[Book] Duniya Ta Complete Hausa Novel by Asma Baffa

Duniya Ta

Title: Duniya Ta

Author: Asma Baffa

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 752KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Ku dauki littafin marubuciya Asma Baffa mai suna "Duniya Ta" complete hausa novel text document. A littafin dai bai wuce batun soyayya ake yi ba a cikinsa kamar yadda aka saba.

Book Teaser: Zaune suke a wani katafaren Palo na Alfarma,Palo Wanda yaji furniture Dan gaske,duk Wanda ya Shiga wannan Palo bazai so Fitowa ba,wani uban kamshi da sanyi ne ke tashi,Family Guda su Shida rakacal sai ta bakwan Yar karamar yarinya tana Wasa a kasa,Kidan Bob merly ne ka tashi a wata katuwar plasma tv kamar ka dakko mutum,gaba Daya sunyi Shuru duk Basu cikin nishadi,Ahmad Dake narke cikin luntsumemeyar kujera shine yake kada Kai cikin maye da kwaya da gani kasan Kansa ba kalau ba,sai bin wakar yakeyi da bakinsa,gashi babu Wanda ya Isa yace ya kashe ko ya daina,baya Jin Maganar kowa,Mummy dattijuya itace ta nisa fuskarta dauke da damuwa Tace Haba Ahmad Kaine fa babban Danmu Amma ka duba yanda ka maida kanka Completely Useless har mun gaji da Dake Hanya tun daga Lagos muna zuwa Nan Kaduna wajenka akan magana Daya kaki ji,tunda hakane yau da Yamma zamu koma,Wani farinciki ne ya bayyana a kyakyawar  Fuskarsa,ya Mike tsaye yace wow Mama the Mama,Allah yau zaku tafi?yawwa Haka nake so sabo da na samu freedom,yau kwananku biyu Kun dameni dama,Shut up Daddy ya Furta banzan yaro marar tarbiyya,ai Kai dama Daddy nasan baka so na,Zama ya sake Yi Yana bin wakar Bob merly,sai Chanel din Suka cire wakar aka Sako tallan Wani body lotion.

Wata Uwar Tsawa Ahmad ya saki tare da nuna Tv da yatsa cikin mayensa na giya da kwaya ya kalli dalleliyar Budurwar da aka Nuno tana tallan Body lotion a tv yace Kai...dalla ku matsa can Kar ku kawo Mana Harkar Daudu anan,mu ba Daudu Muka zo gani ba Ana Harkar arziki zaku zo Mana da Mata Yan Daudu,ke dalla ja can, Dan uwarki a Nan Nigeria muna da man shafawar mu Habiba yawwa,Muna da Habiba Muna shafawa Muna Kara Baki wuluk abin mu yafi Mana,Dariya ya Bawa duka Yan palon har Daddy ya kalle shi yace Ahmad Kai da kake fari Kal jinin Larabawa Kuma a gidan uban wa kake shafa wannan Man,sannan ce maka aka Yi Habiba karamin company ne? Mummy Tace Allah ya shirya min kai,Baki ya turo tare da gyara Ass down dinsa da yayi da wani Creazy jean.

