[Book] Radadi Complete by Sa'adatu Waziri Gombe

Radadi

GABATARWA

Bismillahi rahamanir rahim, ina gabatar muku da wannan littaf da sunan Allah, ina fatan zai zama mai amfani ga al’ummarmu, alkairin da ke ciki Allah Ya hada mu a ladan, kuskuren da ke cikinsa Allah Ya gafarta mini.

Zaune ta ke kan gadon asibiti yayin da ta jingina bayanta jikin gadon, kafafunta a mike ta zura musu ido tana ganin irin kumburin da su ka yi. Kana kallon fuskarta za ka san tana cikin matsanancin damuwa da quncin rayuwa. Sanye ta ke da dogon riga mai kama da (maternity dress) ta yane kanta da jan mayafi, idanunta sun kada sun yi jawur sai dai duk q

Kokarin da ta yi ta samu ko digon hawaye ya zubo amma hakan ya gagare ta, sai azabar zafin zuciya da kuma wani irin radadi da ciwo da ta ke ji yana mata.

A wannan halin ta juyo kanta da qyar ta maida kallonta kan jinjirin da ta haifa kwana uku da suka wuce yana kwance cikin gadon jarirai da ke gefenta yana callara kuka irin na jarirai. Ba ta da abin da za ta iya illa iyaka ta zura masa ido, tana kallonsa saboda ko motsa jikinta ba za ta iya ba balle har ta mike ta iya daga shi. Nan da nan ta ji wani irin kewa ya lullube ta, ba za ta iya yi wa kanta komai ba balle jaririn da ta haifa.

Runtse ido ta yi tana jin kukansa na ratsa kunnuwanta. Lokaci guda kuma ta ji kukan ya rikide a kunnuwanta ya koma kalamansa masu daci da zafin saurare.

“Da ma ashe ke ballagaza ce, shashasha, mara hankali, wadda ba za ta iya kula da gidanta ba balle mijinta har a kai ga abin da ki ka haifa? Mahaukaciyar banza kawai, sakarai!...”

Tuni ta ji wasu hawaye masu radadi sun zubo mata suna tsere a kan fuskarta.

Wannan kadan ne daga cikin kalamansa masu daci da zafin gaske. Tuni ta ji ta tsinci kanta cikin rashin gata, cikin kewa ta dinga jin rayuwarta ya shiga cikin garari da tambele da rashin gata wanda sai ta yi da gaske za ta iya tallafar kanta. Ta riga da ta sadaukar tare da yanke tsammani da wani jin dadi, ko wata rayuwa ta farin ciki da nutsuwa. Tabbas ta san addu’a ne da taimakon Allah ya sa har yanzu ta ke da sauran hankali da karfin zuciya, da tuni zuciyarta ta buga, an mance da ita da labarinta. Da tuni ta yi mutuwar kunci da da-na-sani. Akwai abin da Allah ke kaddara maka kuma ya jarabce ka, akwai kuma abin da kai ka ke jawo wa kanka. A yau ta tsinci kanta a halin rayuwar da ba ta taba gani ko tsammanin za ta taba fuskantar rayuwarta ba.

Muryar likitan ya katse mata tunanin da ta ke, saboda yadda ta ji yana kwada wa Nurse kira da karfin gaske, hakan ya sa ta maida hankalinta da kallonta gare shi, ta lura ransa bace yake ainun. Wata nurse ce ta turo qofar ta shigo da sauri, ya kalle ta ransa bace ya ce, “Ina Hafsah?”

Ta amsa da cewa, “An mata waya daga gida cewa danta ba lafiya, kuma jikin nasa ya yi tsanani”.

“Shi ne kuma dukkanku ba wanda zai iya zuwa ya yi replacing dinta kafin ta dawo?”

Ya sa hannu ya dauki jinjirin yana jijjiga shi, saboda irin karar da yake cillawa jin an daga shi ya sa ya sassauta kukan.

