[Book] Ni Zan Ladabih Complete by Sajida Niger

Ni Zan Ladabih

Title: Ni Zan Ladabih

Author: Sajida Niger

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 701KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Dauki tare da sauke cikakken littafin marubuciya Sajida Niger mai suna "Ni Zan Ladabih" complete hausa novel document a text format. Ku kawai ya ke jira, ku saukeshi.

Book Teaser: A sanyaye ta sake juyowa barin da suke tsaye

Dan murmushi ta saukewa Hasan din ko zai sasauta irin hade fuskar da ya yi kafin ta sake mika hannu ta kuma tsayar da dan adaidaita sahu. 

Yana tsayawa ta ce" Bawan Allah anguwar mai shanu zaka kaini da yarana dari da sittin ce da ni"

Kallonta ya yi sannan ya leko ya kalli yaren ya ce" Aman baiwar Allah kin san da kin so kanki ko? Yaya zaki ce a kaiki har anguwar mai shanu a dari da sittin da kuma yara?"

Dan ajiyar zuciya ta sauke tana dan matsawa gefe dan ta gama gane shi dinma ba zai daukesu a haka ba, tun daga babar makarantarsu take janye da yaren dan su dan rarage tafiyar ko zasu samu a kaisu a haka din domin wannan cenjin shine kadai abinda ya rage mata a yar jakar sakarta da ta yi, sauran kudin kwata kwata ba na anfanin hakan bane, kudin makarantar ne take faman tarawa

Bata ja maganar ba ta ce da dan sahun" Allah ya kawo kasuwa"

Daga haka ta sake juyawa wajen biyun a hankali ta ce" Hassan dina idon ne?"

Hassan ya sake murtuke fuskarsa sosai bai ce mata ci kanki ba, sai Usaini ne ya yi dariya da maganarsa mai ruwa ruwa ya ce" Mama mu karra yin tafiyar kadan zan ci gaba da jan hannunsa har mu samu masu kaimu a haka, na tabata ba za'a rasa na annabi ba"

Murmushi ta yi tana kallon bayan dan sahun nan da sai da ya sake lekowa yana sake kallon fuskar Hassan din sannan ya ja adaidaitarsa ya yi gaba ya barsu a nan zafin ranar na sake tandar fatar jikinsu. 

Hannayensu ta kama tana tsakiyarsu tana jansu a hankali suna tafiya cikin salonta na sanyin jiki da magana tana dan tambayarsu idan suna jin yunwa ne da sauransu har suka yi tafiya mai nisan gaske sannan ta sake gwada sa'arta ta kuma tsahar da wani dan sahun, sai dai a nanma saboda talatin kadai da ta rage a kudin ya nuna ba zai iya daukarsu ba sai dai idan yaren zasu zauna a gaba ne, ita kuma abinda bata yarda da shi ba kennan watau ajiye biyu a gaban adaidaita, domin yaren nata ba dai kiriniya ba idan sunna cikin dadin rai zasu iya fadowa ta shiga uku, dan haka ta gwamace sake yin wata tafiyar. 

Usaini ne ya fara takwakwafa fuskarsa, domin shi din dama ba dai ragwonci ba, kadan ya sha wahala zata nuna a jikinsa, ya ga damar ya fara sheka kuka har inda zasu je ya ja ya tirje yana kallonta da fuskar kuka a shinfide wace ke nuni da tabas yana daf da fashewa da kukan. 

A sanyaye ta ce" USEIN din Mama, menene?"

Useini ya juya gabas da yama, kudu da arewa ya ce" Mama ni gaskiya na gaji, ki duba baban titin nan kowa a cikin sahu yake dan ranar nan da ake kwalawa, daidaiku ne muke ganni sunna tafiya a kafarsu, suma babu yara a ciki, ni gaskiya ki goyani "

Ido ta dan zarro jin ya ce ta goya shi, bayan tafiyar da sauransu sosai da sosai, bayan wannan ma yanzun idan ta goya shi Hassan zai murje ido ya kirta aikin da ba shikenan ba, dan haka sai ta age tsayinta sosai ta duka tana kallonsa ta ce" Ka ga dan albarkana ita tafiya fa tana da dadi, jikin mutun kan samun karin lafiya, ka san kuwa mai yin tafiya sosai a kafarsa baya yawan yin rashin lafiya bale a bashi magani? Zo maza dan albarka salihi dan Mamansa mu tafiyarmu mu karra kadan sai mu shiga dan sahu "

