[Book] Hafsatu Manga (Yarinyar Kauye) Complete by Khadija Candy

Hafsatu Manga

Title: Hafsatu Manga (Yarinyar Kauye)

Author: Khadija Candy

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 390KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Yau, cikakken littafin marubuciya Khadija Candy muka kara kawo muku mai suna "Hafsatu Manga (Yarinyar Kauye)" complete hausa novel a text document. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: A hakali ta sauko saman Motar fuskarta ɗauke da damuwa. 

"Na gode"

Ta furta murya ƙasa-ƙasa kamar mai shirin yin kuka. Dattijon da ta yi ma godiyar ya ciro wata tsohuwar naira ɗari ya miƙa mata yana faɗin

"Karɓi wannan ki siye abinci"

Sai da ta share hawayen da suka zubo mata sannan tasa hannu biyu ta karɓa tana masa godiya

"Na gode Allah ya saka maka da alheri"

"Babu komai Allah yayi miki mafita"

Cewar Dattijon, mutanen da ke cikin Motar suka amsa da 

"Amin"

Sannan Dattijon ya tashi Motar suka hau titin unguwar Gada biyu, titin da zai sada su da tsakiyar birnin Gusau.

Da kallo ta bi Motar itacen, hawaye na bin fuskarta, sai da ta daina hango Motar sannan ta maida dubanta gurin manyan gidajen da suke gabanta, wata irin ajiyar zuciya ta sauke mai haɗe da kuka mai ƙarfi, kukan da bata san ta ina yake fito mata ba, kukan da ba ta san ranar tsayawarsa ba, hawayen da babu mai share mata su, sai Ubangijin daya ƙaddaro mata rayuwar da ta tsinci kanta ciki. 

Ba ta damu da rashin takalminta ba, ta cira ƙafafunta cikin rashin kuzar tana ɗingishi ta nufi wata ƴar kwarkwaɗar data hango wadda ke tsakankanin gida da gida, cikin kwarkwaɗar ta shige ta zauna saman simintin dake gurin sai ta fashe ta sabon kuka muryar a daƙishe saboda majinar data kama maƙoshinta.

Kuka take mai tsuma zuciyar mai sauraro, kuka mai ban tausayi, kukan rashin Uwa da Uba, kukan rashin ƴan'uwa da abokan rayuwa, kukan rayuwar da ta samu kanta da kuma wanda zata zo mata nan gaba, kukan rashin sanin makomarta, kukan baron duniyar jindaɗi, duniyar dake cike da masoyanta da abonkan rayuwarta, lokaci ɗaya komai ya tsarwatse mata ta rasa komai nata, yau gata cikin duniyar da bata san kowa ba.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga uku na bani na lalace, wayyo ni Allah na" 

Ta furta hakan yafi a ƙirga kamin kuka ya ci ƙarfinta, ta ɗauki tsawon lokaci a gurin tana kuka ba tare da kowa ya kula ba, kasancewar unguwar manyan mutane ce, ba kasafai za ka ga mutane a unguwar ba, sai Motacin dake kai da kawo suma kuma ba sosai ba, mutane dake tafiya da ƙafa kuma tsinta-tsinta ne kowa na sha'anin gabansa, ba kowa ba ne zai kula da gurin da take zaune balle har a iya gano da mutun a gurin kasancewar yamma tayi sosai.

Hakan ya bata damar tausayawa kanta, ta ci kukanta har ta gode Allah ba tare da kowa yaji ba. 

Kiran Sallah Magariba ne ya saukar mata da natsuwa har ta samu damar jan numfashi ta lumshe ido tana sauraren Ladani tana girgiza kai. Yau Magariba tayi mata ba'a gida ba, wasu zazzafan hawaye ne suka fito daga idonta dake rufe suka gangaro zuwa kumatunta. 

A she kayi kuka a kula da kai a baka haƙuri gata ne, ji take kamar wani ya zo ya dafata ya rarrasheta kamar yadda mahaifiyarta take mata a duk lokacin da take kuka, amman ina! Yau ta rasa wannan gatan, lokaci ɗaya haske ya zame mata duhu, fari ya koma mata baƙi duniyarta ta barkace ta zo mata bai-bai, ji take kamar ita kaɗai ce ta rage a duniya, jikinta na bata wani yanayi na daban komai ganinsa take kamar mafarki.

Sai daf da ƙare Sallah Magariba sannan ta fyace majinar data ɓata mata fuska, ba ta damu da share hawayen ba, ta fito daga kwarkwaɗar tana cigaba da ɗingishi. 

Hanyar dake damanta ta kallah kamin hagu, sai shawartar zuciyarta take gurin zuwa, ga kanta babu ko ɗankwali, zane da rigar dake jikinta ma ko wanne daban-daban ne kamar wata sabuwar haukaciya. 

Cikin unguwar ta kutsa kai, ba dan tasan inda za ta ba je ba, ita dai tafiya kawai take tana kalle-kallen manyan gidaje. Tafiya ta riƙayi har ta kusa kaiwa ƙarshen unguwar bata ga gidan da zata iya shiga roƙon mayafi ba balle abinci, a ƙofar wani ƙaton gida ta tsaya tana ƙare masa kallo, babban gida ne da aka ƙawata shi da ƙwayaƙwan lantarki, a gefen gidan kuma an yi masa kwalliya da fulawoyi masu kyau da ɗaukar hankali. 

A tunaninta babu mutane a gidan haka zuciyarta ta nasalta mata, gurin da fulawoyin suke ta nufa, kasancewarsu ba masu tsawo sosai ba, ya bata damar tsallakawa ta shiga ɗan filin dake tsakanin fulawoyin da kuma ginar gidan, zaunawa tayi a gurin zuciyarta cike da rauni da zullumin abunda zai same ta. 

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Bakar Wasika Complete by Khadija Candy


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post