Ya kalli Nurse din ya ce, “Kun san condition na wannan patient din tana bukatar nurse a kusa da ita a ko da yaushe, a ko wani lokaci ba a barinta ita daya, ita da jaririnta suna buqatar kulawarku a ko wani lokaci’.

“Sorry sir”. Ta fada murya qasa-qasa.

“Forget it”. Ya fada ransa bace, tare da fadin, “Private nurse zan xauko mata, wacce ba ta da hadi da asibitin nan, aikinta kawai na kula da patient dina da jaririnta kafin nan bana jin ina buqatar fada miki me za ki yi”.

Duk wannan fadan da yake musu tana jinsu, amma idonta rufe tana kukan zuci tare da addu’a a cikin zuciyarta don samun sassauci. Me ya fi wannan rayuwar kaskanci da kunci da rashin gata? Akwai Allah! Ta fada a zuciyarta.

“Ba na yanke kauna daga rahamar Ubangiji, Yana ganina, Yana sane da ni. Allah mai yafiya ne, Mai rahma, Mai yawan jin kai. Astagfirullah”.

Ta ci gaba da maimaitawa a zuciyarta, take ta ji hawaye suna tsere a fuskarta wanda hakan ya sa ta samu sassauci da sanyi a zuciyarta.

Ta yi nisa sosai tana istigfari, tana jin sanyi da nitsuwa a zuciyarta da jikinta baki daya, har bacci mai dadin gaske ya soma dibanta. Tuni ta manta da komai ta yi kokarin ba wa baccin nata muhimmanci. Can cikin bacci ta ji maganganunsu na bin kunnuwanta, yana ratsa zuciyarta wanda hakan ya kwashe baccin idanunta, da duk wani nutsuwa da sukuni da ta samu.

Dariya suka yi tare da tafawa da shewa gami da fadin su yadda manya, amma fa wannan akwai sakaryar mace, ba ta san da namiji ba, ai namiji ba dai munafurci ba, ina jin a halittar da namiji akwai gane-gane da leqe-leqen mata, son mata a halittarsu yake ko da kuwa muninta ya kai duwawu in dai zai hango ta a layi kyau za ta masa ya bi ta ko da kuwa kyawun matarsa na diga ne”.

Dariya suka yi tare da sake shewa suka fita, har suka gama gyarata ba ta ma san suna taba ta ba, duk kuwa da kullum in an taba jikinta sai ta ji wani irin azababben ciwo, amma sam yau ba ta ji hakan ba saboda azabar zafin zuciya da radadi da ta ji maganganunsu na mata, sun taso mata da sabon bacin rai ta ji komai ya dawo mata sabo da qunci da bacin ran, wayyo rayuwa.

Likita ya isa gida a gajiye, zuciyarsa cike da damuwar rashin lafiyar Halima na damunsa, ya rasa ta ina zai bullo mata yana son taimaka mata har cikin ransa, saboda ya fahimci halin da take ciki tana buqatar taimako, nan ya dauko loptop dinsa ya kunna, ya sake duba [case] xinta yana karantawa. Hotonta ne ya bayyana, wanda ya dauke ta lokacin da yayi mata c.s tana kwance a dakin tiyata, ya yi shiru ya qurawa hoton ido yana nazarin ciwon nata, yadda ya qurawa laptop din ido, ita ma haka ta tsaya a bayansa, tana kallonsa, tana kuma kallon me ya ke yi, tsawon mintuna suka dauka a hakan, sannan ta juya ta nufi kicin, kasancewar lokacin sanyi ne ya sa ta hado masa coffe mai zafi ta hada a kan tray ta nufo inda yake ta ajiye a kan table din da ke gabansa ta gefe, sannan ta sa hannu ta dafa shi .