Ido ya fara murzawa zai fashe da kuka, sai a lokacin Hassan ya bude baki ya ce" Ka san Allah idan ka mayar da katon kan nan naka baya ka fashe mana da kukan rainin wayo zan cire abin kan nan nawa na tatakaka a bakin titin nan, ka san da zan iya , kai ko kunya baka ji katon banza kai"

Useini ya zaro ido ya juya wajen Maman tasu yana nuna kansa da nashi salon na rigimar sai dai ga dukkan alamu yana shayin dan uwan nasa domin uwar ya kafe da ido yama so ta yi magana a kan lamarin za'a tataka shi kafin ya samu kwarin gwuiwar yi shima. 

Zata yi magana wani dan sahun ya ja ya tsaya yana fadin" Hajia tafiya ne?"

Shima bata boye masa gaskiyar abinda yake hannunta ba ta fada mas akuma wajen da zai kaisu, sai aka taki sa'a ta fada kan wanda nema ya fito da zuciya daya da kuma godiya ga Allah kan abinda zai samu da zarar zai samu fita to fa zai kwatanta adalci wa masu shiha adaidaitarsa ya basu damar shiga, wannan ya rufe babin fadan da suka ja dunda zasu dora a bakin titi wanda ta tabata da ace sun fara shin to fa lalle da sai ta kusan yi masu kuka koda zasu dajata, domin yaren akoy rigima sosai a tsakaninsu sannan akoy fahimtar junna a tsakaninsu da ita. 

Daidai gidan Baba Lauratu aka ajiye su, ta kuma kama hannayensu bayan ta biya dan sahun suka shige cikin gidan tana salama a bakinta tana kuma jin yadda Hassan kasa kasa yake dan jan tsakin biyowar da suka yi kafin su karasa gidansu. 

Har kasa ta duka tana gaishe da babar dake amsata da fara'a sosai a kwonce saman fuskarta kafin ta maida dubanta kan Hassan tana fadin" Ganninku alkhairi ne koda a saman dokinku kuke, ga maza ga biyu kyautar Allah, shin waye ya taba Alhassan bawan Allah ya kuma kumburan fuskar miji nake ganninta a hade haka?"

Useini ya dan fara cika fuska shi ala dole shine mijin baba Lauratu , Hasan kuwa ya sake tamke fuskarsa yana sake cira kansa gefe

Baba Lauratu ta ce" Kin ga *AMINA* ga cen kwanon da na dama fura harda siga dauko masu su shanye na tabata harda zafin rana ta hadasa rikicin  biyu ba abin wasa ba"

Ai kam har sai da ta sauke ajiyar zuciyar farin ciki kafin ta karasa ta dauko ta ajiye masu a cen gefe ta ja kowane tamkar makafi ta zaunar da su daya bayan daya sannan a sanyaye ta ce" Dama zasu min abin kirki su sha kama kama ba tare da sun yi fada ba?, Kai da na ji dadina sosai"

Tana gama fada ta koma saman tabarmar Baba Lauratun ta shiga tayata kula lalenta na hausa da take kukulawa na siyarwa

Kasa kasa sosai Baba Lauratun ta ce" Yaya mai baban sunna an dace kuwa?"

Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye jakar tata ta saka tana ciro takardun ciki , ta bude baban litafin cikin ta ciro naira dubu hudu da dari bakwai ta mikawa Baba Lauratun ta ce" An gode Allah, aman cewa suka yi haka gwamnati ta rubuta kudin zana jarabawar, ba zasu iya rage min ba , ni kam yanzun na danganama Baba, Allah ya fido min da wata hanyar, kudin nan ki kuma ajiye min su zan je na ci gaba da buga bugar mu ga yadda Allah zai yi, idan da rabo badi zan zanna in sha Allah"

Baba Lauratu ta sauke ajiyar zuciya, ita kam da yarinyar zata bi ta tata da ba haka take so da ita ba

A sanyaye ta ce" AMINATU, Aure fa?"

