[Book] Daurin Boye Complete by Safiya Abdullahi Huguma

Daurin boye

Title: Daurin Boye

Author: Safiya Abdullahi Huguma

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 1.0MB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2021

Description: Daurin fili ma wuyar kwace gareshi bare kuma na boye. Ku sauke littafin marubuciya Safiya Abdullahi Huguma mai suna "Daurin Boye" complete hausa novel document.

Book Teaser: Sake gyara tsaiwarshi yayi jikin machine din nasa samfurin lifan kirar MOTO B,agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya kalla yana sake qiyasta mintocin daya kashe tsaye a qofar gidan,tabbas banda wani babban dalili babu abinda zaya sanyashi zaman jira har kamar haka,babu abinda ya tsana a rayuwarshi kaman jira,mutum ne shi mai kiyaye qa'ida wanda bai yarda da samfurin wannan maganar da hausawa ke bawa lokaci ba na african time.

Sauke hannun nashi yayi ya maida dubansa ga madaidaicin get din dake maqale da katangar gaban gidan wanda ya kasance shine kofar da zai sadaka da ainihin cikin gidan,kaman jiran hakan kuwa ake qofar ta soma yunkurin budewa,cikin sakannin kadan matashiyar dake yunqurin bude qofar ta bayyana.

A hankali take takowa zuwa inda yake,sanye cikin dinkin atamfa riga fitted da skert wanda ya zaunawa jikinta das,ta lullube jikinta da mayafi wanda baikai matsayin medium ba,a hankali yayi kokarin mamaye fuskarshi da murmushi duk da yadda fuskarta take kadaran kadaham hakan bai dameshi ba duk da yana ankare,ba fara'a sannan ba kuma a daure take can ba,kallo take kare masa tun daga nesa kaman yadda ta saba masa duk sa'ilin da ya ziyarceta,shirt ce jikinsa ruwan makuba da bakin wando jeans mai matsakaicin kudi,kafafunsa saye da takalmi budadde dinkin hannu na kasuwar kofar wambai,fes yake hakanan kayan sun masa kyau babu laifi,sumarshi kanshi zuwa sajensa a gyare a taje wanda hakan ya sake bayyana sirrin kyan da Allah ya bashi,ba shakka banda wani abu guda tak muhammad ya cika mijin aure wanda za'a iya nuna shi a ko ina,saidai wannan abun daya rasa din ya sanya ta cireshi daga tsarin mutumin daya cancanci aurenta.

"Barka da fitowa gimbiya zulaiha" ya fada cikin sassanyar muryarsa wadda na daya daga cikin abinda ke burge zulaihan tare da shi,duk da bata jin zata iya bashi damar kasancewa cikin rayuwarta,yana ci gaba da nazarin yanayin fuskarta a fakaice sanda ta amsa masa

"Barkan ka" ta fada cikin wani salon shan qamshi da basarwa

"Har na fidda rai ai,na tsammaci yau bazan samu ganinki ba"

"Kusan da hakan ce ta kusa faruwa,saboda zamu fita ne da maama,sannan ma kuma bansan zaka zo din ba,yanzun ma zuwa nayi na gaya maka.....don Allah ya kamata ace duk sanda zaka zo ka fara sanarmin tukunna kafin kazo din"ta fada kanta tsaye tana yamutsa fuska murmushi ya saki gami da dan duqar da kanshi qasa yana wasa da duwatsun dake shimfide a qofar gidan,baice komai ba sai murmushin da yaci gaba da fitarwa yana tattaunawa shi da zuciyarsa,tabbas yasan wannan rana na nan tafe,fiye da haka kuma na nan zuwa nan gaba kadan,wannan ba baqon lamari bane a gareshi,zulaiha ba itace mace ta farko da makamancin hakan ta faru tsakaninsu ba,saidai bazai yanke mata hanzari ba,zai jirata har zuwa ranar da zai zata furta kota yanke alaqar dake tsakaninsu da bakinta,sai bayan daya kammala wannan tunanin sannan ya dago ya dubeta

"Shikenan....babu damuwa...kiyi hakuri" ba tare data tanka ba ta juya tana niyyar komawa cikin gidan nasu

"Ki gaida maaman idan kin shiga"

"Zata ji" ta fada gami da jan qaramin tsaki can qasa ta shige gidan gami da rufe qofar gidan garam.

Kai ya girgiza bayan shigewarta cikin gidan yana sakin murmushi tare da cije lebansa na qasa,cikin qwarewa ya haye saman babur din bayan ya tadashi ya figeshi cikin gudu ya fice daga layin,zuciyarsa cike fal da tunani da mamaki,mamakin da har yau yaqi barinsa,tsahon shekaru kenan wannan abu na daure masa kai,da gaske haka rayuwa ta koma?,ya gode Allah da baiyi gaggawar yiwa hukunci wa rayuwarsa ba.

