[Book] Gaba Gadi Complete by Jamila Umar Tanko

Gaba Gadi

Title: Gaba Gadi

Author: Jamila Umar Tanko

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 494KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2021

Description: Ina makaranta suke? Ku sauke sabon littafin marubuciya Jamila Umar Tanko mai suna "Gaba Gadi" hausa novel document complete a text format. Har da taba ka lashe muka kawo muku.

Book Teaser: Sun tafi da murna sun dawo da gagarumin bacin rai, bacin ran da ba zai musaltu ba .Tun daga Airport na Malam Aminu Kano da ke birnin kano direban da ya je daukarsu ya fahimci hakan. Babu walwala,  babu Annuri a fuskokinsu.  Ko gaisuwarsa ma basu amsa ba. Haka suka bude bayan mota suka zauna. Hakan ne  ya tabbatar masa cewar Mummy da Daddy babu lafiya abinda bai taba gani ba tunda ya fara yi musu aiki.

"Wai shin meya bata musu rai haka ? Ko sakon rasuwa aka aika musu, don sun dawo da wuri ba kamar yadda suka saba dadewa idan suka je London ba ? Ko fada suka yi a junansu? "  Habibu direba yake tambaya a zuciyarsa. 

Har suka isa gida ko tari babu wanda yayi a cikinsu. 

Wannan bacin ran nasu shi  ya hana su cin abinci balle hira, ko kallon talabijin. Babu wanda yake ganin gilmawarsu tunda kowannensu ya Shiga dakinsa ya datse. 

Kwanaki uku kenan da dawowarsu 'yan sannu da zuwa sun zo ba adadi sai dai 'yan hidimar gidan su ce su na daki su na baccin gajiya, dan haka baa samun damar ganinsu. 

Masu aiki koda yaushe su na jere abinci akan tebur haka suke zuwa su tarar da shi baa ci ba su kwashe, su jera sabo shima kuma a haka zasu zo su tarar baa ci ba . Tabbas jikinsu ya fada musu gidan nan babu lafiya. Domin basu taba ganin irin haka ta faru a rayuwarsu ta gidan nan ba.

Kullum da safe yaransa sai sun shigo don su gaishe su amma sai masu aiki su ce su na daki su na bacci. Wannan ma sabon al'amari ne wanda basu saba gani ba. Kwanaki uku kenan dan haka sun tabbatar ba lafiya ba gashi wayoyinsu dukka a kashe. In ma a kunne ko an kira baa dauka. 

Yaransu su bakwai yau sun hallara a cikin babban falon gidan da zunmar yau sai sun ga mahaifansu ko da kuwa dakin Zaa balla . 

Bugun kofar da suke yi ya karfafa in dai mutum ba bacci mutuwa yake yi ba dole ya farka . 

General Nafi'u ne ya bayyana a bakin kofar dakin fuskarsa murtik babu walwala, babu annuri, idanuwansa sun kada sun yi jajawur, ya wurgawa kowannensu harara yana yi musu duba irin na rashin fahimta.

Su dukka suka duka suka gaishe shi,  bai amsa ba ya kawar da kai gefe ya fada cikin  fushi " lafiya ku ke buga min kofa? Ko na ci bashin wani ne ban biya ba ?" 

Daga Jin wannan amsar sun san tabbas General ya kai kololuwar fushi . Sai suka hau kallon-kallo a junansu aka rasa wanda zai bashi amsa.  Sai Sosa keya da gashi suke yi . 

General ya sake daga murya cikin tsawa " shin wa ya baku izinin ku wuce falo har guda uku, ku zo kofar dakina ku buga min kofa ?

Muhammad ya yi karfin hali ya ce " Oga, kwana biyu  ba mu ganku ba daga kai har Mummy tunda ku ka dawo daga tafiya. " 

Abubakar ya ce " kwana uku ma kenan idan za mu tafi wajen aiki kullum da safe mu na shigowa don  mu gaishe ka sai mu iske baka falo masu aiki sai su ce kana bacci ." 

General ya ce " me ya shafe ku da baccinmu? "

Umar ya Sosa keya ya ce  "ranka ya dade baccin ne yayi yawa kamar ba lafiya ba hankalinmu ya tashi ." 

Aliyu ya ce " gaisuwa ce baba ." 

General ya ce " ku rike gaisuwarku ." 

Ya na fada ya buga kofa ya rufe dakinsa. Ya barsu anan a tsaye aka hau kallon-kallo. 

Usman ya kwashe da dariya "yau Boss fa ba kanta.  Me aka yi masa haka ne ? " 

Muhammad ya harari Usman ya ce " kada ka sake yi mana dariya ba abin dariya ba ne . This matter is serious. " 

Mu'awiyya ya ce " normal ne kawai , ku zo mu kauce kawai sai ya yi normal  ma dawo ." 

Hamza ne bai ce komai ba ya yi shiru kawai yana tunani ya juya ya nufi kicin ya sami masu aiki yana jero musu tambayoyi game da matsalar da take afkuwa a cikin gidan nan. Rabecca ta zaiyana masa duk abinda suka lura da su tun bayan dawowarsu daga tafiya.

Hamza ya fito a Sanyaye, a falon farko ya sami 'yan uwansa a zazzaune su na tattaunawa.  

Abubakar ya zabura ya kalli Hamza ya ce "ka tambayi masu aikin abinda yake faruwa ? " 

Hamza ya gyada kai ya ce " sun shaida min tun ranar da suka dawo daga tafiya basu kara cin abinci ba kuma basu sake jin motsin su ba . Kowanne yana dakinsa ya kulle. " 

Suka zauna har tsawon awa guda su na tattaunawa akan yadda Zaa shawo kan wannan matsalar don a samo mafita . Hakan ya cinma ruwa . Gashi gaba daya wajen aiki zasu tafi kasancewar yau litinin har wasunsu ma sun makara . A dole suka tashi suka watse an tsaya akan a hadu da daddare a cikin gidan . Amma su dukka sun yi amanna Na'ila ce kadai take da amsar wadannan jerin tambayoyin.

Motocinsu tsala-tsala a jejjere guda bakwai haka kowa ya Shiga tasa ya kama hanyar ofishinsa. 

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Kwana Ashirin Da Hudu Complete by Jamila Umar Tanko

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post