Wata Yar kyakyawar jar mota ce Honda tayi parking a bakin wani Restaurant,Yar kyakyawar Budurwar ta fito Hannunta dauke da Handkerchief tana goge zufa, Hannayenta ta Shiga tafawa tana Waka Sannu da Zuwa.....Sannu....da zuwa kekashashe na,Oyoyo Dan Kedararre na.....Oyoyo Karmashashe na,Barka da dawowa Dan tsomalalle na,My Karmash I miss you,Wani saurayi ne matashi mugun siriri wuyansa kamar murkin laima,Kugunsa Kamar zai tsinke,Baki ne wuluk Kamar Iska zata dauke shi Haka ya fito daga jar motarsa Yana wani basarwa a dole babban yaro,Bakinsa ya Bude da Niyyar magana Yan hakoransa manya na gaba Guda hudu Suka yo waje,Yana kallon Budurwar yace naga Alama Baki da tarbiyya,Kamar Ni saurayinki Ina sonki kina so na Amma kina ci min Fuska,glass dinsa ya zare a Fuskarsa ya kalle ta sama da kasa yace Yar talakawa Dake matsiyaciya ki kalle Ni kina wani ce min Oyoyo Karmashashenki? Baki da Manner? An fada Miki badan so ba Zan iya tsayawa da Yar matsiyata irinki? Ki kalle Ni nafi karfinki ta ko Ina,Yar budurwar kyakyawar gaske fara Tace Kayi Hakuri Wasa nake maka wallahi badan naci fuskarka na fada ba,Tsawa ya daka Mata yace dalla ja can dama iyayenki Basu Miki tarbiyya ba,Baki da hankali dai,Ran Budurwar ya baci tace kaga Malam na maka tauna na maka hadiya baka gani ba,to naji bani da tarbiyyar sai kace Iyayenka suzo su Yi min,daga na maka Wasa Kai baka San wasan masoya ba,wannan ne wasan a gidan uban wa ya Zama Wasa? Nan take Budurwar ta bashi amsa a gidan Ubanka Kamalu,Baki Bude ya kalle ta yace Aamna a gidan wa kika ce? Wacce aka Kira da Aamna ta sake cewa a gidan Ubanka nace Kamalu,Kamalu ransa ya dugunzuma yace it's over between me and you,bani ba ke,Aamna Tace ae naji Nima bani ba Kai tsotsatsen banza,me zanci da Kai dama idan anyi auren ma Banda kashinka ya dinga suka na me zanyi,Dana kwanta a jikinka gwara na hau katifar fasasun  kwalaba,Kuma da na aureka ka min kiss da bakinka me hakora Kamar kacar Keke gwara na tsotsi Kusa me tsatsa,Yace irin na Ubanki ne ai hakoran,naji ta furta tare da koma cikin Restaurant taci gaba da aikinta.     

Wajen masu girkin taje ta faki idonsu ta saci yankan nama Uku ta watsa a Jakarta ta fito ta baya can ta cinye Naman sannan ta dawo ciki ta Iske Fried rice an Gama an kaiwa wani yaci ya bar Rabi kadan ma ya ci,Aamna da sauri tazo Wajensa Tace Alhaji ka Gama Zan gyara wajen 2pm yanzu resturant zai cika,kafin yayi magana ta sunkuce abincin ta dauke Masa lemon da ko budewa baiyi ba ta Sha kwana tayi ciki,Alhaji ya saki Baki Yana cewa ke ke ke ban Gama ba Amma Ina Aamna tuni Taki ma kula shi,tana zuwa Tace Alhaji ya koshi ta zauna ta lashe abincin ta Balle lemon ta shanye sannan ta fito fes da ita da mamakinta sai taga Alhajin Bai tafi ba,da sauri ta koma Wajensa Tace Alhaji wani abincin Za'a kawo maka ne? Alhaji ya kalleta yace ke Amma wacce iri ce bance na koshi ba kin dauke abinci lemon ma Dan wulakanci ko Bude shi banyi ba kin dauke Ina ta kiranka bakya ji? Aamna Tace eyya Allah sarki kayi Hakuri matsalar kunne gareni banji ba Kuma gashi na zuba komai cikin shara bare na dawo maka da shi,Harara ya balla Mata tare da zube wani kudin yace kawo min wani abincin,da murna ta dauka dama Bata koshi ba,taje ta hadowa Alhaji duk abinda ya bukata,wata white rice with salat ga kwai da kaza,ga lemo,Aamna tunda taga Haka take ta faman zaga wajen da mopper a Hannunta Wai a dole gyara takeyi,tana ta faman goge goge a saitin Alhaji,Alhaji yace ke kin dameni da goge goge ga customers can sunzo kije Mana Haba wannan wacce irin Maaikaciya aka dauka Haka idan bakya so sai na daina zuwa cin abinci a wajenku aikin banza,Aamna tayi murmushi tare da gyara pcap dinta Tace afwan Alhaji ta juya ta tafi Amma sai ta labe a bayan wani lungu daga ciki tana ta kallon Alhaji tana so yayi ya Gama ta samu rabonta,Siyama ce kawarta taje ta sallami wasu customers din Aamna tana labe tana zalama wajen Alhaji,Siyama tayi Dariya tare da kallon Aamna tana labe labe Tace Allah ya shirye ki,Alhaji kadan yaci ya bar komai ya tafi kafin ya Gama fita tuni Aamna ta kwashe komai tayi ciki,Nan ma ta zauna ta cinye ta koshi sannan Tace saura na dare kafin na tafi gida,dole na dinga kiba Ina yin kyau,Aiki a restaurant ai Dadi gare shi ko ba komai Zan cika tumbi na.

