[Book] A Dalilin Gata Complete by Safiyya Jegal

A Dalilin Gata

Title: A Dalilin Gata

Author: Safiyya Jegal

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Fiction

Doc Size: 224KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2016

Description: Ina daukacin masoyan marubuciya Safiyya Jegal? Ku sauke cikakken littafinta mai suna "A Dalilin Gata" complete hausa novel a text document daga shafin nan namu.

Book Teaser: Cikin shirin shi na alfarma ya fito falon ya durk'usa har k'asa yana gaida mahaifiyar shi. Kafad'ar shi ta rik'o ta mik'ar dashi ya zauna gab da ita.  "Sai ina yanzu son?".  "Mum zanje company ne saboda muna da meeting da za muyi da wasu bak'i ne".  "Sai ka shiga ku gaisa da Dad d'in ka duk da ina tunanin kamar barci yake yi".  "In hakan ne bara kawai in wuce don nasan Dad sai mu wuce 15mnt muna gaisawa, ga shi sauri nake yi".  "Kenan kasan halin abinka nan 6angaren, amma d'ayan 6angaren duk yanda nake lurar da kai ba ka gane wa".  Da saurin shi ya mik'e cikin murmushi ya doshi hanyar fita "inna dawo ma yi maganar".  "Kullum hakan kake ce wa, fatana d'aya Allah yaganar daku baki d'aya".  Yana gab da fita ya ji muryar ta tana furta "Brother ni ma ba za'a tsaya mu gaisa ba kenan"?.  Cikin saurin ta ta k'araso gab dashi, hugging d'in shi ta yi "Mrng Brother". "Mrng Little Sister, inna dawo za muyi magana".

Da sauri ya fice saboda agogon hannun shi daya duba ya ga saura minti biyar, a k'a idar shi bai son African time yayi ko ayi mai.  Sai da ya hau kan titin ya k'ara gudu sosai saboda saurin da yake yi.  K'eeeeeee kake ji sanadiyyar mugun birkin da yaja wanda saura k'iris ya kad'e mutumen.  Cikin isa da k'asaita da kuma 6acin rai kwance a saman fuskar shi ya fito daga motar.  Mari biyu k'warara ya yiwa dattijuwar fuskar mutumen wanda baki sake ya bishi da kallo.  Hannun shi na dama ya saka ya cire glass d'in shi no respect, yasa d'ayan hannun ya fitar da handkerchief a gaban rigar shi ya goge fuskar shi.  Cikin azama ya koma cikin motar ya tada ta, ganin ce wa zai iya bi saman kan shi yawuce yasa cikin sauri yaja jikin shi gefen titi da mamaki fal a ran shi.  "Ohhh! duniya ho yanzu wannan yaron zai fito ya faffallamin mari hankalin shi kwance kuma yana k'ok'arin takani ya wuce, duniya ce ta ishi kowa riga da wando".  

**  

Yau kam tana ganin sun makara ga yanda suke fitowa mazaunin su na masu bara gefen wata ma'aikata.     Bayan sun iso gurin ne ta gayar da wa'anda ta tarar sannan suka ne mi guri suka zauna.  "Har ga Allah ba na son wannan zaman barar da muke yi, kawai abin ne ya riga yafi k'arfi na, don in mun daina bansan miye mafita a garemu ba".  Matar kusa da ita ne ta ta6o ta sanadiyyar wani da ya zo yana raba masu d'ari-d'ari wanda har ya zo kanta bata sani ba nan ta kar6a ta yi godiya.  12:00pm suka fara watsewa da kad'an-kad'an inda ita ma Zajla ta rik'a sandar mahaifin ta suka doshi hanyar gida. Asaman hanyar ne suka had'u da yaran da ke tallar zogale da 6ula had'e da k'uli mai magi da yaji.  "Baba ko mu siyi zogale da 6ula?".  "Nawa ne muka sa mu yau hala?". Kud'in ta fitar ta irga taga 350 ne, nan take gaya mai ko nawa ne.  "Siya mana 6ula na 100, zogale da k'uli na 50".  Hakan ta tsayar da yaran ta siya suka wuce gida. Da shigar su gidan ne ta yi masu kwad'o suka ci.  Bayan sun gama ne ta ebi ruwa ta je ta yi wanka ta yi shirin islamiya.  Wasu kod'add'un uniform kalar blue ta saka sannan ta yiwa Baban ta jagora ta fito dashi k'ofar gida cikin inwar icen mangoro gurin su Malam Inuwa.  "Y'ar Baba za'a je makarantar kenan?".  Ta bashi amsa ta re da durk'usa wa ta gaida su. "Sai ki biya ki kira Salmat in ta shirya ku wuce".  Gidan Malam inuwa ta dosa a k'ofar gida suka ci karo da Salmat, hakan suka sa kai sai makarantar su.  

