[Book] Budurwar Mijina Complete by Sadnaf

Budurwar Mijina

Title: Budurwar Mijina

Author: Sadnaf

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 170KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Ku sauke sabon littafin marubuciya Sadnaf mai suna "Budurwar Mijina" complete hausa novel a text document daga shafin nan. Za ku iya daukarsa yanzu.

Book Teaser: Sauk'owa yayi daga Kan machine d'in fuskarsa d'auke da murmushi dan yasan fushin zagin da lubna ta mata take yi.

D'auke kanta tayi ta maida gefe Mahfuz ya sake sakin murmushi Yana "Kiyi hakuri wlh wanka na Shiga ta d'auki wayar bansani ba"

"Jiya ma haka kace wanka ka Shiga ta d'auki wayar ta zageni kaga ma d'aukar wayarka bashida amfani tunda ko na d'auka itace ta bugo dan ta zageni na rasa mai na tare mata inaga baka tab'a bata labarina ba in ba dan kaddara ba tasan bata Isa ta rigani samunka ba"

Tace tana Jan siririn tsaki

"Kiyi Hakuri hakan bazata sake faruwa ba ki dan saki fuskarki mana sweet dina"

Sai a lokacin ta dan saki murmushi tana "Hmm Mahfuz ya zancen namu saura wata biyu naje gida fa"?

"Karki damu insha Allahu madam na haihuwa zan yunkuro ki kwantar da hankalinki

Sai a lokacin Hadeeza ta saki murmushi tayi wal da Ido ta juya ta koma ciki

Bata fi minti biyar da Shiga ba ta fito da wani leda mai dan kyau ta mik'awa mahfuz daya washe baki Yana "Bakya gajiya sweetyna"

Ya bude ledar ya dauko dan karamin flasks din  potato balls ne a ciki ai sauce din albasa sai kamshi ke tashi  har dasu chocolate dasu  biscuit.

Yana Jin dadin yanda Hadeeza ke hada Masa break fast sabo da girkunanta yasa baya damuwa yaci na gida duk da yasan lubna itama ba a baya bace wajen iya girkin.

Bai tab'a tunanin zai dawo da Hadeeza rayuwarsa har ta samu gurbi a zuciyarsa ba.

Dan ta wulakanta shi a baya kafin ya had'u da Lubna yaso ya auri Hadeeza sai ta nuna Masa tafi karfinsa,dan zai iya cewa shine mai karamin karfi a manemanta.

Yana ji yana gani ya hakura da ita,Allah cikin ikonsa ya hadu da lubna da ta saka shi manta wata Hadeeza har yaji a yanzu yasan ya had'u da wacce take Sansa sabida Allah 

Tuni ya shafe babin Hadeeza ya manta da ita har Allah yayi aurensa da lubna wata hud'u da aurensa sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa koda ya daga a gigice ta jefa mishi tambayar "Mahfuz dagaske ne kayi aure"?

Duk da yasan itace cewa yayi "Da wa nake magana"?

Kamar zatayi kuka tace "Haba Mahfuz Kamar ya da wa kake magana Hadeeza ce"

"Wacce Hadiza wai kimin bayani nagane"? yace Yana  hararar wayar dan karfin hali yake gani a wajenta"

"Mahfuz dan Allah ka bari nasan kasan wacce take magana so kake kawai ka wulakantani"

Tsaki yayi ya kashe wayarsa ya danna lambarta a block dan kallon mai kwadayin abin duniya yake mata ko uban Mai yasa ta kirashi yanzu ko kunya bata ji ba.

Kwana biyu a tsakani ta sake kiransa da wani lambar Yana Jin itace ya Kara kashe wayarsa Yana mamakin mai take nema a wajensa.

Bata hakura ba ta hau tura Masa message ta watsapp da  message ko karantawa baya yi sai ya goge.