Dattijo ne fari me gemu sosai Wanda shi kanshi gemun ka kalla kasan Dattijon ya tsufa domin yayi fari,da gudu gudu sauri sauri ya shigo gidansa inda yake wani mugun Rubabben gida,Gida ne na Haya Kuma gidan Talauci,da gani ba sai an fada maka ba Dattijon Talauci ya Gama da shi,cikin Gida ya Fado Yana masifa tare da furta me zangani Aishatu?me zangani yau,wacce ya Kira da Aishatu ta kalle shi shekeke tare da balla Masa Harara Tace mene? Gashi can kina karar min da kudi,kina min asarar Duniya da Almubanzanranta,yanzu ki duba sabo da Allah tunda na taho Ina kallon kwalabati kumfar Omo tana ta bin ruwa tana ficewa Ful...ful,Yanzu a zamanin Nan kumfa ka gani a kwata kasan kudinka ake kashewa,kina ta kashe min kudi kina abinda kika ga dama,Ga jarabar karar da Ashana kiyi ta kyastata sai ta Kare,Takaici na yanda kike wanki ko wanke wanke sai asarar Omon bala'i,to wallahi da sake baza ta yuwu ba,kullum Ina fama a hanyar sakateriya wajen Dan aiki na Wanda masinja ne ni nayi retired Ina nemowa Ana wulakantawa bazai yuwu ba,Daga yau ko mangyada ne za a zuba a abinci to kowa cokali Daya Daya babu kari aikin banza,Wata buta yasa kafa tare da yin fatali da ita Yana zare Ido yace Ina Aamna sakarai da Sweety Zuhra?Aishatu banza tayi Masa ta ci gaba da aikinta,yace Aamna har yau ba labarin Mijin Aure?

Aishatu tayi Shuru,Dattijon yace na gaji da yahudanci wallahi da nasan Haka ne Aamna ko secondary baza tayi ba,Dan fa Kawai Ina tunawa Amana ce a wajen mu, Nima ban San ya akayi basirata ta toshe na biya Mata har tayi wani HND sabo da asara,ai karatun mace Bai da amfani,amfanin mace aure da girki tayi ta zazzago Haihuwa,yarinya ta Zama bayahudiya abinda taga Dama shi takeyi,Nima jarabata ce tasa Rana tsaka Ina Kauye tare daku cikin sutura na dawo damu Birni na Kama haya,da Muna Kauye da tuni hankalinmu kwance,da duk wannan karyar Bamu shige ta ba,Aishatu Tace ai sai Dana fada maka kaki ji Aamna tana secondary a Kauye Ss3 ka kwaso mu Muka dawo birni gashi yanzu ta waye Taki aure muna ta ciyar da ita a banza ,wallahi baza ta Sabu ba,gidana ya koma na yahudu bazai yuwu ba,ai Birni na dawo ne Kawai Dan na samu sana'a me kyau to gashi hakan Bata samu ba,Dan pension Nawa ma baya Isa Nawa yake Ina abin,kullum sai talauci ne ke karuwa,birni kwai masifa Ni tunda nazo banga wayewar ba,ban wani waye ba,Aishatu Tace yo shekarar mu Nawa a Birnin kwata kwata shekara hudu fa rak Ina wani wayewa Aamna da Zuhra ne Kawai Suka Dan waye Dake su Yara ne,Dattijon yace ke tafi can Aamna Ina ta waye ai gwara Zuhra,Amma Aamna kina gani magana ma Bata iya ba ta Kauye takeyi duk abinda yazo bakinta dankarawa mutum takeyi Dan tayi makaranta ne ma take Dan canjawa,ni dai na fada Miki a kiyaye asarar Omo yawwa ya furta tare da ficewa falau falau da rigarsa doguwa ta wani tsohon yadi dinkin wani falkeke komai ta Masa yawa

