[Book] Kwarata Return Complete by Jamila Musa

Kwarata

Title: Kwarata Return

Author: Jamila Musa

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Romance

Doc Size: 355KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: A baya mun kawo muku littafin kwarata na farko, yanzu ga Return na Kwarata wanda marubuciya Jamila Musa ta rubutashi. Za ku iya sauke cikakken littafin nan yanzu haka.

Book Teaser: Dakel aka fiddoshi daga wurin , dan bashi da hankali akan ɓarar da kuɗi. Idan zai kwana a haka baya gajiya kuma ba zai daina ba , zaiyi ta zubawa ne baya gajiyawa , haka kuma idan zai bayar yake kyauta maisa ɗimuwa.

      Wace ce ita...............???

      Wata irin dariya yakeyi bayan an fito dashi yana tsaye gaban Momy data bishi da kallon takaici , hahahaha yaci gaba da dariya yana kallonta , nima binshi nayi da kallo ina murmushi saboda ba ƙaramin kyau yakeyi ba idan yana dariya....

       Momy tace idan ka gama haukar ka ɗauki matarka ku tafi gida , daina dariyar yayi tare da taɓe fuska , a yatsine yace ai ba tare nazo da ita ba. Murmushi mai cin rai nayi , ba tare dana sake kallon inda yake ba. Kafin inyi magana akaja Momy wai anayin faɗa , binta Rabiya tayi da sauri ni kuma na kalli Dikko ƙasa da sama a yatsine nima nace , tir tittir nabi tsoho ya ɓatamin wanka , nine tsohon ? Ya tambayeni yana nuna kanshi.

       Yadda ya ɓata ranshi yasa nayi shiru ina kallon ƙasa , jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai sannan yace Allah ya maida mu gida lafiya , banyi magana ba kuma banyi gigin sake ɗagowa na kalleshi ba , nine dai tsoho ko ? Ya sake tambayata da yanayin ranshi ya mishi babu daɗi , hmmm tsoho , ƙara jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai , mtswww , ya wuce daga wurin yana magana ƙasa².

       Da sauri na ɗago ina kallonshi dan harya tafi ya sake dawowa , nine dai tsoho ko ? Dan ina tausayinki kenan yasa kika raina ni ? Har nine zaki kalli tsabar idona kicemin tsoho tsabar kin ɗaukeni sallau , duk shekarar nan ni banma samu wanda ya ɗaukeni sakarai ba kamar ki , ajiye kai yayi da ɓacin rai , zaki ci gidanku Allah ya maida mu gidan lafiya zaki faɗamin nine tsohon idan na riƙeki , yana faɗin haka ya wuce , a firgice na juya bayana da sauri , Rabiya ce ta dafoni ta baya , nayi tunanin shine ya sake² dawowa.

     Ana fita da Dikko itama ta sulale ta fice daga cikin holl in da farin cikinta , ta wani ɓace abunta ba tare da anga fitarta ba , jikin motar ta , ta tsaya ta saka hijabi da niƙaf , bayan ta gama ta wani shige tayi layar ɓata abunta , wannan shine ɗabi'arta , hijabi da niƙaf , bata rabuwa dashi ita musulma , idan kuma zata tafi bariki bata fita da motarta dan gyaran tako.....

       Wai ke me zakiyi mata ne kike neman ta ? Barni na ganta sai in ɗauki mataki a gabanku , tou wai yaushe suka saba haka har ya saki jiki yana mata ɓarin kuɗi a gaban bainan nasi....? Waye ma zai iya sani ? Tsoki ƙawarta tayi cewa wai kema Jiddah bazaki bar wannan banzan Dikkon ba ? Sai kace Dikkon diamond ? Murmushi Jiddah tayi tare da kallon Mardiyya cewa faɗa mata waye Yaya D ' K.

