya.

Hajiya tace "yauwa dama gidan Maman Ummi zakije, kicemata ya maganar adashi, yanaji shiru, ko har yanzu, ba'a gama had'a kud'in ba?.

Kuma kice ina gaisheta, sannan ta d'auko naira Hamsin tabata, Anshi ki hau napep, ta kar6a sannan tafice Daga gidan, Hajiya namata fatan zuwa lafiya da kuma dawowa lafiya.

Taje gidan ayken harta, Isar da sa'kon takuwa yi sa'a dan angama had'a kudin saboda haka aka bata, dama kwasar adashine na Hajiya.

Kasancewar hajiyar kud'in zuwa kawai tabata, can kuma gidan dataje, Mmn Ummi tabata, kud'in napep d'in Amma ta'ki kar6a, saboda haka a 'kafa ta tafi, tana tafiya tana zancen zuci, tayi matu'kar danasanin tahowa a 'kafa domin yanda ta lura da duk Inda ta gifta maza ke binta da ido.

Azuciyarta tace "Allah ya taimakeni hijab na Sanya, da nabani.

DOWNLOAD BOOK


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post