Ya juyo suka kalli juna, ta yi masa murmushi, shi ma ya yi mata tare da jawo ta jikinsa ya rungume ta. Ya lumshe ido, ya ce, “Ni kadai na san irin nutsuwar da nake ji idan ina kwance jikinki ina samun dukkan wani energy na daga gare ki, daga yanayinki. Allah ya miki albarka”.

Ta amsa da, “Amin”. Tana murmushi sannan ta ja daya daga cikin kujerun da ke wurin ta zauna suna fuskantar juna. ta jawo hannunsa ta hada da nata ta tattara hankalinta gabadaya a kansa tana kallonsa. Ta kira sunansa cikin nutsuwa, “Abba”. Ta bi bakin yara yadda suke fadi.

Ya dago kai ya kalle ta shi ma hankalinsa ya tattaro gabadaya ya bata yana sauraronta.

Ta ce, “Na san ka gaji yau, ka jima a asibiti, kuma na san yau ka ga marasa lafiya wanda jikin nasu ya yi tsanani da masu manyan ciwo. Allah ya taimake ka, Ya kuma biya ka da gidan aljanna”.

“Ameen”. Ya fada yana murmushi. Ya ce, “Kalamanki sun tafiyar min da gajiyar gaba daya, na gode Ummu Ayman da goyon bayanki, ya sa nake samun nutsuwar aikina, Allah ya ba mu aljanna da ni da ke gabadaya”.

Ta yi murmushi, “Amin Abba, da ma magana nake so mu yi ko in ce wata shawara nake so in ba ka”.

“Ina jinki”.

Ta dan sake gyara zama ta kalle shi ta ce, “Abba mai zai hana ka aure ta?”

Ba-zata ya ji maganar, ya qara ware idanuwa yana kallonta, sunanta ya kira kai tsaye, “Fadimatu, kin san me ki ke fadi kuwa?”

Ta girgiza kai, ta ce, “Qwarai likita, na san me nake fadi, ina fatan za ka fahimce ni da dalilaina kamar yadda na sani kullum kana fahimtata, ka saurare ni in kana ga ba ka gamsu da abin da nake fadi ba, kana iya yin yadda ka ke so, ni ma ba zan maka rashin fahimta ba”.

Ya sake mata duba tsaf! Ya ce, “Ko me ye dalilinki? Bayan kin san wannan ba ra’ayina ba ne?”

Ta yi murmushi, “Na sani a iya sanina da fahimtata ra’ayi bai fi yin abin da yake daidai ba, bai fi humanity ba, bai fi taimako ba. Babban kuma shi ne, bai fi aikin lada ba. Ina mana wannan kwadayin ladan ni da kai kamar yadda muka gina rayuwarmu ni da kai a kan taimakon al’umma iya qarfinmu, muna taimako wani lokaci da iliminmu, wani lokaci da lafiyarmu, wani lokaci da dukiyarmu, wanda duka Allah ne Ya ba mu shi ba wayonmu ko dabararmu ba. In mun yarda dukkan wannan abubuwan Allah ne ya ba mu iko da damar yi tunda wasu Allah zai basu dukkan wannan abubuwan, amma Allah bai ba su ikon yi ba, ka ga kuwa Allah na sonmu Ya sa muka samu wannan damar, to me zai hana mu yi wannan taimakon  da Allah ya ba mu dama, ka yadda da ni, Allah ya sa min jin hakan da amincewa da hakan a zuciyata. Bana jin qunci ko baqin ciki yayin yanke wannan hukunci, eh ina jin kishi. Amma kuma ina jin wani satisfaction a zuciyata wanda wannan nutsuwan ya kore min zafin kishi. Ka fada min in ba Allah ba wa zai sa min wannan abin a zuciyata ka tuna yadda nake qaunarka da kuma yadda nake da zafin kishi, amma da yake Allah na miqa wa lamarina ban yi amfani da wayo ko dabarata Allah ya ba ni mafita qwarai likita na damu ganin yadda ka damu da rayuwar ‘ya mace. Hankalina ya tashi duk da na sanka na yadda da kai, aikinka ka ke kai mutum ne da in ka sa abu a gaba, to sai ka ga bayansa da ikon Allah.

