[Book] Yar Gata Ce Complete by Miemie Bee

Yar Gata Ce

Title: Yar Gata Ce

Author: Miemie Bee

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 1.5MB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Gataralliya gata dadi. Ina makaranta? Ku sauke cikakken littafin marubuciya Miemie Bee mai suna "Yar Gata Ce" complete hausa novel a text document gashi mun kawo

Book Teaser: _Gidan Alhaji ISMA’IL YUSOUF Unguwar Dutsen Tanshi, Bauchi, Bauchi State._

     Matsakaicin gida ne ba yabo ba fallasa,  na d’an kasuwa meh arziki dai-dai ba irin na hauka d’innan ba, arzikin sa beyi yawa ba be kuma kasa ba. Kalan arzikin Alhj Isma’il Yusouf ake kira da middle class earners. Gidan nasa wanda ya k’unshi sashi biyu, k’arami na bayan ya kasance BQ. Daga babban sashin wata ‘yar yarinya chocolate skinned meh k’imanin shekaru goma sha d’aya (11) ce tafito a gurguje ta nufa kitchen inda ta d’au wani k’warya da magani ciki tafito a hanzarce, tsabagen saurin da take har tafashashshen maganin na zube mata a hannu amman hakan be hana mahaifinta k’olla mata kira a fusace daga ciki ba “MARIAM! MARIAM! Wai d’auko maganin ne har yanzu?! Mschww!” kamar wacce zatayi kuka takaici kwance fal a fuskarta tace, “gani nan zuwa fa Baba” chan k’asa k’asa tace, “haihuwa sekace hauka Ya Allah karkasa Mama ta haifi na mac-” bata k’are maganan ba tayi kacib’us da Baban nata a bakin k’ofa, wani kallo ya galla mata tare da wabje k’waryan maganin ya nufa ciki da hanzari a yayinda Mariam ta juya tayi d’akinsu da k’anwarta YASMIN.

     “Gashi HAFSAH sha kinji? sannu, sannu ko?” Baba wanda ya kasance dark skinned amman kyakkyawa ajin farko yanada ball eyes da long eyelashes with thick brows, sajen fuskarsa ya had’e da moderate gemun dayake ajiyewa, ya kasance cikakken na miji me tsayi dakuma kauri kad’an, sede ba wani babban mutum bane dududu shekarunsa talatin da takwas (38) ne. Maganar yayi ma fara kyakkyawar matar dake kwance kan turkey bed dake d’akin. Mace ce me shekaru talatin da d’aya, (31.) A very young and beautiful woman. Miqe akan gado take tana juyi da tsohon ciki tattare da ita se nishin nak’uda take duk tabi tayi zufa sede sam yanayinta be hana kyawunta wanda yasamo asali daga tushen Fulani fitowa ba. Gefenta wata ungozoma ce zaune tana mata sannu. A sannu a sannu ungozomar tasamu ta d’ura wa Hafsah maganin har a yanzu Baba na a tsaye kan matarsa hankali tashe yana me addu’a a ransa Allah sa Hafsah  ta sauqa lafiya ta haifo masa santaleliyar ‘ya mace. Yake ga ba me kaisa murna in matarsa ta haifi ‘ya mace, ‘ya macen da ze samu yayi wa margayiya beloved sis nasa ZAINAB takwara. Zainab takasance best sibling na Alhaji ISMA’IL cikin yayyun sa mace da miji d’aid’ai dakuma k’annensa mata biyu ciki harda Zainab d’in wacce take binsa dab daga shi se ita. Duk cikinsu ba wacce yafiso suka kuma fi shiri da shaquwa kamar marigayiya Zainab ba, shekaranta d’aya (1) da aure mutuwa yayi halinsa, shekaru biyar (5) da suka wuce kenan yanzu amman Alhaji se gani yake kamar jiya ne rasuwan nata, tun rasuwan ta Alhaji Isma’il yad’au alk’awarin da zaran Hafsah ta sake samun ciki ta haihu muddin mace ce takwaran Zainab sistersa zeyi kodan zena tunawa da alkhairun data masa wanda kad’an daga cikinsu ya kasance na basa jarin fara kasuwancin da yakeyi har a yanzu wanda Allah ya mugun sa masa albarka ciki se bunk’asa yake. 