Kuka Aamna ta saki Wiwi tana Hawaye tare da nuna Budurwar da Hannu tana masifa tare da Furta In Allah yayarda Shedan sai ya sumbace ki,Shedan sai yayi kissing dinki,muguwa,Azzaluma, maciya Amana,Baza kiga dai dai a rayuwarki ba Saratu,Saratu anyi asarar Duniya,An Sarai asarar duniya,Shegiya wacce Shedan yayi Mata fitsari a Kai, Wacce ake Kira da Saratu murmushi ta saki tare da karkada key din motarta Tace nafi karfinki Kina talaka kucaka me Deeni zaiyi dake duk kudinsu,ke wawiya ce Baki da hankali da har kina me siyar da Abinci a Restaurant kike tunanin Dangidan Dan Majalisar jaha Deeni zai so ki,ai ko kansila Aamna bazai tayaki ba,ganinki kyakyawa Fara Wai zai sa samari su soki? Kinyi kuskure Aamna,ai yanzu samari sai masu kudi suke Nema gidan da Suka gaji arziki,ai yanzu sai kana da kudi ake rayuwa da kai,ke Dan Dakikiya ce tunaninki kyau Yana sawa a so mutum? Dan kina da kyau har Shishigi kike Yi to ki sani samari sai dai su yaudare ki Amma yanzu duk munin masu kudi Haka ake aure su,Talaka ma Bai son Auren talaka bare irin su Deeni masu kudi,Ina Baki shawara ki fita Harkar Deeni ba ajinki bane.

Aamna tana tsaye sanye da Jean skert Blue da rigarta T-shirt fara tas me Rubutu Red a Gaban Rigar An saka A&G Food Joint,ta Sanya pcap Red takalminta ma Red,ba karya Aamna karshe ce a kyau,haskenta me kyau ba fari Kal Kal ba Amma fara Ce dai ba Wanda ya Isa yace wankan tarwada ce,dole dai farar ce,Gashinta har gadon baya Baki wuluk,Ga Zararan gashin Ido tare da kwantaccen Gashinta dake goshinta,Girarta wuluk me yawa,Hancinta me kyau bai cika tsayi ba,Fuskarta ba doguwa ba baza Kuma ace Round face ba,Dan Bakinta gwanin Sha'awa Karami with pink lips,Gata doguwa Amma ba can ba,ga Uban Hips kamar ita tayi kanta komai nata me kyau,hakoranta kanana farare tas,Idonta dara dara, Mashaallah,Aamna baza ta wuce 24years ba,Haka kanwarta ma Zuhra kyakyawa ce Amma ita chocolate ce kamarsu Daya da Baba.

Murmushin takaici Aamna tayi Tace ai gaki Nan da Muni yayi Miki yawa Deeni zai kwasa ki cinye Deeni please ta juya tare da komawa Kan bakin aikinta wurin masu siyen abinci,ita kuwa Saratu Tsaki ta ja tare da Bude dalelleliyar motarta baka ta Shiga sannan ta fisgeta a Tamanin.