Ka rasa sukuni, ka rasa nitsuwa, ni ma na rasa sukuni na rasa nitsuwa wanda na san ba mu gina gidanmu da rayuwarmu a haka ba, yaramu da ke kallon mu  ba su tashi sun saba ganinmu a cikin halin na rashin nitsuwa ko rashin fahimta ba. Abba bana son bata ginin da muka jima muna yi, don haka na fara gyaran daga kaina na nemi taimakon Allah hakan ya sa min nutsuwa da kuma qaunar hakan a raina, nutsuwarka da kwanciyar hankalinka shi ne babba a wurina. Ina son kare dukkan wani zargi da rashin fahimta, ko batanci tare da dinke dukkan wani qofa na rashin yadda ko zargi da rashin gaskiya da zai shigo cikin gidana, gidana nake gyarawa. Ina fata za ka ba ni hadin kai in har ka yarda da tunanina da hangena, in har ka yadda hakan ba wani son zuciyata ko wani dalili na daban da ya wuce samun nutsuwarmu da kwanciyar hankalinmu duka.

Shi dai Abban kallonta kawai yake kamar talabijin, gabadaya ta zame masa wata sabuwar halitta godiya yake yi wa Allah da ya yi masa zabin mace ta gari, don kuwa ya yadda ba wayo da dabararsa ya mallaka masa ita ba. Allah ne ya yi masa zabi duk kuwa da cewa bai amince da shawararta ba, ta burge shi yadda ta nuna damuwarsa da samun maslaharsa shi ne kan gaba fiye da nata, ta amince mini da auren macen da ba mu sani ba, ba mu san asalinta ba, ba mu san halinta ba, yadda Fadimatu ta ke ya sa ba ya qauna ko sha’awar qara aure saboda yana iya auro wacce za ta zo ta wargaza musu gida ta tada musu hankali, musamman ‘yammatan yanzu ‘yan qyale-qyale, ‘yan ta-more miji ba sa son wahala sai jin dadi sai son abin duniya ko wacce da burinta da wani tunani na daban suke shigowa gidan aure wanda hakan ya kaucewa manufar aure gabadaya… aikina na matuqar buqatar nitsuwa don haka wannan shawaran ba karbabbiya ba ce a wurina”.

Miqewa ya yi tsam! Ya jawo ta suka nufi cikin tsakiyar falon, ya ajiye ta bisa kujera, sannan shi ma ya zauna tare da kwanciya bisa cinyarta tare da hada hannunsa da nata, ya ce, “Fadimatu, na gode da fahimtata da ki ka yi, haqiqa canjin fuska da na gani daga gare ki na kwana biyun nan ya matuqar tada hankalina, sai dai kamar yadda ki ka fadi, akwai fahimta na tsawon shekaru a tsakaninmu, don haka ban zarge ki ko na ga laifinki ba, saboda sanin kishi da kuma rauni irin na ‘ya mace Fadimatu na mace ce, kuma jaruma da ta iya sarrafa gidanta da mijinta don kin yi rauni na wani lokaci ba zai sa in ga laifinki ko in ji haushinki ba, in na yi haka zan kasance cikin munafukai marasa gaskiya, marasa jin kai da tausayin iyalinsu, in na ga laifinki na so kaina Fadimatu, ko wacce mace dole zuciyarta ya sosu a duk sanda ta ga hankalin mijinta ya karkata ga wata mace, Fadimatu ina so ki sani ba ni da kamarki, ba alqawari ko wani abu tsakanina da ke da ya nuna cewa ba zan miki kishiya ba, sai dai kin san a kan yadda muke tafiyar da rayuwarmu hankalina da tunanina bai taba karkata ga wannan ba, saboda wannan wani abu ne da Allah ke qaddarawa mutum yake hukunta masa yawan matansa, yaransa da shekarunsa. Mu ba mu isa mu yanke hukunci za mu yi ko ba za mu yi ba, wannan a hannun Allah yake. Ina so ki sani Halima mara lafiya ce kamar kowa da nake gani, nake ba su kulawa. Yawan kulawa da yawan karkata ga mara lafiya na da hadi da qarfin ciwon mara lafiya, sanin kanki ne Fadimatu ban taba samun case irin wannan ba, eh na sha treating masu deppression, amma da yaddarsu da amincewarsu.

