[Book] Kukan Kurciya Complete by Bilkisa Ibrahim & Abba Gana

Kukan Kurciya

Title: Kukan Kurciya

Authors: Bilkisa Ibrabim, Abba Gana

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 86KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke cikakken littafin gamayyar marubuta, Bilkisa Ibrahim da Muhd Abba Gana mai suna "Kukan Kurciya" complete hausa novel a text document daga shafin nan.

Book Teaser: Tafiya take tana had'a hanya, kai da kaganta kasan ba,a hankalinta take ba, dan kariyar ALLAH ce kad'ai ke tareda ita a bisa titin, takalmanta rik'e ahannunta, gata dai k'yak'yk'yawar mace dirarriya kuma fuskarta tana nuna alamun hak'uri, wani ihu datayi yasa muka maida kallonmu gareta, tacika hannu dak'asa ta watsa jikinta, tasake kwala ihu saini Ameeda,  d'iyar malam dauda da iya Abu, d'iya d'aya tilo agurin iyayenna, nice tafari nice auta,  yarinya mai farin jinin tallah.

   Bansan sanda hawaye suka zubo bisa kumatunaba, takuma kaikaicewa ta rabga ihu, na girgiza kai dan tabani tausayi matuk'a.

   Mai adaidaita sahu ta tare, cikin muryar 'yan maye ta ce, "gidanmu zaka kaini.

    Mai adaidaita ya yatsine fuska, toni nasan gidan kunne? kifad'i anguwar dazaki malama.

   Tayi shiru alamar tunani, can tađ'ago tana kallonsa da rinannun idanunta, ta ce, "kaga namanta sunan anguwarmu amma muje zan dinga nuna maka hanya.

   Mai adaidaita yaja dogon tsaki yana fad'in saboda nima makakkene irinki ko??, yaja adaidaitarsa yayi gaba.

   Ta tuntsure da dariya tana nuna babur d'in tasa, kaga mahaukacin mutum, amfad'a maka dan ina a bige kwakwalwata bata aiki ne?, jiri ya jata kamar  zata fad'i, tayi saurin dafe wata mota dake bayanta.

  Indai tak'aice muku ta tsaida adaidaita kusan uku amma basu d'auketaba dan jin tamance sunan anguwarsu, da k'yar wani yad'auketa, tako ringa nuna masa hanya dalla dalla har kofan gida, ta zaro d'ari biyu acikin d'ankwalin ta tamik'a masa, yakarb'a yana fad'in toga canjin malama.

   Ta juyo tana kallonsa dan harta fara tafiya, ta ce, " sunana ba malamaba, kuma canji kaje nabar maka duka, tafad'a dad'an k'arfi.

   Mai adaidaita ya jinjina kai yana godiya ya ce, "ya ALLAH yashiryeki kinji.

   Muda muka biyosu abaya mukace amin ya RABBI.

  Cikin gidan tashiga tana tangad'i, iya Abu dake a tsakar gida tana aiki tabita da kallo cikin bacin rai.

   Ameeda tazube agabanta tana fad'in iya taimaka mini da abinci wallahi cikina kamar b'arayin duniya sunmin sata.

    Iya abu ta balla mata harara ke  tsinanniya kada ki bata min rai in abinci kikeso ki koma ki ciwo daga inda kika fito , idan kuma kinje kibar tunawa dani, inkuma bahakaba wlhy yanzu jikinki zaya gaya miki.

   ameeda ta tuntsure da dariya harda bugun k'asa ta ce, "iya aii tsinannun nada yawa dankema tsinanniyarce, na tabbata kafin iyayenki su mutu saida suka tsitstsine miki albarka..

   Kafin ta k'arasa iya abu tashiga jibgar ta tamkar ALLAH ya aikota, itako sai ihu take da kururuwa harda zagi, makwafta suna jinsu, babu wanda ya leko balle a shigo ceto, dan idan da sabo sun saba, babu wayewan gari dabaza'a daki ameeda ba, saidai idan bata kwana a gidanba, dan wata sa'in bata kwana agida,

         duka sosai iya abu tayi mata, saida taga  ko  yatsun hannunta baya motsi sannan tabarta tana cigaba da kalaman tsinuwa da d'ebe albarka ga d'iyar tata.

   Ahaka malam dauda yashigo yasamesu, azatonmu za'a samu rangwame daga garesa, amma saimukaji yana ambatar wannan shegiyar sai yanzu tadawo gida??.

   iya abu dake cin rai ta huro hanci ta ce, "yanzu tadawo zatamin iskanci nazane shegiya.

    Yayi dai dai,yasa k'afa ya shuri ameeda dake kwance A kasa matsiyaciya tashi kibawa mutane wuri, sai kaurin taba kikeyi asararriyan yarinya.

   Na rintse ido nabud'e danjin irin munanan kalami da iyaye ke yima d'iyarsu, lallai dole ameeda ta lalace indai har haka iyayenta suke mata tun tana karama.

   Itako ameeda tana kwance ko motsi batayiba bare ta amsa kalaman baban nata kota bi umarnin sa, ruwa ya d'ebo ya watsa mata, tabud'e idanunta dak'yar,  ya ce, "bacewa nayi kitashi anan ba me kika tsaya kina kallona, ameeda ta mika masa hannu tana fad'in taimaka ka kaini d'aki baba wlhy duk jikina yayi tsami, waccan tsohuwar ta dakeni sosai, kafa yasa ya shureta da karfi yana zagi da tsine mata, ta maida hannunta tana fad'in bakaso natashi kenan, dan nikam bazan iya tashiba, duk cikin yanayin maganar bugaggu take maganar.

   Banza sukai mata suka cigaba da harkokinsu, saida taji rana tafara dukanta taja jikinta da k'yar tashiga dakinta a kofar dakin ta kwanta abinta.................

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Fuska Uku Complete by Sameena Aleeyou{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post