Sai 11pm ta tashi a Aiki ta saka After dress dinta me Dan kyau tare da rataya handbag dinta tayiwa abokan aikinta Sallama ta wuce gida,Napep ta Shiga zuwa gida,can cikin wata Unguwa ta masu rangwamen gata aka sauke ta a Kofar gidansu na Bulon siminti Amma ka rantse kango ne baiyi Kalar gida bane,da Sallama ta Shiga da kyar aka samu aka amsa mata,Mama Wato Aishatu ta Iske tana Daura Net a dakin babansu Tace Mama na dawo,Tsaki dattijuwar ta ja Tace to sai me,idan da sabo ta Riga da ta Saba,Baba ta kalla Yana daki Tace Sannu Baba,da kyar ya amsa,Kai Kawai ta girgiza ta wuce kitchen Nan ta Iske abincinta an zuba Mata Amma an barshi a Bude baza a iya rufe Mata ba,ta Saba Kawai ta dauka tare da Fitowa sai ga Daya matar gidan tunda dama gidan Haya ne,mutum Uku ne a ciki ko wacce mata da dakinta biyu da kitchen Amma toilet Guda Daya ce du,Gaisawa Suka Yi Tace Maman Zeenat ya gida,Tace lfy Alhmdllh da fara'a, dakinsu ta wuce ta Iske kanwarta Zuhra tana kwance a saman katifarsu tana chatting da saurayinta Wanda zata aura Nan da wata daya.

Murmushi Aamna tayi Tace Zuhra Ana Shan love, Murmushi Zuhra tayi tana juyi Tace Aunty Aamna an barki a baya wallahi,Soyayya tayi a rayuwa,Adam ne ke kashe Ni da zafafan kalamansa masu sweet,Dariya Aamna tayi Tace na tayaki murna kanwata ke kin samu Miji Ni kuwa kin barni nice Kuma yayarki gashi Mama da Baba sun tsaneni akan ban kawo musu Wanda Zan Aura ba,Hawaye ne ya silalowa Aamna Tace why me naaa?why Me Zuhra? What have I done wrong? Tausayin Yayarta ya Kama Zuhra Tace kiyi hakuri Aunty Inshaallah kema Zaki samu miji very soon,Kuma Inshaallah su Mama zasu hakura su daina fushi da ke.

Kai Aamna ta girgiza Tace Zuhra Ni bazan iya auren Wanda bana so ba,da Zan Iya Dana fitar da ko ma waye Dan na farantawa Iyayena Rai Amma idan nayi bazan iya yiwa Wanda bana so Biyayya ba,Illar Hausawa kenan Allah Bai kawo maka Miji ba a takura maka karshe har sai ka auri Wanda baka so,baza ka Dade ba za a sakeka,ko Kuma kullum ku Kare a fada da sasanci,bana fata inyi aure na fito Zuhra,Nafi so ko wa Zan Aura ace Ina sonsa sosai sabo da shine kadai Zan iya Masa Biyayya,kin San halina Ina da taurin Kai,Kuma Ni ba a iya tankwara ni,So shi kadai ne zai sa nayi Biyayya,Kin San idan bana son mutum wallahi zanci ubansa ne,Amma su Mama sun kasa fahimtata,Zuhra Tace ai ke matsalarki kenan Aunty akwai saurin fushi ga rashin barin ko ta kwana,aure Kuma sai Hakuri,Hakuri na Kawai na auri Wanda nake so ko jibga ta zai nayi kullum Zan zauna Kuma bazan ji Haushin kowa ba.

Mama ce ta fado dakin Tace Ina Jin duk abinda kuke cewa,ke Zuhra ki daina saurarar marar hankali,ai yanzu ba auren kauna akeyi ba dubawa akeyi aikin mutum ake dubawa me yake samu,zai Iya rike ki, ci da Sha shi ake kallo ayi aure,ke soyayya Zaki aura Zaki ci ubanki kuwa a hannun maza,kika sake  sai Namiji ya sa Miki ciwon zuciya,Aamna tace kinji ko Mama bakwa duba Iliminsa da Addininsa Kawai kudi kuke dubawa ayi aure,Baba Yana ji ya tsomo Baki daga dakinsa yace Ni ki tambaya Sanda na auri Uwarku ban taba ganinta ba Haka itama Bata taba ganina ba Kuma gashi Muna tare har mun haife ku,wallahi Aamna kika sake Watarana sai na koreki daga gidana,badan ma kece kike rage min nauyin gida ba da tuni nayi Miki auren Sadaka Kuma wallah Matukar Naga dama auren Sadaka Zan bada ke.

