[Book] Kudi Da Maciji Complete by Nazir Adam Salih

Kudi Da Maciji

Title: Kudi Da Maciji

Author: Nazir Adam Salih

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Fiction

Doc Size: 161KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2005

Description: Wani tsohon littafi muka kawo muku wanda marubuci Nazir Adam Salih ya rubutashi tun shekarar 2005 mai suna "Kudi Da Maciji" complete hausa novel book. Tabbas labarin yana da matukar dadi.

Book Teaser: Abakin Wata katuwar fadama da misalin karfe hudu da rabin wata ranar Juma'a ta karshen karni na goma sha takwas wasu jinsin tsuntsaye sukayi sahu sahu abakin fadamar suna ta shakatawa abinsu domin kuwa babu abunda ya dame su don basa fargabar a fada musu da yaki ko kuma a kawo musu hari kamar yadda sauran jama'ar gari keta kwanan zullumin kasancewar wadannan abubuwa guda biyu akansu.

Da yawa daga cikin tsuntsayen dake bakin fadamar neman abincinsu sukeyi yayinda wasunsu kuma keta wanka abinsu wasu ko sai shawagi sukeyi a gefen fadamar suna kaiwa yan kananan kifaye haribko Allah zaisa su dace su sami Abinci.

Acan gefe fadamar daga yamma wani manomi ya jefar da fatanyarsa gefe guda ya mike tsaye ya share gumi kana ya juya ya dubi matarsa wacce ke ta faman aiki babu ko sassautawa kaikace itace Mijin.

Matar ta dago kai ta dube shi a yatsine tace

To Uban malalata yanzu fa saikace harga gaji ko? Na dauka tun duku dukun nazo gonar nan bance nagaji ba saikai dakazo da tsakar Rana.

Manomin ya dubi matar cikin murmushi haba Tagogori ke kinsan Ai nayi kokari ma da na kawo haryanzu ina noma nifa na rigaya na fada miki bazan iya noma ba gara ki kyale ni akan sana'ata 

Tagogori ta dubi mijinta a fusace domin tasan abinda yake nufi Oh Amma dai zangeru wallahi kaji kunya yanzu ace mutum ya fifita SATA akan sana'armu ta Gado Noma?

Zangeru ya dubi tagogori ya fashe da dariya sautin dariyarsa ya watsu aduk fadin fadamar harda dama daga cikin tsuntsayen dake garin suka tashi a tsorace.

Haba Tagogori kin manta da cewa abindana gada kenan tun kaka da kakanni? Ta gogori ta jefar da fatanyar dake hannunta ta mike tsaye sosai ta dube shi kai kasan da tun farko nasan kai BARAWO ne na rantse da Allah bazan fara ma aurenka ba.

Zangeru ya sakato datti daga kogon kunnensa cikin murmushi yace kinga kuwa ni a ganina wallahi duk cikin sa'anninki babu wacce tayi dace da miji kamar ke domin ke kadaice kikayi dacen auren Jarumi.

Tagogori ta turo baki gaba kamar suda wanene Jarumin? Zangeru ya bugi kirjinsa da karfi yabada wani sauti Fuss tsuntsaye suka sake watsewa ya dubi matarsa Tagogori tace Ni Kuwa aganina babu rago kamar malalacin daya zabi sata fiyeda noma dubi fa ciki ne dani wata biyu amma tun hudowar rana nake aiki haryanzu bangajiya ba.

Zangeru ya kurawa matarsa tagogori idanu na tsawon lokaci sannan saiya danki fatanya ya rataya a kafada yace shiyasa nake son ki rabu da wahala amma har kullum inata kokarin nuna miki Annabi kina runtse idanu dubi cikinki ya fara girma amma kullum kina kara cusa kanki cikin wahala ya danyi shiru yana kallonta.

Ganin tayi shiru batace komai ba sai yaci gaba.

Toni yanzu tagogori in banda abinki ma dan abin nan da zamu samu awannan yar gonar nawa yake? Sanin kanki ne acikin dare guda ina iya tara miki abinda zamuyi shekara guda muna ci amma duk in kin bi kin dami kanki.

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Yar Aiki Complete by Alawiyya Ado

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post