[Book] Wutsiyar Rakumi Complete by Billyn Abdul

Wutsiyar Rakumi

Title: Wutsiyar Rakumi

Author: Billyn Abdul Ce

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 921KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Ku dauka tare da sauke cikakken littafin marubuciya Billyn Abdul mai suna "Wutsiyar Rakumi" complete haua novel document. Ita dama wutsiyarsa ta yi nesa da kasa.

Book Teaser: Tun daga farkon dosowa kwanar gidan zaka farajin luguden daga da taɓare, yayinda mata ke arerewa da shewa irinna nishaɗin madaka, hardama masu buɗe hanci su callara guɗa a kwashe da dariya ana ƙara ƙaimi wajen dakan surfen masarar tuwo ko dawa da akeyi.

      Na kutsa kai cikin gidan domin ganema idona wainar da ake toyawa, mata ne da adadinsu zai iya kai goma sha, sun kasu group-group suna daka a turame da aƙalla zasukai huɗu. A gefe kuma ƙarƙashin inuwar dalbejiya wasu matanne dasuka ɗan manyanta zazzaune suna tasu hira da taɓin daddawar sayarwa ta ɗaya a cikinsu, sai wata can gefe tana faman hura wuta a gabanta da bokitan fenti biyu, maida kallona nayi ga wadda ke gefenta tana ta motsa wani abu a tunya tamkar taliya, sai zabga zufa take saboda hucin wutar da itama take aiki kusa da ita, sai kuma da'irar yara daketa sheƙi da ƙasa suna wasa.

       Wanda bai san BABBAN GIDA ba a garin Ɗilau idan yazo zai iya rantsuwa taron biki sukeyi kona suna, sai dai sam ba haka baneba, dukkan waɗannan jama'ar da kuka gani mazauna gidanne, a hakama babu wasu yaran masu wayo da kuma mazan gidan,  wasu sun tafi binni neman kuɗi, yayinda ƙalilan a cikinsu suna waje a majalisun da mazan ƙauyen kan kafa, yara kam wasu an aikesu wasuko hidimar gabansuce ta fiddasu.

             Duk bayanin dazan muku gameda alaƙar jama'ar wannan gida bazaku fahimtaba, dan kuwa ƴaƴan wane dana ƙanne da ƴaƴan ƴaƴa da matansu, kai harma da jikoki sun auro suma kuma sun hayayyafa.

      Malam Buhari shima mazaunine a wannan gida, kuma yana ɗaya daga cikin wannan ahali, matansa uku da ƴaƴa goma cif, matarsa ta farko itace Yalwa, amma suna kiranta da suna baba yalwa, yaranta biyar, uku maza biyu mata, kasancewar mazan sune manya duk sunyi aure, suma matansu na nan acikin gidan, sai ta biyu, Ɗahara, itakam ƴarta ɗaya Ummukulsoom, haihuwarta kusan huɗu amma suna wabi (suna mutuwa bayan ta haihu), sai akan Ummukulsoom ne ALLAH ya barmata, bayan haihuwar Ummu takuma samun ciki, a wajen haihuwar cikinne ta rasu, lokacin Ummu tanada shekara Uku a duniya. Sai amarya Asabe, yaran Asabe huɗu, mata uku sai Namiji ɗaya shine auta.

     Sana'ar Malam Buhari itace Saƙar mafitai da tabarma, fai-fai irinna fulani dadai sauransu, shiyyasa ake cemasa MAI KABA. Bama shiba duka jama'ar gidan wannan sana'ar suce, sai dai kuma wasu sun bari tuni, sai ƙalilan a matan gidan keyi, shidai ya riƙe gam kuma yanacin amfaninta, dan yakan ɗauka yashiga birnin Kaduna da Zaria ya sayar ya dawo gida, wani lokacin kuma ƙanwarsa Laraba dake aure acan take aiko ɗanta ya karɓa kokuma ita tazo da kanta.

      Da wannan sana'ar malam Buhari ke riƙe da iyalansa, sai noma da yake a kowacce damuna.

       Matasan ƴan mata kusan bakwai da shekarunsu bazasu gaza sha biyarba suka shigo a tare, kowacce kanta ɗauke da bokitin fenti alamar ruwa suka ɗebo. Sannu matan dake surfe a tsakar gida suka shiga yimusu, suko suna amsawa kowacce na nufar sashensu.

      Baba Yalwa dake faman zufa a gindin murhu ta riƙe ƙugu bayan taja murfin tukunyar taliyarta ƴar murji ta siyarwa ta rufe.

     ”K Hadiza ina kuka baro Umma?”.

     Wadda aka kira hadiza ta sauke ruwan kanta tana ɓata fuska, “Yo Baba yalwa tana can baya wannan mayen saurayin nata Basiru ya tsaidata wai zai koma makaranta suna sallama”.

     Ashariya baba yalwa ta lailayo ta dire, “Kai amma ƴarnan anyi tsinanniya, to ni kodai lallatseta yakeyima shiyyasa sukabi suka nanuƙe ma juna?”.

     Kwashe da dariya matan gidan sukayi, dukda kuwa akwai surukanta matan ƴaƴanta a ciki. Kafin wata ta samu damar tofa tata Ummu tayi sallama. Tamkar zasuga abinda Baba yalwa ta ambata a jikin Ummu, duk sai suka zuba mata idanu. 