Wannan karon ba haka yake a kan Halima ba, ga deppression ga hawan jini, ga ciwon zuciya ga gangar jikinta yana daf da daina aiki, in ba ta ba ni hadin kai mun soma treatment ba. Hadin kanta shi ne ta yi magana, ta yi sharing feeling dinta, pains dinta disappointment dinta da duk wani bacin ranta, ta rage nauyin damuwar da ta sa wa zuciyarta, kin ga ko kafin haka ya samu sai na bi ta a hankali, na zama friend dinta na ba ta kulawa, sai na yi winning trust dinta har ta ji za ta iya fada min wani abu, kin san qwaya sai dai ya taimaka mata, amma ba shi ne asalin maganin cutarta ba, ki sani ko da namiji ne ko yarinya, ko tsohuwa ko babbar mace ne a matsayin Halima, to yadda na mata haka zan yi wa ko waye a position dinta. Burina taimako da samun lafiyar mara lafiyar da na kwantar, wanda suka zama responsibility na”.

“Na fahimta likita”. Ta fada tana kallonsa cike da gamsuwar abin da yake fadi, “Kamar yadda ka ce na yi rauni haka yake, kuma wannan rauni yana tare da ni har yanzu, don haka na zo mana da maslaha Fadimatu. Wannan ba maslaha ba ne, ki tuna kina yaqi ne da duk wani tashin hankali da zargi da rashin fahimta da zai shigo gidanmu, ya rushe ginin da muka yi. Idan hukuncin da ki ka yanke ya zama sila, sanadin rushewar gidanmu fa, aure ba wasa ba ne, kuma kina maganar auren macen da ba mu santa ba, ba mu san halinta ba. Kin san dai ba a aure haka nan ko?”

Ta yi murmushi, ta san ba ya son nuna mata kai tsaye ya qi amincewa da shawararta ne don haka ya bullo ta nan. Ita kuwa tana son nutsuwarta da kwanciyar hankalinta fiye da komai, muddin likita zai dinga kaiwa kawo a kan Halima tare da tattara hankalinsa ya maida kanta, to zargi da rashin kwanciyar hankali ba zai taba barin zuciyarta ba, don haka gara ta yi maganin abin, don kuwa ba za ta iya rayuwa a hakan ba.

“Kina jina Fadimatu…” Ya katse mata tunani.

Ta ce, “Na fahimce ka sai dai ka manta na fada maka taimakon Allah na nema, istikhara na yi, sannan ka sani zuciyata mai kyau ce, haka intention dina ka ga kuwa da ikon Allah ba mai iya cutar da mu. Allah zai kare min kyakyawan manufata, Ya tsare min kwanciyar hankali da nitsuwar da ke cikin gidana, ina da wannan yaqinin a zuciyata, akwai Allah”.

Ya ja doguwar ajiyar zuciya, ya ce, “Bana iya ja da ke, sai dai ki sani na ban san ta ya ya ya zan fara rayuwa da wata mace cikin gidan nan bayan ke ba, wannan wani sabon karatu ne a wurina”.

Ta yi murmushi, “Wannan ka barshi a hannuna, don kuwa wani sabon tsari za mu fitar da ni da ita”.

