[Book] Rai Biyu Complete by Khadija Candy

Rai Biyu

Title: Rai Biyu

Author: Khadija Candy

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 742KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Iko sai rabbi, ko ta ina rai ya zama biyu? To, sai kun karanta wannan littafi na marubuciya Khadija Candy mai suna "Rai Biyu" complete hausa novel document a text format. Za ku iya daukarsa a wannan shafi bayan kun karanta taba ka lashe na cikin labarin.

Book Teaser: Bana son na yi aure a gidan da za'a saka min gadon dubu ɗari biyu da hansin su riƙa girmamani suna ganin girman da ganin mahaifina yana da rufin asiri, na fi son na yi aure gidan da za'a saka min gadon miliyan uku su dinga ganin mahaifina talaka ne suna raina min wayo. Ma'ana dai har yanzu ina kan bakana na auren mai kuɗi fiye da talaka!”

Na yi dariya ina sauraren zance ko burin Jidda da ta saba nanata min a duk lokacin da muke zancen aure da ita. 

“Ƙawata ba za ki taɓa ganewa ba, kin fiye maida zancena shirme Wallahi Nawwara rayuwar nan ɗa muke sam bata dace da mu ba”

Dariya na sake yi a karo na biyu kana na dube ta irin duban na nake mata a duk lokacin da nake son ta ɗauki zance na muhimmancin.

“Kina da yawan buri Jidda kamar yadda nima nake da shi, sai dai duk da haka na ki be kai nawa ba, gwargwadon rufin asiri Jidda kuna da shi, amman kina tsawwalawa rayuwarki akan son aure mai kuɗi, ba ko wane kuɗi ba ne na halak, ba ko wane mai kuɗi ba ne bane mutumen arziki, da da yawanzu basa darajanta talaka basa ganin girman iyayen matansu, basa kunyar taka kowa saboda suna ganin suna da kuɗi.

Wasu masu kuɗin maneman mata ne Jidda, ke da kike matarsu sai su wulaƙantaki musamman idan suka sa ke ɗin ba kowa bace, nafi sha'awar auren takala ɗan'uwana mai ilmi da ganin ƙimata, mutumen da zai taimake ni na gyara lahira ta, kuma na inganta rayuwar yaro na, ya mutunta iyayena ko da bayan raina, ni iya wannan ya wadatar da ni matuƙar yaƙar yana da halin da zai iya ciyar da ni”

Jidda ta dafani a lokacin da ta lura da hawayen da ya sauko daga idona ba tare da sani ba har sai da ta yi min magana.

“Share hawayenki Nawwara, nasan abunda kike ji, amman rayuwar nan da muke ciki ne bata da daɗi, ka tashi cikin talauci ka girma a haka kai ma kana son sauyin rayuwa, kana son ka taimaki iyayenka, karatu nan ma fa Nawwara ba zai yiyu ba idan babu kuɗi, idan baka da kuɗi kai ba kowa ba ne, yadda aka ga dama haka ake takaka, babu mai son takala sai Allah”

Na yi murmushi ita kuma ta amsa kiran da Mahaifiyarta take mata ta tashi. Na san yadda ƙawata take ji haƙiƙa rayuwar talauci babu daɗi, sai dai ni har yanzu rayuwar masu kuɗi bata burgeni saboda nasan yadda take, ba ko wace ƴar takala ce ke auren mai kuɗi ta jidaɗin rayuwaba, ko da kuwa ya aje mata banki ne a cikin ɗakinta.

“Kin gani ko kullum baƙin tuwon dawa sai na masara babu wani sauyi, ni Wallahi rayuwar nan ta isheni, ni ina tausayin rayuwar yarana idan nayi aure zasu tashi suna cin tuwon dawa duk suyi baƙi, ke Wallahi Nawwara da kwana ɗari da talaka ƙara kwana ɗaya da mai kuɗi”

Jidda ce take wannan maganar, yayinda take dire kwanon samira mai ɗauke da ƙatowar mulmular tuwon dawa da miyar kuka, agabana.

‘Allah sarki rayuwa ku har kun samu tuwon dawa’

Na faɗa a raina, a fili kuma sai na ce.

“Aifa sai ki yi mitarki kuma ki ci tuwonki dan ni dai a ƙoshe na ke”

Jidda ta wara ido tana min kallonta na iskanci wanda ta saba min a duk lokacin da aljannun rashin mutunci suka hau kanta.

“Maman Nura, Maman Nura yi sauri ki zo”

Nayi saurin kai hannu ina rufe mata baki jin tana kiran mahaifiyarta, nasan wata ƙulalliya zata ƙulla min.

“Jid”

Ban yi furucin ba sai ga Maman Nura a cikin ɗakin wato mahaifiyar Jidda.

“Maman Nura tace gida zata je da shi”

Jidda ta faɗa sai Maman Nura ta ce

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Bakar Wasika Complete by Khadija Candy{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post