Suna shiga islamiyar suka tarar da mutane na alwala sanadiyyar kiraye-kirayen sallar azahar da ake yi ko ina, nan su ma suka yo alwala suka bi jam'i akayi sallah.  Bayan sun k'are ne suka wuce ajin su na d'aukar hadda, hakan suka biya da d'ai d'aya inda Ustaz Lukman ke sauraren su had'e da gyara ga duk wanda ya yi kuskure.  Da hakan suka k'are har la'asar ta yi suka fito akayi sallah.     A k'a idar makarantar duk ranar larba za'a za 6i d'alibai uku cikin Maza uku cikin Mata domin gabatarda abubuwan da ake koya masu a cikin class.  Hakan ta kasance yau ga d'aliban da aka za6a sun fito sun gabatar da abubuwan gwanin sha'awa ga ma su saurare.  K'arfe shida na yamma aka tashi kowa ya ka ma hanyar zuwa gida. Asaman hanyar ne Salmat da Zajla suke tattaunawa.  "Gaskiya Salmat yau sai gaba na ke fad'uwa na zata Ustaz Lukman zai sanya ni a cikin masu karatun satin nan".  "Tabbb! Ai kima shirya kinsan satin sama dole za ki shigo a cikin wa'anda za su yi".  "Ni fa abinda naso su bar mu muji da karatun haddar mu tunda lokacin musabak'a na k'aratowa".  