Bata tab'a fashin kiransa ba Kiran da take masa har da tsakar dare akan dole ya koma kashe wayarsa daddare ranar da abin ya ishe shi Yana d'aukar wayar yace "Wai Mai kikeso a wajena ne Hadeeza naga mun rabu nayi Aurena mai Kuma kike nema a wajen wanda ba ajinki ba"?

Cikin muryar kuka tace "Mahfuz yanzu dagaske kayi aure kana nufin ka hakura dani ya kake so nayi da san da nake maka wlh ko a baya Ina kaunarka wlh gwadaka nake daga naje gida na dawo kawai naji labarin aurenka a wajen Abdul (A gidan kanin mahaifinta take a zaune tana karatu Iyayenta suna garin gombe)

Tsaki mahfuz yayi yace "Hadeeza ba gwadani kike ba a samarinki da kikeso ki aura aka yaudareki shine yanzu Kika nemoni nidai a yanzu nayi Aurena na auri matar da nake balain so da kauna muna zaune lafiya Dan Allah ki rabu dani ki daina kirana a waya"

Daga haka ya kashe wayarsa ko minti biyar ba'ayi ba sai ga message kaca kaca daga wajenta na ban hakuri da irin san da take mishi ya  bata dama ta gwada mishi irin san da take masa,ta yarda zata je ata biyu za Kuma tayiwa matarsa biyayya.

Ko ta kanta bai bi ba ya danna Mata blocking dan ko mai zata yi bayajin zai saurareta shi da Allah ya bashi finta ma Lubna Mai so da kaunarsa ba abinda ta rage shi dashi.

Ga mamakinsa Hadeeza haka ta cigaba da canza lambobi tana kiransa ko da zai gaya mata bak'ar magana hakan bazai saka ta fasa kiransa ba har ta kai message din safe daban na rana daban na dare daban.

Bai tab'a bari lubna tagani ba take yake gogewa dadin dayaji  lubna bata mai bincike bata damu da taba masa wayarsa ba.

A haka ya samu shekara da Aurensu da Lubna watarana yaje wajen aiki awa biyu a tsakani sai ga Hadeeza a office dinsa.

Rabonsa da ita shekara biyar kenan taci kwaliyya ta Kuma yi kyau kamar ba ita ba ta canza akan sanin daya mata a baya ta Kara gogewa sai kamshin turare take. 

Ledar da ta shigo dashi ta ajiye masa agabansa ta langabar da kai ta hau matsawar kwalla.

Mahfuz kuwa kau da kansa yayi yana "Hadeeza dan Allah mai kike nema a wajena"

"Ba abinda nake nema a wajenka so nake kawai komai ya wuce mu cigaba da soyayyar mu"

"Shekara daya da Aurena Hadeeza idan ba yaudararki kikeso nayi ba banida ra'ayin yin soyayya ko na Kara aure matata ta isheni rayuwa Dan Allah kije ki nemi wani"

Bai idda magana ba ta fara hawaye har da sheshek'a mahfuz ya shareta ya cigaba da danne danne a laptop din gabansa sunansa data Kira yasa ya dago ya kalleta

"Allah ya jarrabceni da kaunarka mahfuz bansan ya akayi na wayi gari cikin tsananin sanka ba amma tunda kace haka dan Allah Ina neman alfarma mu cigaba da zumunci ka zama abokina"

"Ana abota tsakanin namiji da mace ne Hadeeza cigaba da muamalla dake kamar dai muna soyayyar kenan Mai amfanin haka"

"Dan Allah Mahfuz iya alfarmar da zaka min kenan ko ba kullum ba muringa waya ko chatt har Allah ya yaye min"

Burinsa kawai ta tafi daga mata Kai kawai yayi yace jeki naji"

Washe baki tayi ta mike tana "Nagode mahfuz ga wanan ba yawa sai na kiraka anjima"

"Hadeeza karki kirani kinsan inada mata kidaina kirana anyhow"

"Bakada matsala"

tace tare da sakar.masa murmushi ta juya tana wani irin takun daya sa Mahfuz kasa d'auke idonsa akanta har ta fice.