Da sauri ta kalleta, sai kuma ta samu kanta da maimaita kalmar

Baba Lauratu ta ce " Eh aure nace"

Amina ta yi murmushi ta juya tana kallon yaren dake shan furar, da farko sun fara fada sai kuma Hasan ya zubawa Husain din ido har ya fara koshi sai ya bara masa, domin shine dama bawan ciki ta sake juyowa wajen Baba Lauratu a hankali ta ce" Biyu fa?"

Baba Lauratu ta girgiza kanta cike da rashin jin dadin lamarin ta ce" Kin ga Amina, rayuwa ba ke take jira ba, zan sake fada maki gaskiya kamar yadda na saba, kin ga iyayenki sun rasu, ke da y'ar uwarki suka bari, kunna da dangi ba baku da su ba, irin yadda suka yi watsi da lamarinku tabas abin a duba ne, aman kuma lamarin rayuwarkima abin a duba ce, kin san da tsoratar da maza kike?"

Da mamaki take kallonta da son karrin bayani a kan wai tsoratar da maza take

Baba Lauratu ta ce " yawancin wa'inda basu sanki ba idan sun ganki kina yawo da biyu zasu dauka naki ne koda kuwa yannayin jikinki bai nuna kin haife su ba, aman Amina ba kowa ne ya san cewa biyu y'ayan Firdausi ne, wainda suka sanki kuwa idan sunna da ra'ayin zuwa su aureki zasu iya tsorata da yannayin rayuwa ciyar da y'ayan mutun biyu ba kowa zai iya dauka ba, ki yi hakuri iya gaskiyar nake fada maki Amina kin zo kin sakkawa ranki wahala, wahala ce mana, Allah na tuba a kasar nan idan kai ba kowa bane ba dan kowa bane ko ka samu ka gama karatun sai dai ka san yadda zaka yi da shi aman ba dai ka anfana da shi ta hanyar da ta dace ba, gashinnan shekaru na ja Amina shekarunki nawa yanzu? Sai zuwa nawa zaki iya gane me nake nuna maki ki dauki matakin da ya dace ne?"

Amina da idannuwanta ke lumshe tana sauraron dukkan bayanan Baba Lauratu zuciyarta na dan dokawa, ba dan komai ba sai dan ta san iya gaskiya ne Babar ke fada mata, aman kuma itama da nata maganar, tana da nata bayanin a kan maganar dan haka ta fuskanceta a nutse ta ce" Wani lokacin, du yadda bawa ya kai da son cenza yannayin kadarar rayuwarsa babu abinda ya isa ya aikata sai dai ya ci gaba da adu'a Baba, walau ala ni ban zo duniya dan na yi aure ba, ta yiwu kuma zan samu auren a hankali.......Abinda na fi rikewa da karfina   Baba shine y'ayan nan y'ayana ne, yayan yar uwata ne, diyan zumuna ne,  yanzu da nake cikin haka ina cikin niimar ubangiji, mijinta ya nuna nasa yayanma kama cen riko cen ne yake yi ina zan kaisu? Nawama suke yaren? Ba zan taba sakin hannayen biyu ba Baba, kin ga fa dangin mahaifinsu basa so, ina zan kaisu?......"

Ta sauke ajiyar Zuciya ta dora da fadin" Ni bani da inda zan kaisu Baba, shi yasa na koyawa kaina zama mamansu da soyaya a zuciyata, na koyawa kaina kula da su da basu tarbiya, na tabata wata rana zan samu wani datijon arziki ya daukeni da yarana koda a gidan gadonmu ne mu zauna.......Abu biyu da na san ba zan bari ba shine ci gaba da neman ilimi ta hanyar da ta dace, da kuma ci gaba da kula da biyuna" ta karashe a sanyaye haka kuma jikinta na karra daukan sanyi ainun, bama kamar idan ta tunna irin abubuwan da take fuskanta a wajen wasu mazan dan kawai ya kasance itace mace tal a gidan da suke zaune sai yan yaren na y'ar uwarta, aman ta san ko menene adu'a na gaba da shi, kuma ta san Allah ne gatanta

Baba Lauratun itama ta sauke wata ajiyar zuciyar ta ce" Allah ya dafa maki y'ar nan, Allah ya taya ki riko yarinyar nan.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post