[Book] Walijam Complete by Maman Teddy

Walijam

Title: Walijam

Author: Maman Teddy

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story, Fiction

Doc Size: 161KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Maraba, ku dauka tare da sauke sabon littafin marubuciya Maman Teddy mai suna "Walijam" complete hausa novel document. Labarin gaba dayansa ta sadaukar da shi ga fulani.

Book Teaser: Wani irin iska ne yake tashi daga sararin samaniya ,wanda in badon yanayin da ake ciki na Rani ba da tabbas ka alamta cewa wannan goguwar ruwan sama ne yake dab da tsinkewa. Wata yar budurwan bafullatana ce na hango wacce a shekaru bazata haura 13 ba tana sanye da kayan ta na sak'i ,da ka gane ta kaga bafullatana ta usul ,sanye take da kayan fulani farar sake da akayi masa ado da blue din abawa hannun ta dauke da dan madaidaicin sanda ,wanda yayi dai dai da tsawon wannan yarinyar bafullatanan .

Gyefe guda ta juya da idanun ta tana mai bin shanayen ta da kallo , wanda suke garke guda ,don yawon su ya 6aci dai dai yawon garken shanaye amma duka ita ce mai kula dasu a wannan asararen dajin . Babu kowa daga ita sai dabbobinta . Ganin irin goguwar da sanyayyar iskan dake kadawa ne yasa ta bin sararin samaniya da kallo tana kallon yanayin faduwar rana ,wanda ganin yanayin sanyin da rana yayi yasa ta fahimtar cewa lokacin komawan ta Rugar su tayi . 

Nufar shanayen tayi hadi da masu magana ta harshen fulani hadi da fara kadasu da sandar ta ,su kuma shanayen suna yin gaba tana mai biye a bayansu a haka har suka fara ficewa daga wannan dajin .

Tafiya ce sukayi ta mai tsawo kamin su fara shiga cikin rugar su ta Surbajo . Nan na fara hango bukka dai_dai bakaman bukkan sauran rugar fulani ba , don idan ka wuce bukka daya sao kayi dan dogon tafiya kamin ka kara saduwa da wani bukkan .

Nikam Maman teddy nace rugar SURBAJO kenan , rugar surbajo ya samu wannan suna ne daga wurin Makotan wannan ruga ,wanda yawon yammatan wannan ruga yasa ake kirar su da sunan Rugar surbajo . Yara tun suna da kankantan shekaru basa wuce shekara 7 ko 8 ake aurar dasu ,sai idan sun yi girma akai su dakunan maxajen su ,bikin al'adar su kadai sukeyi masu wato shad'i.

Hakan yasa wannan ruga  da akwai yara kanana sosai ga yammata ,amma ko wacce ka gani da Auren ta ,idan kuma babu karama ce wadda bata shekara shida ba tom da akwai wanda yake rikon ta . A takaice dai duk yarinyar da ka gani indai takai shekara 8 tom tana da miji a wannan ruga .

Rugar surbajo rugace da ta tara fulani ,wanda ba mazauna ba ,idan suka tafi kiwon cirani sai sufi shekara goma biyar basu waiwayo rigar surbajo ba . Idan kaga Budurwa ta waiwayo rugar surbajo tarewan tane yayi daga nan sao ayi bikin shadi a kaiki Garken mijinki .

Duk wacce baayi bikin tarewar taba to tana tafiya yawon cirani wato kiwo da shanayen ta amma su yammatan da suke da Aure shekara daya ce sukeyi wasu ma basa kaiwa suke dawowa rugar su ,a gansu suna yan kwanaki suke kara komawa...wannan dai shine kadan daga cikin Al'adan wannan Ruga . Bari mucigaba da labari WALIJAAM ,komai xamuji daga gaba .

Also Download: Bafulatanan Ruga Book 1 Complete by Maman Teddy

Wannan yarinyan Bafullatanan ce duk wani bukka da zata wuce sai ta tsaya da garken ta ta masu gaisuwa da cewa Ifini jaam kamin ta wuce ,a takaice dai kamin ta isa bukkan su sai da tadan kara tafiya mai tsawo ,amma ahaka kowa ta gani tsakanin ta dashi Ifini jaam , wanda kowa cike da fara'a yake ambaton sunan yarinyar da SHATTU , hakan ne ya tabbatar mun da cewa Wannan ruga ,ruga ce mai hadin kai toh kun kuma san fulani badai hadin kai ba.

Garken ta nufi da shanayen tana kaisu masaukin su ,kamin ta nufi bukkan Mahaifiyarta da ta tadda bata nan a wajen bukkan .

Bukkan ta kutsa kanta hadi da dan dukawa kadan sannan ta shiga daga ciki ,bata tadda Oumman nata ba ne hakan ya tabbatar mata da cewan Oumman tata tayi nisa ,komawa tayi tana rage kayan jikin ta kallabin dake saman kanta hadi da sauke nishin gajiya kamin ta zauna saman tabarman kaban dake bukkan tana magana ita kadai da cewa " _Aradu hande miwadi kugal misomi"._

DOWNLOAD BOOK

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post