Sai da ya gama abinda yake ya bude ledar da ta kawo turare ne.masu kamshi sai snacks da akayi wrapping a foil paper har zai mayar da snacks din ya gutsiri meatpie din yaji ya masa dadi a haka ya gyara Zama yaci iya Wanda zai iya ci dan ta hutashe shi siyan abincin Rana, lubna taso ta ringa aika Masa da abincin rana ya hanata dan baya san ya wahalar da ita.

Tunda ga lokacin Hadeeza da zage wajen zuwa office d'insa tun bai wani bata fuska ba har ya fara bata fuska duk zuwan da zatayi da kalar abinda zata kawo Masa, text kuwa haka take tura masa.

Bai tab'a d'aukar wayarsa ya kirata ba sai dai ita ta Kira shi.

Yau da gobe a hankali ya fara damuwa da lamuranta har idan bata zo wajen aikinsa ba bayajin dadi, yayi balain sabo da snacks masu Dadi da take kawo Masa.

A irin wanan yanayin ta daina aiko Masa da text din da ta sabar.masa dashi,ta bar zuwa office d'insa haka.kawai.yaji ya damu tun Yana ganin zai iya daurewa har yaga bazai iya ba aranar da aka samu sati daya baiji daga wajenta ba ya kirata a waya sai daya mata.miscall ya kusa goma Kafin ta daga murya can kasa da Sunan bata da lafiya shiyasa yaji shiru Nan kuwa karya takeyi so take ta gwada shi taga ko ya damu da ita.

Ana tashi daga wajen aikin ya kirata ta mishi kwatancen gidan da suka koma bai Sha wahala ba dan ba wani nisa tsakanin gidan nasu da wajen aikinsa.

Sai gashi har da kayan dubiya.

Har dan karamin palon gidan aka masa iso da alama ba kowa a gidan sai kannenta da suka kasance yaran kanin mahaifinta.

A kwance ya sameta a doguwar kujera ta Sha kitson attach da tayi parking,sai riga yar kanti armless da taje mata har kasa duk da batayi kwalliya ba bata yafa komai ba tayi wa mahfuz kyau.

Nanarkewa kawai take tana shagwaba Kamar bazai tafi ba lubna dake ta kiransa a waya yasa ya Mik'e ya Mata sallama ya ajiye Mata kayan dubiya ya fito.

Wani ikon Allah Koda ya dawo gida suna Hira da lubna Yana tuno Hadeeza da yanda ta ringa Masa shagwaba tunda ga wanan lokacin ya dawo da Hadeeza rayuwarsa ta samu matsayi a zuciyarsa dan ta Kai yanzu har breakfast take Masa idan zai wuce ya karba da Rana ma abincin take aika Masa.

Dak'yar yake yakice cin abincin dare a wajenta gudun kar Lubna ta zarge shi.

Zuwa yanzu baya iya kwana biyu bai ga Hadeeza ba duk da ba abinda Lubnarsa ta rage shi dashi wanan kenan.

LUBNA

Jan kunshi mai kunshina ta rangada min a hannu da kafa.

Tana ciremin na sallameta ta tafi na hada Abubuwan da nake dan gyaran jiki dashi na hada na mulka a jikina dashi sabida fatata ta Kara laushi.

Iya kokarina zanyi dan na dawo da hankalin Mahfuz kaina bazai yu wata Yar iska can ta kwace min shi ba,nima sai a yanzu naga wautata da na hau fushi da shi,waya sani ma ko kwana ma yayi jiya yana waya da yar iskar SR.

Sai da na goge ko'ina na  jikina na Shiga wanka har wani iska naji Yana Kara Shigana.

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Kwarata Return Complete by Jamila Musa{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post