"Lallai ma Zajla kin kai, kawai kije kiyi ta bitar haddar ki sannan ki zauna da shirin fitowa larbar sama karatu gaban ko wa".  "Muguwa kawai tunda kin ga kin yi yau hankalin ki ya kwanta ai zaki rik'a kayar min da gaba", tana maganar had'e da kai mata dundu a bayan ta.  "Gaskiya kar ki tayar da hankalin ki abin baida wata fargaba kawai dakin fito dakewa za kiyi, kuma kar ki rik'a kallon mutane ki nok'e kan ki kawai".  "Shikenan Allah yakai muna rai yasa fargaba ta fice min kamin ranar".  "Ameen", ta amsa a gajarce.  Da hakan har suka k'araso gida, a tare suka shige gidan su Salmat d'in saboda wannan k'a idar ta ce in sun da wo daga islamiya gidan su Salmat take zama har sai Baban ta sun k'are hira sannan ta fito su shiga gida.  **  Cikin 6acin rai ya shiga d'akin meeting d'in wanda sanadiyyar hakan kowa ya sha jinin jikin sa.  Hakan akayi meeting d'in rayuwar sa 6ace wanda mataimakin shi ne Imran ya jagoranci komai har aka k'are.  Bayan bak'in sun wuce ne wani cikin ma'aikatan ke ba da shawara kan ce wa me zai hana ayi musaya da wa'ancan bak'in a basu fata suko su bada ire-iren takalma, jakunkuna da sauran dangin kayan da ake sarrafawa da fata d'in?.  Ya cigaba da ce wa "a tunani na hakan zai fi akan abada fatar su bada kud'i ko ya kuke gani?".    Ya k'arashe maganar had'e da kallon mutane cikin nu na bajin ta kan shawarar da ya bayar.  Kallon da mutane suka bishi da shi ne na alamar ba kada hankali, wasu kuma na tausayawa gare shi ya sa ya sha jinin jikin shi ya yi tsit.  Ko wa ya yi zugum domin jiran me zai biyo bayan maganar da ya furta, saboda duk yanda aka zauna meeting ba bu mahaluk'in da ya isa yace tak ba tare da ya bashi dama ba, barrantana yau da ya shigo rai 6ace wanda ya hana yayi magana har akayi meeting d'in aka k'are.  "Duk da ce wa kai bak'o ne a wannan ma'aikatar bazai hana hukunci na yahau kanka ba".  Cikin damuwa Imran ya tari numfashin shi had'e da bashi hak'uri amma ina ya gama furta "na sallame ka daga yau".  Hakan ya ta shi tamkar guguwa yabar gurin cikin mintunan da basu wuce uku ba.  Durk'ushe ya yi gaban mataimakin A.K.A kuma babban aminin shi yana mai bada hak'uri had'e da furta  "In har kuka sallame ni bansan ina zan dosa ba, da wannan aikin nake kula da mahaifiya ta da sauran k'anne na marayu".  "Sai dai kayi hak'uri aikin gama ya gama duk nan ba wanda ya isa ya janye wannan hukuncin".  "An samu matsala ne tun farko ba'a gaya ma tsarin shi ba shiyasa, ko ni nan da nake mataimakin shi kuma babban aminin shi indai a office ne ban isa yayi magana inyi ba har sai ya bani dama".  Hakan sauran ma'aikatan suka rik'a bashi hak'uri had'e da fatan alkhairi saboda bakin alk'alami ya bushe, don shine mutum na bakwai da hakan ta kasance dashi tun lokacin da mahaifin shi ya yi ritaya ya bashi kula da company d'in, da hakan kowa ya Kama gaban shi.  Mutum biyu ne suke tattaunawa akan matsalolin da ke faruwa a ma'aikatar.  "Gaskiya wannan ma'aikatar ba ta nesa da rushewa, kaduba kaga yanda yaron nan ke shuka rashin mutunci son ranshi", cewar tsamurarren.  "Tabb to ai abin gado ne haka mahaifinshi yake tsula tsiya lokacin da yana manager, don ni na rasa gane tsakanin d'an da uban wa yafi rashin mutunci", a cewar bak'in mutumen kakkaura.  "To Allah yayi masu magani, kuma yaganar dasu".  "Ameen". 

Hakan ya fad'o gidan ko sallama babu sanadiyyar wani huci da yake yi shi ala dole an 6ata mai rai fuska tur6une tamkar namijin zaki.  Da saurin shi ya ta shi ya taryo shi yana bubbuga bayan shi, sanadiyyar ya k'i jinin jure damuwar d'an shi komi k'ank'antar ta.  "Wa ya ta6a uba ga Dad kuma d'a ga Dad?, bazan juri ganin ka cikin 6acin rai ba komai k'ank'antar shi".  Ruwa ya tsiyaya a cup ya d'ora mashi a baki ya kauda kai yana huci, d'ayan gefen ya mayar da cup d'in sannan ya sha kad'an ya kauda kai tamkar wani jinjiri.  "Gayamin Babana meke faruwa, kuma wa ya 6ata ma rai?".     