   Sede kash! tundaga kan Yasmin meh shekaru shida (6) yanzu wacce takasance ‘yar auta cikin yaransa hud’u wanda biyu daga ciki maza ne biyu kuma mata, tun daga nan haihuwa yayi rana wa matarsa mafi so fiye da komai a rayuwansa, yau shekaru hud’u (4) kenan rabuwanta da haihuwa se a shekara na biyar (5) Allah ya azurta ta da wani cikin wanda Alhaji Isma’il yad’au buri da gatan duniya ya aza wa cikin, burinsa a kullum bayyafin Allah yabasa santaleliyar macen da zema margayiya Zainab takwara. 2 months back yaje aikin hajj inda ya riga d’awafi yana rok’an Allah cika mai burinsa.

      Babban d’ansa IBRAHEEM wanda ya kasance fari ne tas wane mahaifiyarsa Hafsah, kyawunsa kuwa sak na mahaifinsa yanada 13years ayanzu yana matakin JSS 3 a karatu a Havardth School wanda ke kusa da unguwansu da k’afa ma suke tahowa se kaisu ne mahaifin keyi a motansa k’iran Corolla S baqa, dan gudun kada suyi latti. Daga Ibraheem se k’anwarsa MARIAM shekaru biyu (2) ne a tsakaninsu. Mariam wacce takasance 11years kyakkyawa ce itama kamanninta irin na Baba kaman Ibraheem sede ita ba fara kamar mahaifiyarsu bace bakuma baqa kaman mahaifin nasu ba chocolate skinned take tana JSS1 a matakin karatu itama a Havardth. Daga Mariam se OMAR shekara d’aya da rabi (1½) ne a tsakaninsu, Omar is  9½ years yana Primary 5 a karatu shima a Havardth, skin colour nasu d’aya da Mariam sede kaman yad’an fita haske. Daga Omar se Yasmeen auta. Shekara uku (3) ne tsakaninsa da Yasmeen she is 6 years tana matakin Primary 2 a karatu itama a Havardth, tanada haske sosai sede bara a kirata da fara ba.

Also Download: Kasaita Complete by Deenad

    Cike da tashin hankali da tsatsan tausayin Hafsah data kasa haihuwa tin tin d’azu, a kaita asibiti kuma taqi, bana wai haihuwan gida takeson yi. Alhaji ya d’ago kai yana kallon Omar daya sasa yima Mamansu fifita kafin Ibraheem ya siyo petir da za’a sa a engine a tayar.

    “Wai a bangon duniya Ibraheem yaje siyo petir d’inne?!” Yayi maganar cikin kakkausar muryan dayasa Omar b’ari ko amsa mahaifin nasu yakasa se fifita Maman su yake da sauri da sauri. “Omar dakai fa nake magana! Ina Ibraheem?”

   “Bbb... Bbaba ban sani ba kaifa ka aikesa siyo petir yana han-” be k’arisa maganan ba Ibraheem yashigo da galon na petir a hannunsa tare da yin Sallama “Baba gash-” tunkud’esa Baba yayi tare da wabje galon d’in “se yanzu kaga daman dawowa kabar mahaifiyarka tana jiqewa anan dan zufa ko?!”

   “A’a fa Baba yau gidan man da layi ne-”

  “Rufa min baki ka wuce kaje kasa ka tayar yanzun nan” ya danqala masa galon d’in a sanyaye yaje ya aiwatar da abinda mahaifinsa ya buqacesa.

  _30 minutes later..._

      A’ee (Ungozoma) ce tafito da jariri nannad’e cikin shawul pink a hannunta batai ko inaba se d’akin Baba inda tayi Sallama, rashin amsawansa yasa kawai tasa kai ta shige, zaune kan Sallaya hannayensa biyu d’age a sama yana addu’a ta tarar dashi. Bayan Sallaman da tayi tanemi gu ta zauna har anan Baba be juyo ya kalleta ba sakamakon kukan jariri dayaji yasa yabar dukkanin abinda yake ya juyo da hanzari “A’ee bade Hafsah ta sauqa ba?”

    “Ga santaleliyar ‘yarku nan anan.”