Cike da tsantsar soyayyar Dikko Mardiyya ta fara rattafo mata , hmmm ai ya wuce duk inda hankali baya tunani , saima kin ganshi , gashi mai kyau , ɗan gayun bala'e uwa uba ga kuɗi ga mulki , idan yana magana sai ya baki sha'awa , gashi sakatacce wani irin kallo yakeyi mai burgewa , Dikko matashi ne mai wayewar kai , buɗewar ido da gogewar rayuwa amma bashi da mutunci ko kaɗan , damen ɗan iska ne , kuma shiɗin ƙyalƙyal na lariya ne , tantirin kwallon ɗan iska ne yanzu mutum anjima bai sanki ba , yana da baƙon hali , haƙurin zama dashi sai ɗiyar ɗan caca , dan itama "yar tasha ce. Kinsan auren tasha baya ƙarewa saida aci uban juna yanzu , anjima kuma a zama masoya , duk da biyu Mardiyya tayi wannan maganar , sanin manufarta na faɗar haka sai ita da kanta.

       Ƙawar Jiddah tace tou ni me yasa baku kirani na ganshi ba lokacin daya shigo ? Murmushi Jiddah ta sakeyi tare da cewa har hanzu baki makara ba , Mardiyya bata hotonshi ta gani , a duniyance Mardiyya tace waye yaba Mardiyya hatimin nasara ita ba jikar matsafi ba , ai hoton Dikko sai wurin matarshi , gaba ɗaya suka ɗingumo suka yo wurina !

      Sultana Momy tace muje in ajiyeki gida , tou na faɗa tare da kallon agogon wayata 11:22am gaba nayi ba tare dana sake magana ba , ta baya Jiddah ta riƙomin riga , da sauri na juyo dukana dan ganin waye ya rainamin wayau haka ? Cikina ta kalla sannan kuma ta kalleni amma yanayin fuskarta ya nuna taji babu daɗi , amma dake "yar duniya ce , saita wayance da murmushi cewa ina ta magana shiru nace ai nasan bakiji ba , banyi mata magana ba na tsareta da ido , dafe kafaɗa ta tayi kamar ƙawarta tana cewa Aunty Rabiya ai muma a gidan Yayan zamu kwana.

     Rabiya bata kalleta ba tace ai kina da numbershi ki kirashi ki faɗa mishi , ai basai na kirashi ba kuje gidan muma muna zuwa bayanku , Rabiya bata sake magana ba ta wuce , sauke hannun Jiddah nayi daga jikina nima na wuce muka tafi , har muka zo gida Rabiya batayi magana ba nima banyi ba , a waje ta ajiyeni ta wuce. Ni bansan abinda ya haɗasu ita da ɗan uwanta ba , ni na shiga da kaina ciki raina a jagule , a get na biyu na haɗu da Ashiru , yana gani na ya tsaya yana cewa ranki ya daɗe mai gida yace naje na taho dake , ko inda yake ban kalla ba kuma banyi masa magana ba na wuce , shi kuma ɗayan marar kunyar a get na ukku na haɗu dashi shima fita zaiyi , wato bai gaji da iskancin ba zai sake komawa , kenan dawowa yayi gida ya sake sabon wanka , yanzu garin nashi ya waye , ko wane bawan Allah idan dare yayi yana gidanshi yana bacci , koba a gida ba duk inda kake idan dare yayi zaka samu natsuwa , idan bakayi bacci ba , tou kana kusa da ubangiji kana bauta masa a dai² irin wannan lokacin , amma banda Dikko daya maida dare lokacin huɗɗoɗinshi.

      Shima magana yayi min wai daga ina nake ? Kuji fa ? Wai ma daga ina nake ? Kamar ma baisan ina ya baroni ba , shima ko inda yake ban kalla ba na wuce , An mata bakyaji ina miki magana ne ? Ban dawo ba kuma ban tsaya ba na wuce , da ribos ya biyoni saida yazo inda nake yace ke Yarinya bakiji ina magana ne ? Canja hanya nayi naci gaba da tafiya , An mata dake nake fa ? Ganin Sultana tabi hanyar da zata shigar da ita ciki batayi mishi magana ba , yasa yayi parking ya fice da sauri yabi bayanta.

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Kwarata Complete by Jamila Musa


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post