To Baba kuyi Addua Allah ya kawo min na gari,Kuma da kuke cewa Baku ga juna ba aka muku aure ai ku a zamanin da ne Kuma asiri akeyi Ana kafe matar ta zauna dole,Salati Baba ya saki yace Ni Zaki hada da shirka Ina Dan Izala? Shuru Aamna tayi,Mama Tace mayaudariyar banza,kin Yaudari Affan kin Kore shi kince kin Kama shi da cin Amanarki Yana kula Mata,Hassan Kuma kince Dan karya ne,Deeni ma yaro me kudi yanzu kince ya yaudareki ya koma wajen Saratu kawarki Yar gidan Alhaji Sani Likita, yanzu ga Kamalu kin ci Masa mutunci ya gudu shima,Jollof din shinkafata wacce ta rigada tayi sanyi ta bushe ita Aamna ke ci su Mama suna ta mata fada har ta Gama,ta cire kayan jikinta gaba Daya ta wanke tare da shanya su a daren,Wanka tayi da ruwan zafi tare da Shirin bacci ta kwanta ta bar Zuhra tana chatting da masoyinta .

Dalleliyar mota ce ta gaske wacce a kalla ta miliyoyi ce,ta danno cikin wani katafaren gida na Gagara,Gida ne Wanda ya amsa sunansa,Babu abinda babu a ciki,motoci ne zasu Kai takwas a gidan Wanda suka gaji da haduwa ga tsada,farare Guda hudu a jere bangare daban Haka ga wasu kaloli daban,Machine ne Guda Uku kala daban daban masu tsada harda Keke na masu kudi su biyu,Gidan Ya gaji da tsaruwa ga flowers ko ina,idan ka Shiga gidan baza ka so Fitowa ba,Kalar gate din ma na daban ne,ba ko Ina ake ganin Irinsa ba a kasar Haka furniture sai dai ko gidajen Gomnoni, Wani Matashi ne ya Bude motar baka Daya shigo da ita,Fitowa yayi da kyar Wow wani Fari ne tas kamar Balarabe har wani ja yake kamar ka taba shi jini ya fito,dogo ne Amma ba can ba,gashi shi ba Mai kiba ba baza ace Kuma siriri ba,Fuskarsa me dauke da hancinsa zarkadede ba irin me tsayi da yawa ba,Sumar Kansa baka wuluk dauke da wani mayen Aski irin na Yan duniya,an kwashe gefe da gefe an yanki wani waje siriri an Kona shi tare da maida shi Fari tas,Sajensa me kyau luf luf me dauke da Dan gemunsa cas,idanunsa Dara Dara farare tas suna wani lumshewa,kowa ya kalli wannan matashi yasan ya Gama gajiya da haduwa,Naira da Hutu sun zauna a jikinsa,Jikinsa na maza Wanda suka amsa sunansu maza,sanye yake cikin wani Crazy Jean me tsada gaba Daya wandon a farfashe yake ruwan toka,da wata T-shirt me Rabinta Fari Rabi Kuma Blue,Takalminsa da agogonsa masu tsada,Yatsansa sanye da zoben Azurfa,da kyar yake takawa ga takama ga aji Amma Kuma Yana tangadi da Alama yayi shaye shaye ya gaji,Yana dafa bango Yana tangadi AHMAD kenan a Haka har ya Isa katafaren palonsa tare da fadawa saman kujera ko Takalminsa Bai cire ba ya kwanta Haka Yana sambatun maye shi kadai har bacci ya kwashe shi.

