[Book] Dan Waye Complete by Zahara'u Baba Yakasai

Dan Waye

Title: Dan Waye

Author: Zahara'u Baba Yakasai

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 161KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Labari mai matukar kayatarwa. Littafin marubuciya Zahara'u Baba Yakasai mai suna "Dan Waye" complete hausa novel document. Ku saukeshi daga wannan shafi namu mai albarka.

Book Teaser: A hankali yake tafiya cikin sanyinjiki, da alama ya sha wuya,zai sanya ka sanyanayin sa nutsatstsen matashi ne.A nutse ya karya lumgun da ya shiga, adai dai lokacin wata fitinanniyar mota ta sako kaicikin lungun. Yanayin yadda ake jan motar dayadda sauti yake tashi shi ya tabbatar masa dacewa matashi ne dan uwan sa, da yake kallo faya ya yiwa motar ya mai da kansa, ya ci gaba da tafiya.

(Horn) din da motar take yi ya sanya shikallon me ake wa hon din? Ai kuwa watamatashiya ya gani tana tafiya a nutse, don yaddata nuna sam ba ta ma san matashin na yi matahorn ba.Can sai ya ga matashin ya fito a zafafe ya wankemata fuska, ta kuwa dafe fuskar ta tana maikallon sa. Ta zuba masa ido, ta ce.

"Me na yi maka ina cikin tafiya za kamare ni?"Tuni idanun ta Sun sonma tsiyayar hawaye,kan ka ce meye wannan duk mutane sun kewasu.Dai dai lokacin da ya soma masifa, ya ce.Shegiya, da na sani ma in take ki in takabanza, shashasha kawai".Ta ce, "Oho, ni ban san abinda kake cewaba, illah iyaka na san ka zalunce ni, don ban sanme nayi maka ba. Ina da matsala a kunne na donbana ji sam""Ka ji 'yar rainin hankali, za ki ce wai bakya ji, gashi nan kina magana rambadadau".Mubarak dake tsaye yana kallon su yataka ya ce."Abokina ba haka ake yi ba, saurin hannuyakan kawo da na sani, bai kyautu ba".

Ya kafa mata idanunsa yana kallon ta, yaSoma magana yadda za tafahimta, ya ce."Ke kin san kina da matsala me ya sanyakika fito ke daya?"Ta ce, "Nayi jiran Surayya ba ta zo ba, nikuma na tafi. Wannan ba shi ne karon farko ba,amma ya zalunce ni, domin marin macekaskanci ne. A ka'idar Musulunci ba a marinfuskar mace, jikin ma ba don duka aka yi shi ba,sai dai na barshi da Allah". 

Wancan mutumin ya ce, "In ba ki barni daAllah ba ya zakiyi? Yar rainin hankali".Ya dawo da hankalin sa kan Mubarak, yace"Malam ba a yi min irin abinda ka yi minyanzu, don na tsani shisshigi. Ke kuma ki kiyayeni, wallahi na sa mota na tattaka ki".Mubarak ya kalle shi cikin mamakinfurucin sa, yace"Kayi hakuri, ban san abin zai bata makarai ba. 

Ke kuma maza muje in raka ki, sabodagudun faruwar irin haka".Suka juya, mutumin ya ce.Nonsence) dama kana son sa kai ne, mezaka yi da musaka yadda Allah Ya yika da kyauhaka?" Mubarak da Izzatu suka ci gaba da tafiya,zuciyar ta na suya saboda takaicin abinda aka yimata..

Sun yi tafiya mai nisa suka karaso wani tafkeken gida, ta juyo ta ce."Na gode, na Allah ba sa karewa, gashi kakawo ni har gidanmu".Ya ce, "To sai anjima".

Har ta shige ta juyo ta ce."Kai wanne irin mutum ne? Ba za ka fadamin sunanka ba?"Ya ce, "Ni suna na Mubarak".Ta ce, "To Mubarak, sai anjima".Ta juya ba tare da ya tambayi sunan ta ba,ta shiga gida da sauri. Tana shiga ta fadawaUmmanta, ta ce."Kinga yau ma na sha mari".Ta ce, "Kiyi hakuri, ita rayuwa haka take"Amma Umma mutane basu da adalci..Nan ta fadawa Ummanta abinda ya faru,Surayya ta shigo ta ce.

Izzatu.Ta ce, "Kinga kyale ni, ai kin san zan fitaki ka fice"Ta ce, "Kai, kin manta ina da (text) yau?Kiyi hakuri, afuwan kinji 'yar uwa".Ta mike tayi falo, don duk suna tsakargidan.Mubarak yaro ne matashi, dan shekaruishrin da bakwai. Yaro ne salihi, na gari, wandaa duk fadin unguwar su in za a fadi matashinmutumin kirki za,a bashi na farko ba to zaishiga na biyu. 

Ya samu tarbiyya gurin iyayen sa,wanda suka dauki so da kauna suka dora masa,ko don shi daya suka haifa ne? oho.Iyayen Mübarak ba masu kudi bane, masurufin asiri ne, don Mubarak yayi (digree) dinsa,don mahaifin sa mutum ne me son sai ya gaMubarak din yayi ilimi sosai, an kuma yi sa'aMubarak din mai kwakwalwa ne.

Sallamar da yayı ya sanya mahaifiyar Sawacce mutanen ungwuwar suke kira da MarmoMubarak, shi kuma Mubarak din yana ce mataMah. Ta taso tana cewa."Kai yaron nan kayi nisan kiwo, ina kashiga ka sanya zuciyata ta kasa zama guri daya?"Ya kwashe da dariya, ya ce."Mah, sannu da gida".

Yai dariya ya ce, "Na girma fa yanzu Mah,a yanzu na kai munzalin da zan kula da ku"Ta washe baki ta ce, "To Mubarak. Yayaan dace?"Ya dan yi jimm, sannan ya ce.Kaiya Mah, rayuwar kasar nan na banimamaki. Ki duba kiga kyau irin na sakamako na,wai amma na rasa aiki. 

A Nigeria ba a duba cancanta illah a duba wa ka sani, wanda yake yasan wani"Mah, ta ce, "Uhm, kai dai dan nan bariInsha Allahu sai ka sami albarkacin AnnabinRahma".Ya ce, "Amin". Ta ce, "Bari in kawo maka abinci".Ya mike, "A'ah Ma, bari in dauko dakaina, ai yanzu ni ya kamata kuma na dinga yimiki kina zaune. 

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Sirrin Qeta Complete by Indo Ce{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post