Titi ya hau ba tare da yayi wata doguwar tafiya ba ya soma sauka daga kan kwaltar zuwa gangaren titin,daf da wasu jeran baqaqen motoci da farare a qalla guda biyar ya soma qoqarin tsaiwa,wanda tun kafin ya kai ga tsaiwar wasu matasa kimanin su bakwai sanye da coat baqi da fari suka doso shi,kowanne fuskarshi manne da baqin gilashi wanda hakan ya sanya baka iya ganin qwayar idanunsa,ya kuma qara musu kwarjini qwarai,daya daga cikinsu shi ya riqe babur din sanda ya sauka,yayin da dayan ya matso kusa da shi yana bude masa qofar daya daga cikin motocin wadda duka ta fisu kyau da girma,sai da yaga ya shiga sannan ya rufe masa qofar,sauran suka zagaya suka shige ragowar motocin nasu,yayin da daya daga cikinsu shi kuma ya haye babur din ya bisu a baya.

"Ya dai,akwai wani sauyi ko ci gaba kuwa yau?" Wani kyakkyawan matashi wanda aqalla zaiyi shekara talatin da hudu dake zaune daga corner motar riqe da magazine ya fada yana dubanshi,fuskarshi na nuna alamun dariya yakeson yi,takalman qafarsa ya soma yunkurin cirewa gami da agogon hannunshi ba tare daya dubeshi ko ya amsa masa ba,ya dannan wani madanni dake gaban sit dinshi,wani qaramin akwati ne ya fito ya zuba agogon takalmin harda wayar dake hannunshi qirar VIVO bayan ya kasheta,ya maida akwakwun muhallinsa ya jingina da makarin kujerar sannan ya waiwaya ya dubeshi

"Me kake tunani mahmoud?,ita dinma kaman sauran,abun ma kamar yana sake lalacewa ne" ya qarashe maganar yana lumshe idanunsa tare da sauke numfashi

"Duk inda xaka je ka dawo dai shawarata ce kan hanya,na sha gaya maka ka sauqaqewa kanka walaha,ka laluba cikin familynka,akwai gomayyar 'yammatan dake sonka ka zabi daya cikinsu ka huta,kaga wannan babu wani fargaba tattare da kai,duka ana tare". Kansa yaci gaba da girgizawa ba tare daya bude ido ya kalli mahmoud ba,tsahon sakanni tamkar bazai amsa mishi ba sannan ya ware idanunsa yana duban sit din dake gabansa

"kana tunanin qaramin abu ne ya sanya na guje musu dukkaninsu na xabi inbiyo ta wannan hanyar?,su dinma kusan duka abu guda ne,babu wani banbanci,halayyar daya ce dai kaman yadda sunansu yake daya,abu guda dukkaninsu suke wa,manufarsu guda ce......" Maganar tashi ta katse sakamakon shigowar kira wayar tasa,ya maida qwayar idanunsa ahankali kan wayoyin dake zube a gefansa,kusan lokaci guda idanunsu shida mahmoud suka sauka kan wayar RAMLA sunan dake yawo kenan bisa screen din,murmushi mahmoud ya saki ganin ya kau da kanshi tamkar ba cikin wayarshi kiran ya shigo ba

"Yallabai ka daga mana?"

"Qyaleta kawai" ya bashi amsa kai tsaye gami da danna wani madanni,wani dan qaramin abu mai kama da fridge ya bayyana,cikinsa nau'ikan abubuwan sha ne masu sanyi da duka duka basu wuce gwangwanaye da kwalba goma sha biyu ba,daya a ciki ya dauka hadi da cup ya maida abun muhallinsa ya koma ya jingina da kujera ya tsiyaya yana kaiwa bakinsa ba tare da yabi ta kan qorafin daga waya da mahmoud ke masa ba,a maimakon hakan ma sai ya maye gurbin qorafin nasa da tambaya

"Jirgin qarfe nawa zamu bi ne?" Tunda ya masa hakan yasan bai bukatar xancan,saboda haka shima ya tayashi

"Yanzun airphort din muka nufa ai,tunda duka duka awa guda da 'yan mintuna ya rage lokacin tashin jirgin ya cika"

"Ok,kafin nan mu biya na sauya kayan jikina"

"Ba matsala" ya fadi yana gayawa driver inda zasu fara zuwa kafin su isa airphort din.

A nutse ta miqe daga saman abun sallar tana sakin 'yar qaramar hamma tare da furta "a'uzu billahi minash shaidanir rajim" gami da ninke daddumar ta mata ma'ajiya a muhallinta,zare hijabin jikinta tayi tanayi tana duba agogon dake maqale a bango saboda gudun makara,qarfe shida na safiya ya nuna mata,hakan ya mata dadi ta tabbatar kafin lokacin tafiyarsu makaranta ta kammala dukkan abinda zata yi din,gyara dankwalin kanta tayi wanda ke niyyar zamewa saboda santsinsa da kuma santsin sumar kanta,sannan ta zura slippers ta bude qofar dakin nata ta fita a hankali.

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Dangantakar Zuci Complete by Safiya Abdullahi Huguma

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post