Tunda ya fara bacci gab da Magriba Bai tashi ba sai da gari ya waye sannan Rana da hasken gari yasa ya Bude lumsassun idanuwansa a hankali,Kara ya saki kadan Jin jikinsa a gajiye,da kyar ya iya tashi  a hankali ya haura samansa Direct toilet ya shige ya Dade Yana wanka dake akwai tsafta,Bayan ya fito daure da Towel jikin mudubinsa ya nufa turaruka ne da mayuka na maza masu tsadar gaske,Lotion me kamshi ya shafa tare da fesa Body Spray a jikinsa sannan ya dakko sabuwar jallabiya me tsadar gaske fara sal Amma ta Dan tsangale Masa baya sa wacce zata Kai Masa har kafa sabo da Damunsa takeyi,Turaruka ya fesa sannan ya dauki wayarsa me tsada Yana latsawa,a hankali cikin tafiyarsa ta Isa da takama ya sakko kasa ya Bude kofa ya fito sanye da wani flat shoe fari sal shima Yana tafiya a hankali ya bi ta wani corido gaskiya gidan Nan ya Gama haduwa tiles din kasan gidan na tsakar gida fari da Baki ne ko Ina sheki yake Yi da walwali,Me Gadinsa ya hango Yana karasa gyara gidan Yana kida da bakinsa Yana rawa Yana aikinsa,Ya Dade a tsaye Yana kallonsa,Abin Dariya ya bashi mutum shi kadai Yana kida Yana Waka Kuma Yana rawa duk shi Daya, murmushi ya saki kadan tare da girgiza Kansa ya juya ya koma inda ya fito.

Har yayi nisa sai ya dawo ya Kira me Gadi Musa,da sauri Musa ya dago yace Oga tare da takowa da gudu yazo gabansa yace Ina Peter banga ya gyara ciki ba Sannan ba Abinci,Oga ai Peter ya tafi kasuwa yace abincinka Yana kitchen yace sauri yake yi,Ni gaskiya Oga Ina  tunanin yafi a dakko mace yar Aiki wacce zata na maka girki da gyara maka ciki tunda Ni Ina kula da Campun,Ogan yace ba Campun ake cewa ba Musa Compound,Kuma Ni bana bukatar mace yar aiki,Ni bana son mace ta rabe ni,duk abinda zai sa na hadu da mace bana kauna,Musa ya zaro Ido yace Oga Mata sune Jin dadin duniya duk wata nutsuwa da Namiji zai samu tana jikin mace,Baki Ogan ya tabe yace Allah ko? A wajen wawaye ba,gwara naci abincin Gardi akan naci na mace,Karka sake furta kalmar Nan mace a gaba na,idan ba Haka ba Kora ce tukucinka,Musa yace an Gama,Kayi Hakuri Ranka ya Dade Namiji gwara nace Namiji,macen banza Banda Mum dinka Oga,Baki ya tabe ya juya da Gadara ya wuce,Abincin Peter ya Bude yaga Bai Masa ba,da Kansa ya shirya Girkinsa da lafiyayyen tea dinsa ya karya sannan ya dauki key din mota yayi waje,Yau da wata mota Ruwan toka ya fita kirar Benz.

Washe gari Aamna wanka tayi tare da Shiryawa tsaf cikin kayanta Riga da wando sunsha wanki da guga,After Dress ta Dora a Kai tare da yafa Mayafi,ba Wanda ya kalle ta a cikin Iyayenta Balle Tace Za'a Bata wani abinci dama yanzu basa kulata,ko ta gaishe su basa amsawa,Sallama ta musu ta tafi,Mama Tace yarinyar banza ace tasan Burin mu Bai wuce mu Aurar da su ba Amma Taki fitar da Miji abin kunya kanwa zata Riga Yaya aure duk ta tsufa a gida Allah wadaran Dan Riko,shekara ashirin da Hudu ai ba Wasa bane,mu duk da a cikin birni muke muna Nan da akidar mu ta Iyaye da kakanni na auren wuri Amma kash Yaran namu musamman Aamna ta Gama watsa Mana kasa a Ido,marikinta Bai da Buri sai na Aurar da su,ai mutuncin ya mace gidan Miji Amma ba komai Aamna wahala da azaba ma Sai ta sa kin fito Mana da Miji,kin daina Jin dadin gidan Nan kwata kwata,yanzu Zan canja Taku wajen gana Miki azaba duk da Kamar  mahaifiyarki ce Ni dole wahala tasa ki fitar da Miji,Zuhra kuwa Shiryawa tayi tuni tayi Kari me kyau Ana ta nuna Mata gata da kauna ta tafi makarantar Boko Wato Secondary school sabo da sun kusa yin candy.