Mum baki ta sake tana kallon sarautar ubangiji, abu gwanin haushi.  Cikin yanga tamkar wata mace ya kora mai abinda ke faruwa.  "Yo banda abinka Son miye laifin wanda ya baka shawara akan cigaban ka?, kuma wai har za ka iya ta da hannu ka fallawa dattijon mutane mari", Mum ce ke wannan maganar cikin 6acin rai da fad'a-fad'a.  "To shi dattijon titin uban sa ne da zai zo yana tafiyar yanga akai?", cewar Dad.  "Wallahi dai ku bi duniya a sannu daga kai har yaron ka, shin kud'i hauka ne? Su talakawan su sukaso ganin Kansu a hakan? Ku da kuke hakan siya kukayi aka baku gyara?, bai dace ka rik'a nunawa yaran nan gatan da yazarce misali ba".  "Mu shiga daga ciki Son, saboda ta fara wa'azin nan na ta da take zama alarammar kan ta taja kuma ta fassara", hannun shi ya rik'a suka haura sama sai bedroom d'in shi.  "Mum wannan abin fa ya kusa yawa, miye laifin wanda zai kawo cigaba akan lamurran ka da Brother zai yanke wannan d'anyen hukuncin".  "Rufamin baki ai duk halayyar ku iri d'aya ce ku ne masu uba mai kud'i to wallahi ina guje maku ranar nadama saboda wannan abin ba gata ne uban ku ke nuna maku ba", cikin fad'a sosai ta k'arashe maganar.  "Kin san dai Mum na d'ara Brother don bazan yi abinda ya aikata yau ba".  "Ku dai kuka sani, Allah ya ganarda ku daga ku har uban na ku don wallahi rayuwar ku kanta abar tausayi ce, don mutumen da baisan darajar d'an Adam ba yana cikin matsalar rayuwa, komai za kuyi ya kamata ku rik'a duba cancantar abin".  "Kullum game da tarbiyar ku tufka nake yi mahaifin ku na yiman warwara, a tunanin shi wannan gata ne".  "Mum tunda munsan girma da darajar ku ai ba muda laifi, dama ca akayi mu girmama iyayen mu".  "Sai akace ku taka duk wanda kuke so wannan shine dai-dai a cikin aya da hadisin Dad d'in ku?, wato mu ne mutane saura dabbobi ne a gurin ku".   "Mum ba kya ga newa ne, shi fa Dad raini da wulak'anci ne bai d'aukar mana ba shiyasa kike ganin tamkar wulak'anta mutane muke yi, amma ba hakan bane".   "Mum fa su mutane ba ka iya masu idan kayi sake sai su ta ka ka son ransu".  Mugun kallon da ta bi ta dashi ne yasa ta ja bakin ta ta yi shiru. D'aki Mum ta wuce tabar Saudat zaune a falon, ganin hakan ya sa ta bi sawun su Dad.  **  Sanadiyyar yau ta kama alhamis ba islamiya ya sa tun safe tana siyo masu koko suka sha ta hau wankin su ita da Baban ta.    Bayan ta gama ne tayi shara ta tsaftace gidan, yau girki ta d'ora masu sanadiyyar tsakin masarar da Mama Inno ta ba su jiya wanda zai kai kwano uku.  Waje ta fita ta yi sa'a da yaran da ke tallan zogale dafaffe nan ta siyo ta had'o da d'an magi ta koma gidan.      Faten tsakin masara ta yi wanda yaji zogale.  Sai da ta samu guri ta saka ma su Mama Inno faten ta kai masu sannan ta dawo gidan.  Ruwa ta ebo ta kaiwa Baban ta ya wanke hannun shi ita ma ta wanke sannan suka yi Bismillah suka fara ci.  Suna gama wa ruwa ta fara kai mai ya yi wanka sai da ya fito ta taimaka mai ya shirya yana ta sanya mata albarka sannan ta shiga wankan ta fito.  Sai bayan la'asar yau suka fita yawon su na bara, daka gansu tsaf dasu sai dai talauci dake barazana dasu.  Hakan ta gayar da mutanen gurin sannan suka nemi guri suka zauna, sai gab da magrib suka wuce gida inda ya tsaya gurin su Mal Inuwa itako ta shiga gidan su Salmat.  Sallah suka fara gabatarwa bayan sun k'are ne suka rik'awa juna bitar haddar su domin su k'ara daddak'awa.  "Salma zo ki lek'a daga waje ki kira Sagiru yakaiwa su Baban ku abincin su".  K'ur'anin ta ajiye ta fice bayan ta kira shi ne sannan ta dawo masu da nasu abinci d'akin, nan suka ci suka gama sannan suka gabatar da isha sai k'arfe tara sannan Zajla ta fita ta ja Baban ta suka wuce gida.                              

