[Book] Mafarin Lamari Complete by Zeetty

Mafarin Lamari

Title: Mafarin Lamari

Author: Zeetty

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 98KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2017

Description: Ina ma'abota karatun litattafai? Ku sauke "Mafarin Lamari" complete hausa novel wanda marubuciya Zeetty ra rubutashi tun wajajen shekarar 2017. Labarin akwai dadi. 

Book Teaser: Shigowa gida yayi ko sallama babu, yafara ball da wani baho daya gani a gefen tsakar gidan, cikin bala'i yafara magana"aikin banza aikin wofi, ni za'a kawoma iskanci a cikin gidan nan?, toh zan yimiki wulak'anci, Aysher ina kike, yooo gani d'an iska ko? Ina magana kina ciki kin maidani shashasha, kai uban giji kayi mana arziki ina ganin wulak'anci a gurin matar nan, bazaki fito ba saina shigo har d'akin na nakad'a miki duka, a gaban 'ya'yan naki kaza uwar son 'ya'ya.?"

Da sauri har tana cin tuntu6e ta fito, tana cewa"kayi hak'uri Abban Aslam, wallahi Afra ce take so tayi bacci, shine nake lalla6ata dan nasamu tayi bacci na k'arasa aiki na."

Doguwar tsaki ya saki, kafin yafara magana cikin kumfar baki"Kinji tsiyar ba, daga anyi miki magana sai kice 'ya'ya sai bala'in son 'ya'ya, wuce kibani guri nidai Allah kawomin ranar da zan rabu da wannan bala'in, saboda banda kud'i kin mayar dani d'an iska, shashasha ko?"

"Kayi hak'uri Abban Aslam ba haka bane, ka gafarceni idan na 6ata maka rai." Ta k'arasa fad'a tare da juyawa dan komawa d'akin ta.

Fusgota yayi kafin ya wanketa da mari, yafara magana cikin hargagi"Ehhh mana wato gani d'an iska ina magana kin tafi kin barni wato nagayawa iska ko.?"

Hanunta dafe da kuncin ta tafara magana tana hawaye tace"Kayi Hakuri Abban Aslam, kace natafi, na juya domin tafiyar, amman yanzu kace nayi maka badai-dai ba, kadaure ka sanar dani laifin dana aikata gareka kake hukunta ni, ta wannan hanyar dan Allah, auren so mukayi ni dakai, bawanda akayima dole amman kwata-kwata baifi zaman shekara d'aya mukayi cikin kwanciyar hankali ba.?"

"Hmmm tuhumata kikeyi,? Nace tuhumata kikeyi, tunda na aureki wane cigaba nasamu sam babu wani cigaba kullum sai komawa baya nakeyi, duk abokaina sun fini kud'i da arziki, nikam tabbas na auro mai farar k'afa, zama nin nan ina ake auren so? Sai dai auren kud'i, to bari kiji dakyau, ina nan nasa ayimin binciken matar aure, auren jari zanyi, 'yar alasawa, muga tsiya, shashasha kawai."

Yana gama fad'in haka yasa kai yafice dan barin gidan.

Komawa tayi da baya ta shige d'aki, zama tayi ta rafka tagumi, shin me natsarema Abban Aslam lokaci guda ya canja min?, talaucin nan bani na d'ora mana ba, lallai nice ma mai farar k'afar?, ikon Allah.

Bayan ta gama komai ta gyara gidan tsaff ta d'auko turaren tsinke mai rangwamen kud'i ta kunna, kud'in da Yayanta Nasiru ya bata shekaran jiya da taje gida dashi ta sake amfani yau dan yimusu cefane, Macaroni ta dafa da dankalin turawa, ta siyo d'ayen kifinta ta soya ta watsa a ciki.

Bayan ta gama komai ta share gidan, ga goge ko ina tsaf, tashiga wanka ta fito ta kimtsa, cikin kwalliyarta mai sauk'i, hak'ik'a AYSHER tanada kyau, koda ace batayi kwalliya ba, dubeta yanzu kamar bata ta6a haihuwar yara har guda biyu ba.

Tana zaune a falo ya shigo yana cika yana batsewa, salama yayi ciki-ciki, Aysher ta amsa tare da fad'in"Sannu da dawowa Abban Aslam."

"Yauwa sannu" ya fad'a a dake.

Tace"Me zaka farayi wanka ko cin abinci.?"

"Bazanyi wankan ba, nace bazanyi wankan ba ko dole ne, zoki mak'ureni nayi dole uwata."

"Yi hakuri barin kawo maka abinci."

(Tak'arasa fad'a tare da mik'ewa dan zuwa kawo mashi abinci)

Try ta d'auko mai d'auke da food flask da plate da cokali, ta k'araso gaban sa ta ajiye tare da bud'ewa ta zuba masa, ruwa ta d'auko a roba ta ajiye masa a gaban sa, duk yana binta da kallo saida ta gama tace"Bismillah"

Yace"Kina wani yimin abu isa-isa idan tak'amarki yau ban baki kud'in cefane ba kiyimin list, in sha Allahu zan biyaki idan nayi kud'i."

"Kayi hak'uri duk maganar baikai haka ba."

"'Daukar abincin yayi yafara ci kamar dole, daga k'arshe dai zagewa yayi, yaci yayi kat, kafin ya mik'e a 3 seater, yana satan kallon matar sa, tayi masa kyau take wani sha'awata ya lullu6eshi."

"Zan shiga ciki Abban Aslam saida safe, saika shigo."

Yace"Aikin kenan, toh banyadda ba kijira nagama kallo, har lokacin tashina yayi mushiga tare, inada buk'ata, kinsan ai dole zan buk'ace ki wannan kwalliya haka dan tsabar jarabarki ta motsa shiyasa kika yimin ita, kijira zan biyaki hakkinki, kar Allah yakamani kodan saboda haka narasa ganin dai-dai, barin gama mushige dan nasan ko kinshiga ciki ba bacci zaki iya ba, mayya kawai."

Maganar tasa tayima Aysher ciwo, amman ba yadda zatayi, komawa tayi ta zauna tana kissima abubuwa dayawa a ranta, wato yanada buk'atar ta amman shine zai juya maganar kanta, Allah kayimin agaji........

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Zubar Hawaye Complete by Zeetty

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post