[Book] Daren Goma Sha Hudu Complete by Bintuu Seer

 Daren Goma Sha Hudu

Title: Daren Goma Sha Hudu

Author: Bintuu Seer

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Fiction

Doc Size: 481KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Download Daren Goma Sha Hudu complete hausa novel. A historical adventure story which occurred during the era of slave trade in one of the biggest and prestigious kingdom in middle east.

Book Teaser: K'atoton jirgin ruwa ne irin gari gudan nan yana tafe a saman tekun atlantic ocean cikin tsakiyar daren goma sha hud'u,duniyar tamu gauraye take da hasken farin wata yana hasken ruwan teku,idan mai hange ya qure  dubansa gabas da yamma, kudu da arewa babu abunda zaka hango sai ruwan tekun bahar maliya wanda baida iyaka,tamkar gbdy duniyar tamu ruwa ne sbd girman ruwan teku,jirgin ya fito ne daga nahiyarmu ta africa zuwa qasashen sahara..... 

A cikin wannan jirgi kowa yana sabgogin gabansa tamkar ba a saman teku suke ba, yawancin fasinjojin wannan jirgi larabawa ne da turawa wanda suke zuwa qasashenmu na baqar fata kwasar al'umma su kaisu qasarsu su maishesu bayi, yanzun ma hknne don kuwa kusan dukkanin baqar fatar daka gani cikin wannan jirgi toh yana daya daga cikin kamammun bayin da suka kamo a qasashenmu na africa,wasu y'an mata na gano cure wuri guda daka gani dukkaninsu sun fito ne daga mabambamtan qasashe don kowacce cikinsu yanayin shigar jikinta ya bayyana hkn, wasu yan fillo na gano sanye cikin shigarsu ta saqi daga ganinsu fulanin ruga su biyar ne kowacce ba baya bace a fagen kyan halitta saida daga qarshen duk na rauna kyawun halittarsu lkcin da idanu na suka sauka bisa kan d'ayan cikinsu dake takure wuri guda ta sanya fuskarta tsakanin cinyoyinta nayi nasarar tozali da kyakykyawar fuskarta wannan yar fillo ne lkcin da wani bature dake gefensu yasa hannu ya dago dakanta ya busa mata hayaqin sigarin dayake busawa,lalle tsarki ya tabbata ga ubangijin daya qagi wannan kyakykyawar halitta, tana da dara dara idanu farare tas tamkar madara, bakinta dan mitsitsi ga le6enta pink tamkar ta sanya jan baki, hancinta dodar yake, kanta babu dankwali hkn ya bani daman ganin tsawon gashin kanta, gashin ra6e yake gida biyu rayi kalba, tsawon kalbar ta sauka har duwawunta ga gashin sai kyalli yake don baqine qirin irinna fulanin usul,billah Allah yyi ruwan tsallar madarar kyau a wurin, tsantsar kyau ne kawai daga rabbil izzati babu alqus.....

Jikinta rawa yake,haqoranta na had'uwa da juna ta qara qudundune jikinta a cikin wani kwali dake gefenta don dukkaninsu a yashe suke a qasan jirgin, babbar cikunsu ta matso kusa da ita tana ta6a jikinta tace" bimbii zazza6i kk,jikinki da zafi sosai" tana mata mgn ne da harshen fillanci,shiru ta mata batace komai ba, baturen dake kula dasu ne yazo wurin yana kallonsu sai kuma ya d'ora hannunsa a jikin bimbii yaji da zafi sosai yace"noo" watsa musu harara yyi yana huci don shi abunda ya tsana ya samu mara cikakken lfy a cikin bayinsa,gani yake tamkar asara zeyi kafin ya isa dasu wurin da saidawa,kuma ma ba kowa ne yake siyan bawa mara isashshiyar lfy ba, dafe kansa yyi ya koma ya zauna ya cigaba da busar sigarinsa, wani balarabe dake gefe guda shima tafe yake da nasa bayin ya kalli baturen yace" ita wannan bata da lfy ne" mgn yake masa cikin British English irinna na qasar birtaniyya, d'ago da kansa yyi ya kalli balaraben yace" ehh"  tasowa balaraben yyi yazo wurin yana kallonsu sai yyi murmushi ya kalli baturen yace" idan kana so sai muyi musanye na baka bawa mai lfy ka bani ita" tuni baturen ya miqe ya kalli balaraben yana dariya yace" nunamin bayinka sai na za6a dakaina" murmushi balaraben yyi ya nuna masa tawagar bayinsa wadanda kusan dukkaninsu zaratan samari ne majiya qarfi saidai mafi yawancinsu qabilu ne" kallonsu ya dingayi har idanunsa suka sauka kan wani murd'add'en basamuden mutum mai ji da qarfi ya dafashi yace" muyi musanyan da wannan" hk balaraben yasa d'aya daga cikin masu kula masa da bayin ya kunce wannan mutumi ya damqawa wannan bature shi kuma ya taso qeyar bimbii ya kawo masa cikin jerin bayinsa, tana kuka sauran yan'uwanta suna kuka hk don dole suka rabu ita ta koma cikin jerin tawagar bayin wannan balarabe......

A jerin bayin nasa su biyar ne kawai mata kuma kowacce yarenta daban ba wanda yake jin yaren wani, sauran duk maza, tunda ta koma wannan tawagar ta koma tamkar kurma, basa iya mgn da junansu don basu jin yaren juna, zazza6in dake jikinta ya soma tsananta sai rawar d'ari take gashi babu abun rufa hk dai ta takure wuri d'aya, wani saurayi ne d'an qabilar igbo fari sol dashi ya matso kusa da ita ya cire rigar sanyin dake jikinsa ya rufa mata, jin a rufe ne yasa d'ago dakanta tayi tana kallonsa sai kuma ta komar da kanta kan guiwowinta, mgn yyiwa daya daga cikin masu kula dasu ya miqo masa ruwan sha a wata kwarya ya ta6ata ta d'ago da sauri ta matsa daga kusa dashi don su babban zunubi ne a rugansu namiji ya ta6a mace shiyasa tayi saurin matsawa,miqa mata kwaryan ruwan yyi ta miqa hannunta ta amsa ta soma sha sannan ta miqa masa cikin harshen fillanci tace ta gode.........................

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Walijam Complete by Maman Teddy

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post