Zaune suke saman dinning table suna breakfast sai tattaunawa suke yi akan lamarin company.  Sai da aka yiwa wayar shi Kira biyu ana ukun sannan ya d'aga wayar ya nufi hanyar d'akin shi, gaisawa suka fara yi sannan ya fara magana fad'a-fad'a had'e da ya mutse fuska.  "Kana sane da ce wa duk inda ake taro in har akwai Mata ba na nufar gurin, saboda haka kuci gaba kawai idan kun gama ma had'u, ka isar da sak'on taya murna ta zuwa ga Salis, in ya natsu zan kira shi".  Yana kai k'arshen maganar ya dak'ile wayar shi ya bita da wani kallo tamkar ta yimai wani laifi, gado ya fad'a domin ya d'an huta saboda ba mutum ne maison fita ba.   **  Kwanci ta shi asarar mai rai, yau ta ka ma Larba wanda Zajla sai gaban ta ke fad'uwa sanadiyyar tunanin da wuya Ustaz Lukman bai fitar da ita cikin masu karatun k'arshen sati ba.  Kamar kullum yau ma hakan ce ta kasance, bayan gabatar da sallahr azahar suka shiga class domin bitar haddar su saboda k'aratowar lokacin musabak'ar su.  Bayan an gama sallar la'asar ne aka fitar da mimbari da kujeru domin zama tsakiyar makarantar a gabatar da ire-iren abubuwan da ake koya masu.  Mutum uku cikin maza suka gabatar da yadda ake taimama da kuma sallar gawa, sai matan biyu da suka gabatar da koyar da alwala a aikace.  Zajla ce za ta gabatar da bayanin wankan tsalki da kuma addu'o'i.

Bayan ta yi basmala ta gabatar da sunan ta da Zajla Abubakar Zubair sannan ta fara da ce wa'.  "Shi dai wankan tsalki ya kasu zuwa kashi-kashi, akwai wankan janaba, akwai wankan haila, akwai wankan d'aukewar jinin bik'i (jego) da sauran su.  "Kamar yanda kuka sani su dai wad'annan abubuwan wanka iri d'aya ake yi masu sai dai niyyar su ce data ban-ban ta".  "Da farko za'a so mutum ya sa mu ruwan shi tsaftatacce, wa'anda kalar su bata canja ba, d'an-d'anon su bai canja".    "Anan abinda ake nufi da kala ko d'an-d'ano shine kar mutum ya d'ebi ruwan Lipton ko ruwan wankin shinkafa ko ruwan da ke da gishiri yace wankan tsalki zai yi dasu".  "Da farko mutum zai fara wanke gaban shi, bayan ya wanke zai wanke hannun shi saboda najasar da ya ta6a, zai d'ebo ruwa har sau uku yazuba ma kansa, ya murza kansa har ruwan sukai k'asan kansa, daga nan zai yi alwala shud'i guda-guda sannan ya wanke 6angaren jikin shi na dama daga sama har zuwa k'asa, 6angaren hagu ma haka sannan ya game jikin sa da ruwa ya murza ko ina".  "An samu sa6anin wasu maluma da suka ce idan mutum ya wanke gaban shi zai fara gabatar da alwala, wasu kuma sukace sai bayan ya k'are wankan gaba d'aya sannan yayi alwalar. Allah masani".  "Addu'ar shiga kewaye (( Allahumma inni A'uzu bika minah khubithi wal khaba'ithi))  "Addu'ar fitowa daga kewaye". ((Gufranak))  "Addu'ar mugun mafalki". ((Allahumma inni A'udhu bika min sharri ma ra'aytu fii manaamee an yadurranee fii deeni wa dunyaay))  "Addu'ar kariya daga azabar k'abari". ((Allahumma innee As'alukar Jannah, wamaa k'arraba ilaiha min k'aulin wa amal, wa A'udhu bika minan naar wama k'arraba ilaiha min K'aulin wa amal, wa A'udhu bika min fitnatil mahya wal mamat wa min fitnatil k'abr wamin fitnatil masihid dajjal wamin Adhabin naari wasu'il maseer))  "Addu'ar  neman ya fiyar sa6o. ((Allahumma inni a'uzu bika an ushrika bika wa ana a'alam wa astagfiruka li maala a'alam))  Gyaran muryar da akayi da speaker shi ya nu na mata alamar lokacin ta ya yi, speaker ta ajiye ta koma mazaunin ta.       Kabbara ce ta biyo baya had'e da jin-jina mata akan abubuwan da ta gabatar.  Nan akayi salati ko wa ya ka ma gaban shi sanadiyyar gabatowar magriba, kowa da maganar (ZAZ) ya fita a bakin shi sanadiyyar add'o'in da ta yi tamkar itama Malama ce ba d'aliba ba.                                    