Kallonta yake yana mamakinta, har yanzu bai gama sanin matarsa ba, ya ce, “Na ji, sai dai abin da ki ka manta. Halima uwa ce, mai jinjiri tana da aure ko ba ta da shi, ba ki sani ba, kin yanke hukunci. Na biyu in ba ta da aure amincewarta tana son fuskar wannan mijin naki, bayan haka da ciwon za ta ji ko da aure? Shin wai waye ce wannan Haliman da matata ta ke son qaqaba min in aura?”

“Hmmm”. Ta faxa tana murmushi, ta ce, “Ina da amsoshin dukkan tambayarka in dai ka  amince shi ne mai wahala. Na farko in na ce maka Halima ba ta da aure fa? Na biyu in na ce maka nasan wace ce Halima, na uku in na ce maka Halima za ta amince da aurenka fa?”

“Toh…!” Zura mata ido ya yi cike da mamaki, ya miqe.

“Mi ki ke nufi? Kin san wace ce Halima?”

Ta kalle shi, “Qwarai abu ne fa da ya shafi mijina da aikinsa da nutsuwarsa, ya za a yi ba zan bi in sani ba? Kar ka manta ni ma fa na iya naci da dagiya a kan abin da na sa gaba… an ce ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, don haka na yi conviencing, Halima ta ban labarinta, har kuwa na mata alqawarin taimaka mata, amma ita ma na sa ta min alqawari za ta yi min wani abu bayan nan kuma ta amince”.

“Fadimatu wai da gaske ki ke? Yaushe aka yi haka?”

“Kwana uku da suka wuce lokacin da zargi da kishi ya so ya yi nasara a kaina na canja maka fuska, na janye daga gare ka duk kuwa da cewa ba wai fada muke ba komai muna yi sai dai ka ga canji… to a wannan lokacin na yi qoqarin yaqi da zuciyata tare da yi wa kaina fada na kai kukana gun Ubangiji kamar yadda ka san da ma ina zagayawa gun Halima kullum in na je asibiti, ina qoqarin mata hira, wasa, dariya… wataran in ba ta labarai masu ban dariya, wataran in qirqiri labari in ba ta. Wani lokaci…”

Ta yi murmushi, “Wani lokaci in ga tana hawaye, a hankali na fahimci Halima na da boyayyen al’amari da ke mata ciwo, wanda ya shafi mahaifanta da ‘yan uwanta. Akwai wani lamari da ke mata ciwo, yake mata zafi a zuciyarta game da su, don haka na fi ba wa wannan hiran muhimmanci in yi ta ba ta labarin gidanmu, Mamana, yayyuna, qannena… da sauransu. Wani lokaci na kan xauko su Ayman yadda ta ke kuka in ta gansu ya sa na fahimci akwai yara a wani bangare na rayuwarta. Wani lokaci ta yi murmushi, wani lokacin ta yi dariya, wani sa’in kuwa ta fashe da kuka sosai har sai na rungume ta na lallashe ta. A haka har na yi nasara a kanta, ta ba ni labarinta da kanta tana kuka sosai. Duk na ji jikina ya mutu, ta ba ni tausayi matuqa. To amma kowa ba ya wuce qaddararsa, na lallashe ta na kuma yi alqawarin taimaka mata kamar ta fidda tsammani ne da rayuwa da duk wani farin ciki da jin dadi, saboda an cutar da ita, an cutar da zuciyarta sai dai na mata nasiha, na tuna mata kar ta manta da Allah, ta koma gare Shi, na ba ta sabon hope wanda ni ma a nan na samu nawa maslahan…’

Ya kalle ta cikin zumudi da son sanin labarinta, ya ce, “Fadimatu wace ce Halima?”

Ta kalle shi lokaci na farko da ta ga ya saki layi, ta yi murmushi boye abin da ke zuciyarta, ta ce, “An kira magriba bayan isha’i zan ba ka labarin Halima, zan fada maka wace ce Halima”.