Ahmad Bai tsaya ko Ina ba sai gidan Mashkoor inda Suka Fi Zama suna shaye shaye a gidan,can ya Iske abokansu su Biyar Mashkoor, Abdul Tawaga,Jibril Jibson,Bashir Bash, Mubarak Brown sai shi Oga Mai gayya me Aiki Ahmad King,Yana zuwa ya Iske su a zaune a Garden suna zaune a kujeru ga karamin Table an zube kayan maye na shaye shaye kwayoyi da giya iri iri ga Sigari taba da Wiwi,Kirari suke Masa Suna The King...Our King,shi Kuma Yana uban Gadara Abdul Tawaga ya Daga Masa kujerarsa ta tsakiya Kuma kujerarsa ta mulki ya zauna tare da Balle kwalabar Giya ya Shiga tiltila Kamar ya samu ruwa,Bash ya kunna Wiwi Yana zuka ga wasu kwayoyi Daya hada a cikin wani ruwan giya Yana korawa Yana tiltilo hayaki ta Hanci ta Baki cikin kwarewa,Tawaga Yana Aswaki Yana cijewa Yana karkace Baki yace Our King....Sweet Boy,The Handsome King,Fresh Boy, shi kuwa King ya kalli Kansa yace Na me....Na me My Guy,Look at my skin color....

Mubaraq Brown yace Handsome King,Mashkoor Yana wani tangadi a zaune yace Our King ka huta baka hura hayaki sai ruwa Kawai kake bulbula sai kwaya,King ya wani girgiza Kai alamar ya fara daukan chaji shima yace,Hayaki sai dai na shaki na Titi My Guy, Mashkoor yace Look King akwai wata yarinya tayi Fuck Up,the Girl done Mess up man, Wai Ni Ina sonta Tace Banda hankali wani yaro Rabiu Yana Nan malamin makarantar Islamiyya ya kwace min ita,King Yana lumshe Ido duk ya fita a hayyacinsa ya karkace bakinsa gefe Daya irin na Yan shaye shaye cikin kakkausar da mayen muryarsa yace She must Collect,Dole ta karbi Certificate na abinda ta aikata,Na yarje muku kuci mamanta,shi Kuma Yaron za a tare shi dole mu bashi Sample,Sumarsa me laushi ya yamutsa,yace guys gobe Mommy da Dad zasu shugo garin Nan Karku zo gida na sai bayan sun tafi,Abdul yace  Confirm,No wahala,Jibril Jibson ya Mike Yana tangal tangal yace ya za ayi ace baza mu zo gidan King ba,The sweet Boy,Cikin zafi da daga Murya King Ahmad yace hey What's up man Ina magana kana magana kana hauka ne? I'm sorry cewar Jibson ya Fadi a kasa Yana mayensa,da ganinsu kasan talakawa ne Ahmad shine me kudin shike musu komai,Haka Mashkoor Yana da kudi shima Amma ba Wani da yawa ba,Sai Abinda Ahmad yace shine King dinsu,duk wani rashin mutunci da sukeyi a gari shine yake daure musu gindi sai da sa hannunsa akeyi,Ba Wanda ya Isa ya nuna su da yatsa,Dai Dai ne Basu San da zamansu ba musamman Ahmad King din Wanda ya fita daban sabo da Naira da hutu,suturarsa Kawai abin kallo ce,Dukkansu baza su wuce 30years ba zuwa 34years,Ahmad 34yrs yake cif.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post