Gaskiya (ZAZ) kin kawo wuta sosai yau, kinji yanda kike rero addu'o'i tamkar Ustaz Yusuf?".  "Banson sharri wallahi, kina ji yanda murya ta ke wani rawa-rawa alamar tsorace nake. Ni fa shiyasa kika ga ko wannan musabak'ar da za muyi gabana ke ta fad'uwa saboda na k'i jinin karatu a cikin bainar jama'a".  "Tabbb ai wannan shafin mai ne wallahi, kina ganin yanda ake taro sosai idan lokacin musabak'a yayi. Kuma hakan da ake yi duk Larba anaso abin yabi jikin mune har mu saba mu daina jin tsoro", cewar Salmat.  "Ranar da duk Ustaz Lukman ya ji kina furta wannan (ZAZ) d'in a bakin ki kya yi bayani, saboda kinsan ya ce adaina kira na da hakan".  "Yo ai ba sai kin gaya min kina da mai tare maki ba, duk kauce-kaucen ku za ku fito kuyi bayani ne".  "Shin tsaya me kike nufi ne, ban fahimce kiba?".  "Kinsan dai ko kin 6oyewa ko wa soyayyar ku da Ustaz Lukman bai dace ni ki 6oyemin ba".  Cikin gwalo ido da wani cin birki tamkar mai tuk'in mota ta ja ta tsaya, mamaki kwance fal a fuskar ta.  "In har kin yarda kalmar "So" bata ta6a ratsawa tsakanina dashi ba, sai dai mutunci".  "Ke ce baki fahimci hakan ba, amma duk wanda ya yi mai duba na natsuwa idan kina gaban shi to zai hango son ki kwance a k'wayar idon shi".  "Allah yashirye ki, ke kika san wani abu "So" ni kam da saura na".    "Ke ma za ki sani idan lokacin kisani yazo, wa yaga ana soyewa tsakanin Malami da D'alibar shi".  "Allah ni ko guntun namiji bai cikin tsari na ko Aure zan yi, na fison dogon namiji wanda zai yi guda da rabi d'ina".  Dundu Salmat ta kai mata had'e da furta, "makira kika ce baki san So ba kuma amma ga shi kina wassafa mijin da kike son Aure".     "Shi ne sai aka ce maki wassafa ra'ayin ka shi ne So d'in?".. Yanzu bara in tambaye ki akawo maki gabjejen namiji wanda yayi hud'u d'in ki ya kika ga abin?", tana maganar ne had'e da dariyar k'eta.  "Bakin ki yasari d'anyen kashi muguwa kawai, Allah ya kiyaye ni".    Dariya Zajlah tayi sosai akan yanda Salmat ke maganar had'e da ya mutse fuska tamkar ga mijin nan gaban ta.  Da hakan suka k'araso gida sannan suka gabatar da duk wani abu daya dace kafin Zajla taja sandar Baban ta su wuce gida.   