     Gaba ɗaya sai Ummu taji ta ƙara muzanta, sum-sum ta nufi inda baba yalwa take a gindin murhu...

     “Sai yanzu kuka gama iskancin?”.

    Furucin baba yalwa ya daki kunnen Ummu, cikin rikicewa ta ɗaga idanunta da har sun fara tara ƙwalla ta dubeta, “Baba iskanci kuma?”.

     “Oh tambayata ma kike na sake maimaita miki?”.

     A hankali Ummu ta girgiza kanta alamun a'a.

   Baba yalwa taja tsaki, “ki kikaima Hanne ruwan wajenta, dan ita ta rantamin  na ɗora taliyar, tun da ke kinacan wajen saurayi, da kinsan ma bazaki ɗebomin da wuriba ai da bakice zakijeba mai mugun hali kawai, yadai gama lalataki yagano wadda ta fiki a birni ya aure”.

      “Wannan magana ai zaune take baba yalwa, tunda iyayensa suka bijirema wannan auren ai nasan hanyar kuɓuta suke nema”. ‘Cewar Rashida dake ƙoƙarin dama kunun tsamiya itama na saidawa ne’.

      Baba yalwa ta kyaɓe baki tana sauke tukunyar taliyarta a kasa, “To ai idon Ubanta ya rufe ya kasa gane haka rahida, saboda ita ƴar mai ce ba'ason ɓacin ranta, muna nandai maga yanda za'a ƙare kuma ai”.

     Nanma dariya matan suka sanya, kowa yashiga jifan Ummu da magana mara daɗi.

      Ummu dai batace komaiba, ta ɗauki ruwan ta nufi sashen Hanne matar yayansu ta juye mata ruwan ta fito, ganin sauran yaran duk bazasu komaba itama saita nufi sashensu ta ajiye bokitin tana cire hijjabinta daya jiƙe da ruwa, yayinda ƙasan zuciyarta ke ƙuna da tausayin kanta. Tabbas ƴaƴa da yawa marayu sukan tsinci kansu a gararin rayuwa fiyema da nata, maraicin rashin uwa maraicine mai ciwo, sai dai babu yanda bawa ya isa jayayya da hukuncin ALLAH, bayan rasuwar mahaifiyarta riƙonta ya koma hannun kakarsune data haifi mahaifinsu, wato Innayo.

        Kamar yanda na sanar muku tun farko mahaifiyar *_Ummukulsoom_* ALLAH yay mata rasuwa tun tana shekaru Uku a duniya, itace matar Malam buhari ta biyu, ALLAH ya jarabceta da haihuwar ƴaƴa suna wabi, (ma'ana suna rasuwa bayan ta haihu), saida tai haihuwa huɗu ƴaƴan na komawa sanan ALLAH ya zaunar mata da Ummukulsoom, an tayata murna sosai har ALLAH ya sake bata wani cikin, lokacin haihuwarsane kuma ALLAH ya ɗauketa itada cikin gaba ɗaya. Ta tafi tabar marainiyar ƴarta Ummukulsoom.

      Bayan rasuwar mahaifiyar Ummu rainonta ya koma hannun kakarsune, wato mahaifiyar malam buhari innayo, wannan shine dalilin tashin Ummukulsoom cikin tsananin gata, dan innayo batason taji kukan Ummu, idan kuwa taji saitabi ba'asi, daya kasance cikin matan gidanne sai sun fuskanci ɓacin ranta, idan kuwa yaƴansune saita ramawa Ummu.

      Wannan gata da Ummu ke samu fiye da duk yaran gidanne yasaka kowa tsanarta, ko aikane indai Innayo na kusa babu wanda ya isa saka Ummu ko miƙomin. Shi kansa Malam buhari abun na damunsa, dan matansa kullum cikin ƙorafin mahaifiyarsa tafi kaunar Ummu, bata son ƴaƴansu suke. Idan yatari innayo da roƙon taɗan dinga sassauta son da takema Ummukulsoom kodan sauran yaran saita haushi da masifa, har saiya koma yana hurwar bata haƙuri.

        Abin tausayi ga Ummu shine rasuwar innayo lokacin tana shekara tara a duniya, dukda batada girma sosai tashiga damuwa, musamman idan ta zagayo tana buƙatar wani abu ko an daketa tazo kawo ƙara, saita iske ɗaki wayam babu innayo. Haka zata zauna taita kuka tana ƙwala ma innayo kira.

      Wannan halin data shigane ya haddasa tausayinta mai ƙarfi a zuciyar Malam Buhari, gashi dangin mahaifiyar Ummu sun roƙi a basu ita ya hana, dan bayaso ta banbanta cikin ƴan uwanta. Dole suka haƙura suka bar masa ƴarsa.

        Kasancewar sana'arsa bata zaman gida bace ko yaushe sai ya ɗauki amanar Ummu ya damƙama matansa, tareda badata ɗakin uwar gida baba yalwa.

     A gabansa sun amshi wannan amana, harda faɗin ALLAH ya tayasu riƙo.

      Amma malam Buhari na ɗaga ƙafa yakoma wajen sana'arsa sai abubuwa suka canja ga Ummukulsoom, dan kuwa baƙar wahala da tsangwama ta fara fuskanta kai tsaye gasu baba yalwa da ƴaƴansu, kai har dama duk jama'ar gidan. 

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Wutsiyar Rakumi Complete by Zeetty

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post