[Book] Kwana Ashirin Da Hudu Complete by Jamila Umar Tanko

Kwana Ashirin Da Hudu

Title: Kwana Ashirin Da Hudu

Author: Jamila Umar Tanko

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 371KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Cabb, a cikin kwana ashirin da hudu jallin jal ake kammala wannan zazzafan labarin soyayyar. Sauke littafin Jamila Umar Tanko mai suna "Kwana Ashirin da Hudu" / Kwana 24 complete hausa novel document a text format.

Book Teaser: Da misalin karfe shida na yamma , hadadden jirgin nan wato KATAR AIR LINE ya sauka da jigajigan masu kudi na kasashen daban daban a filin jirgin sama na croatia.

Croatia kasa ce wadda mu a nan sai mu rantse muce babu talaka ko daya a cikinta saboda kyawun garin, ko’ina ya kawata. Ga kuma farar fatar ‘yan kasar na sake haskaka garin. A gaskiya Croatia bata cika samun baki bakar fata ba, don da yawan masu kudin mu basu waye da xuwa wannan kasa ba, ko don shakatawa ko don kasuwanci, sunfi xuwa London, America, dubai, da kuma uwa uwa Saudi Arbia, saboda Croatia tana da nisa ainun daga Nigeria don ko ‘yan Nigeria  da suka iso cikin jirgin nan suma ta America suka bi sannan suka iso wannan kyakkyawar kasa mai dumbin arxiki.

Ma’aikata nata kai kawo bayan saukar jirgin don ganin an bude matafiyan dake ciki sun fito kowa ya kama gabansa. Ana ta saukowa daga jirgi har yanxu dai babu bakar fata duk sai turawa majiya kudi da mulki su matansu da ‘ya’yansu. Wadanda sukaxo taryen su sunata murna suna rungumarsu kamar yadda suka saba gaisuwarsu. Atika sadam, mannira bala da axixa adam abdulfatah sune suka fara sako kai suka sauko daga jirgin, bayan sun sauko ma’aikatan da suka dauko musu kayayyakin su suka bisu har xuwa wajen wata dalleliyar mota baka mai walkiya kamar yau ta fito daga kamfanin da aka kerata. Da wasu turawa guda biyu bakar fata guda daya yana rike da wata katuwar takarda wadda aka rubuta welcome to Croatia Axixa, Mannira, Atika yana ta dagawa, ma’ana bai sansuba shima , amma idan suka ga sunayen su sun san su aka xo tarya don haka da suka ga sunayen su sai suka doshi wajen da suke. Suna xuwa Mr Johnson ya tare su da murna da fara’a, y mika musu hannu sannan cikin harshen turanci yace “sannun ku da xuwa” atika saddam ce a gaba, da ita suka fara gaisawa sannan ta mikwa dayan baturen hannu mai suna Mr brown sannan ta matsa kusa da wannan bakar fata dake tsaye a gefe mai suna Ashraf, da alama mai aikin su ne ko kuma direban su, ta mika masa hannu shima ya mika mata gami da yi mata murmushi. Haka itama mannira ta mikawa kowa hannu suka gaisa, amma ta karshensu wato axixa da mr Johnson ya mika mata hannu sai ta tsuke fuska ta kawar da kai gefe tayi tsaki, sannan cikin harshen turanci tace “banxo Croatia ba don in gaisa da mutanen ta, don haka a rabu da ni.” Ta sake jan wani dogon tsaki sannan ta wuce ta nufi cikin mota. Su duka suka bita da kallo tana tafe.

Atika tayi murmushi tace “kuyi hakuri haka halinta yake masifaffiya ce” mr Johnson yayi murmushi yace “babu komai ai kyakkyawa ce don tayi haka babu laifi. Su duka suka sheke da dariya mannira tace “haba ku turawa farar fata ya xa’ayi kuce da bakar fata mai kyau? ” 

mr johnson ya sake tuntsirewa da dariya yace “baku san akwai kyawawan bakar fatan da suka fimu farar fatar kyau ba, ai axixa irin wannan kalar ce da take tsada a nan wato chocolate colour kuma ga kyau ga kudi ai dole ta jawa maxa aji.” Suna ta dariya dai Ashraf ya bude but ya xuba akwatinansu a ciki.

Mr Johnson yace da Ashraf ya je ya tuka daya motar su tafi a ciki shi da mr brown, shi kuma xai tuka su a wannan. Bayan kowa ya shiga, suka ja suka nufi wani kataferen hotel da yake bakin ruwa.

Allahu Akbar, Allah mai yadda Ya so, Ya axurta wanda Ya so Ya tabuka wanda Ya so, yanxu tun suna America suka bugo waya suka shaida musu ga sunan xuwa rana kaxa karfe kaxa suna son kaxa da kaxa. Shine kafin su karaso an tanadar musu komai hatta irin motar da suke so su ringa hawa a kasar itama saida aka tambaye su aka kuma tanadar musu. Daga Croatia ma ba xasu tsaya a nan ba, sati daya xasu yi kafin jirgin ruwa ya xo ya wuce dasu kasashe daban daban ta hanyar jirgin ruwa. Su yi ta xagaya duniya kamar Atlanta, Malaysia , Italy da dai duk sauran kasashe masu manyan tekuna. ‘yan hutu kenan su axixa babu abinda suka xo yi sai hutu kawai har na tsawon wata uku xasu yi, don a America ma satin su biyu sannan suka yo nan.

Nan da kwana uku ma suke sa ran xuwan su Mubarak, Ibrahim da sadik wato samarinsu don su kara jin dadin hutu sosai. Suma wata ‘yar matsala ct a tsayar dasu shi yasa basu taho tare ba. Mubarak shi ne masoyin axixa, soyayya ce mai tsanani kuwa. Ibrahim shi kuma na mannira, sadik kuma na atika saddam. Wai! Wai!! Wai!!! Babban goro sai magogin karfe, yanxu dukkan wadannan samari da ‘yan dukkan ‘ya’yan jigajigan kasar nan tamu ce ko wannensu dan wani multi miloniya ne mai ji da kansa, don haka ma dan talaka ko ‘yar talaka basu kawo kansu ba ma don yin soyayya da daya daga cikinsu. Yasu-yasu ne don haka sai su yi yadda suka so yi da dollar ko pounds.

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Dan Waye Complete by Zahara'u Baba Yakasai

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post