“To shi ke nan. Allah ya kai mu”.

Ya miqe, “bari in wuce masallaci”.

Nan ya fice ta bi shi da kallo. Hawaye ya ciko idanunta, ta ce, “Halima ita ce wacce mijina yake kiran sunanta cikin bacci, ita ce yake sambatun kiranta in yana kwance da ni. Ita ce yake son cirowa daga qunci ya sanya ta farin ciki, ya fidda ta daga halin da ta ke ciki itace wacce ka kamu da son ta wanda Radadin son ta da kaunar ta ya mama ye dukkan gangan jiki da ruhinka Halima tazama a yanzu itace mission na rayuwar ka dukkan wani medical research naka yakare a kan ciwonta, nan ta kife kai a kujera ta na hawaye

Ta share hawayenta, “Zan taimaka maka don samun kwanciyar hankalina da naka.

Duk da kasancewar yau rana ce ta farin ciki amma rakube take jikin bango tamkar marayan dantsako. 

Yakamata ace kawo yanzu ta manta da abinda yafaru diba da yanda tasami cikar burinta. Koda yake banan gizo ke sakarba, shin sirrin da Ta boye tsawon lokaci idan ya watse ya rayuwar aurenta zata kasance? 

Ko shakka babu Hajiya laritu bazata barta ba. Tabbas sai ta mayar da rayuwarta cikin kunci gami da fargaba Wanda batasan ranar yayewarsu ba.

Karfe tara na dare aka dauki amarya zuwa Gidan mijinta kamar yanda aka saba,to amma tashin hankalinda maryusha ke  ciki yayi sanadiyar hanata cin amarcin ranar farko adakin mijinta. 

Jim kadan da watsewar yanrakiya ango ya shigo rike da yar ledarsa wacce nasan bai wuce naman KAZA BA.

cikin kaduwa da firgici ta daga kai ta Kalli ledar sannan tayi ajiyar zuciya. Ko shakka babu tasan babu abinda zai hana Misbahu cika burinsa wanda yajima yana fama da mafarkinsa tsawon lokaci. 

Idanuwansa Sun kada sunyi jawur jira kawai yake sugabatar  da   sallolinda ake  binsu  da  kuma  ta  nuna  godiya  ga  Ubangijinsu.

Jimkadan  da  gama  sallar  Misbahu  ya  zauna  kusa  Maryusha  gami  da  rike  hannuwanta cikin  salo  domin  tayar  mata  da  zanne  tsaye. Maryusha  tayi  sauri ta  sake  kallonsa  wanda  ga  alama  itama  ta  harbu  daga  sallonsa na  iya  fara  sarrafata.

Karar  wayar  da ya  fara  ruri  shine  abinda  ya  tsayar  da  hankalinsu  wuri  guda  . Wayar  maryusha ce  ke  wannan  ruri .Duk  da  bakuwar  lamba  ce  amma  ta  sami  karfin  daga  wayar. Muryar  da  taji  tabbas  Hajiya  laritu  ce  wacce  tayi  alkawarin  sai  ta  ruguza  rayuwarta gaba  daya,daga ciki  kuwa  harda  wannan  babbar  rana  wacce  tayi  alkawarin  nunawa  komi  nata  angonta  misbahu. 

"Kada  kiyi  tsammanin  kinci  bullus,wannan ba  daren  amarcinki  bane, Daren  kaddararki  ne. " Abinda  taji  ana  fada  acikin  wayar  kenan  wanda  tasan  hajiya  laritu  ce. 

Shin  wacece  Hajiya  Laritu? Kuma  meyasa  Hajiya  laritu  ke  neman  tarwatsa  rayuwar  Maryusha?  

Allahamdulillah. 

Yana nan tafe acikin wani sabon littafin Mai suna 

DAREN KADDARA 

Cikakken littafin na nan zuwa, ku biyo shafin nan namu.{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post