**  

Har gida yau suka kawo mai ziyara shi da Salis, bayan sun gayar da Mum suka fita gardener, saboda a al'adar shi in har yana gida indai ba bacci yake yi ba to nan ne gurin hutawar shi.  "Gaskiya (A.K.A) baka kyauta min ba, yanzu ace ayi birthday d'ina ko wa ya hallara kai baka je ba, kuma kana sane da ce wa duk duniya banda friends d'in da suka wuce ku kai da Imran".  "To ku ne da jaye-jaye kuce duk abinda za kuyi sai kun saka Mata a ciki shi ne birgewa a gare ku, ni ko in har hakan za ta cigaba da kasancewa to ina mai tabbatar maku za kuyi lamurran ku ba dani ba".  "Ni wannan abin na ka na d'aure min kai, zanga ranar auren ka da kuma matar da za ka aura, saboda wannan abin na ka ya yi yawa", ce war Imran.  Murmushi ya rik'a yi sama-sama wanda har fararen hak'oran shi na bayyana had'e da dimple d'in shi.  "indai ku kuka ta shi auren Allah sanya alkhairi don kunsan ba dani ba a y'an dinner da sauran su, zan dai je d'aurin aure shi ne na mu".  Kallon da suka bi shi dashi ne ya sa ya yi saurin kauda kan shi yana dariya k'asa-k'asa.  "Ka ma mayar damu wasu sha ka wuce za ka gani ne. Na ma manta in gaya ma Lubnah ta ce in ba ta number d'in ka".  Mugun kallon da ya yimai ne ya sa ya fahimci amsar da yake nufi zuwa gare shi.  "Baiwa wata Mace number ta na nufin rabuwar mu ta har abada dakai, ka sanni kasan waye ni. Duk cikin contacts d'ina number Mace biyu nake da, Mum da Lil Sis".  Cikin 6acin rai ya mik'e ya tattara wayoyin shi ya nufi hanyar shiga gida, duk yanda ya so tsayar dashi don ya nuna mai wasa yake yi abin yaci tura.    Bayan ya shige ne gidan Imran ya kai duban shi ga Salis had'e da hararar shi sannan ya furta.  "Sai ka ta shi mu fice tunda ka takaro zuciyar manya". Dariya sosai Salis ya yi had'e da furta.  "Ni fa suk'uwar shi dariya take ba ni, da abin 6acin rai da wanda bana 6acin rai ba za kaga ya had'e fuska ala dole shi fushi yake yi".  "Allah wataran da gayya nake tsokanar sa saboda inyi dariya".  "Don kasan duk rintsi yana tare damu ne, ko ya yi fushi dole yasauko shiyasa kake mai hakan", ce war Imran.  Hakan suka had'a nasu da nasu suka fice saboda sanin in kwana za suyi gurin bazai kuma kula su ba sai ranar da ya sauko daga zuciyar.  

Kamar kullum yau ma ta gama kimtsa komai na kula da gidan suka shirya suka fito sai mazaunin su na bara, wanda kullum suka fito wani irin mugun nauyi take ji a ranta.  Saboda a tunanin ta kamar ta ya ci ace ta wuce zama y'ar jagora, sai dai ba yanda za tayi sanadiyyar in har bata kula da mahaifinta ba wa ye ta ajiye da zai kula dashi yanda yadace.  

Ga shi dai in har ta ce baza su fito yawon bara ba to batasan wa zai ciyar dasu da sauran lalurorin su ba, tunda mahaifinta ba yada idon da zai fita yane mo musu abinda za suyi lalura.  Don ma Malam Inuwa na k'ok'arin basu abincin dare, duk da shi kan shi ba wata wadata ce dashi ba saboda ba kullum za'a ci abinci sau uku a rana gidan shi ba.  Duk ita kad'ai ke wannan tunanin a ranta, wanda har kullum take tunanin ina za ta ne mo masu mafita akan wad'annan matsalolin.  Sanadiyyar bugawar da motocin biyu suka yi ya janyo hankalin tsirarrun mutanen da ke zaune gefen hanya.  Dattijuwar na fitowa daga motor ta ya tayarda hannu zai sharara mata mari.  Hannun da ya ji ya rik'e na shi hannu ne ya bi da kallo.  "Ka daraja mutum ko da baka san shi ba, wanda ya girme ka haka yake tamkar yaya a gurin ka, haka zalika wanda ya yi sa'ar mahaifin ka tamkar mahaifin kane".  "Bai kama ce kaba kuma hakan bai dace dakai ba, yanda ka daraja manyan ka haka Allah zai sa a daraja na ka iyayen ko bayan idon ka".  Cikin sanyin jiki ya bi dattijuwar matar da kallo, sai wata irin kunya ce ke ratsa ga66an jikin shi, hak'uri yafara bawa matar had'e da neman yafiyar abinda ya tashi aikatawa.  Su duka biyun suka bi gurin da kallo domin ganin ta ina za su ga yarinyar amma ina ta 6acewa ganin su.  

***  

Sandar mahaifinta ta rika suka doshi hanyar gida. "Zajla ki daina saka kan ki a cikin rayuwar wa'annan mutanen, ba mutunci ne dasu ba".  "Baba ai Ba  komai na yi ba nasiha ce kawai na yimai saboda abinda naga ya kusa aikatawa bai dace ba".  "To Allah yamaki albarka yaba ki miji nagari inga auren ki da jikoki na".  "Baba ni fa na gaya ma bazan yi aure ba, saboda bansan wa zai kula dakai ba", tana maganar ne had'e da zum6uro baki tamkar yana ganin ta.  "Haba Zajla kidaina fad'ar hakan, Allah zai kula dani saboda shi ya so gani na hakan kuma zai ya yemin lokacin da ya so. Tunda abin ciwo ne bana halitta ba kuma daga baya ya same ni".  "Baba kayi ta addu'a Allah yaba ni hanyar samun kud'i insa a gyara ma idon ka".  

**

Fitowa tayi da sunan kai ziyara company maigidan ta, amma sanadiyyar abinda yafaru ne ya sa duk ta ji ba za ta iya k'arasawa ba akalar motar ta taja takoma gida.  Da shigar ta falon Saudat tagani zaune tana waya, ganin shigowar Mum ne ya sa ta yi saurin tsinke wayar had'e da mik'ewa tsaye.  "Mum ba dai har kinje company kin dawo ba?".  "Ban k'arasa ba na dawo". Ta ba ta amsa a tak'aice, ganin 6acin rai kwance saman fuskar Mum ya sa bata k'ara magana ba.  "Me ya hana ki zuwa skul yau?".  "Mum fa har na shirya Hafsat takira ni ce wa lecturer d'in bai zo ba shiyasa nayi zama na saboda dama yau shi kad'ai muke da". 

Bayan ta bawa y'an aiki umurnin abinda za'a dafa abincin rana, bedroom d'in ta ta wuce duk ranta jagule.  02:30 Talatu mai aiki ce ta gayawa Saudat ta fad'awa Mum an kammala komai.  Bedroom d'in ta wuce ta gaya mata sak'on k'are girkin, nan Mum ta bata umurnin kiran Brother su had'u falon Baban su.  Bayan sun kammalu anyi lunch an k'are ne ta kai duban ta ga Al'amein.  "Za ka iya tuna ranar da kashigowa Dad d'inku cikin 6acin rai har kana gaya mai ka mari wani dattijo?".  "Mum me ya kawo wannan maganar?, ai ina ga ta wuce, ko kuma wani fad'an za'a maimaita min?". Yana maganar ne had'e da murmushi a fuskar shi.  "Kaba ni amsa kawai". Ta furta a tak'aice.  "ina ga za'a yi sati biyu ko kwana goma".  "Wannan dai-dai yake da maimaita abinda ka aikata akan fuskar mahaifiyar ka", tana kaiwa k'arshe ta fad'a bedroom d'in Dad.  Cikin razana su duka uku suke kallon junan su kowanne 6acin rai kwance a fuskar shi musamman Al'amein da har jiyojin kanshi sun fara bayyana.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post