 “ ‘Ya mace?!” Yayi maganar cike da k’in yarda tsantsan murna da farin ciki “kina nufin mace ta haifa?!” yayi maganan a lokacinda yake amshe jaririyar daga hannunta, yarinyace kyakkyawa ajin farko hanci tun tana k’arama a miqe ba abinda ya rabata da mahaifiyarta Hafsah illa fari da Hafsah tafita, jaririyar ta kasance tana da haske sosai erin masu golden skin d’innan amman da alama harda hasken jarinta tattare da ita nan gaba barata kai hakan haske ba, kyau de kam masha Allah ga gashi kota ina a fuskarta.

    “Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah mai iko kai Allah abin godiya azumin bakancen dana yi alk’awarinyi a gobe zan fara in shaa Allah ya Hafsah da jiki?”

   “Alhamdulillah ta sauqa lafiya tana wanka ne.”

   “Masha Allah! Wannan kyauta haka daga Allah, Hafsah taci kyauta!” nan yayi hud’uba wa jaririyar a b’oye sannan a fili yace, “Allah ya raya ZAINAB, Allah raya Mana ZEEZEE a tafarkin addinin muslinci ya albarkaci rayuwarta AMEEN” shida A’ee suka fad’i a lokaci d’aya. “Toh masha Allah Alhaji Allah ya cika maka burin ka sekaje kaga Hafsah kai mata godiya nikuma barin je in sanar da yaran kyautan da Allah yayi mana gabad’aya” ganin tanada niyyan amshen Zeezee Baba yayi saurin dakatar da ita, “barta kije ki fad’a musu a baki ban gaji da riqe Zeezee ba.”

   “Oh! Oh! Oh! Alhaji anya zakazo kayi adalci tsakanin yaran nan kuwa?”

“Ke ina ruwanki?! Matsa min anan” yana kaiwa nan ya miqe yabar mata d’akin zuwa d’akin Hafsah har alokacin Hafsah bata fito daga bayin ba dan haka yayi zaman jirarta a bisa gado se k’are wa Zeezee kallo yake yana taking nata pictures a yayinda take ta mummutsika jiki da hannu which is damn adorable.

***

     “Assalamu Alaikum gwamnoni da matan shugabannin k’asa” A’ee tayi maganan alokacin da take sa kanta cikin d’akinsu Mariam inda dukansu dasu Ibraheem suka taru sukayi jugum tare da had’a tagumi kowannen su na addu’a a ransa Allah kar yasa mahaifiyarsu ta haifi ‘ya mace, Allah yabata na miji inda hali ma maza biyu su basu damu ba amman de kam banda na mace dan kuwa tun baby’n na ciki basu samu sakat ba ina ace an haifosa yau?

    “Samari da ‘yan matan nawa barasu amsa bane?” Tayi maganan tana k’ok’arin zama gefen Yasmeen dake kusa da Ibraheem, se ayanzu hankalinsu ya buga duk suka dawo da kallonsu kan A’ee dake binsu da kallo fuskan kowannensu d’auke da tambaya da tsantsan tashin hankali. Kusan atare sukace “Baaba A’ee meh Mama ta samu?” Dariya ta saki kad’an sannan tace, “meye haka? Sekace dugjal aka haifo maku?” Nanma almost a tare sukace, “dan Allah mana Baaba A’ee meh Mama tasamu?” Kowannensu na me kasa kunne dan jin amsarta. Ibraheem yayi k’wafa yace, “Allah sa ba mace ba” qannensa suka amsa da “ameen” a takaice ciki harda ‘yar Yasmeen, ita yanzu shikenan baby’n da aka haifa zata k’wace mata autanci.

    “Toh ku kwantar da hankalinku d’a na miji Mama ta samu” ta musu k’arya don ganin reaction nasu, zan so kuga yadda ake sakin hamdala a d’akinga daga meh “yes!!” Se meh “alhamdulillah” semeh “thank god” se me sujjada seda ta barsu suka gama haukansu sannan tace, “lallai kuwa yaran nan! Toh ‘ya mace mesuna Zainab Mamanku tasamu”

      Ibraheem ya had’e gira kai “Baaba A’ee banda wasa please.”

  Mariam tace, “ai ma wasa take bawani macen da Mama ta haifa na miji ne born boy!” tad’an murmusa.

   Omar ya bud’e baki zeyi magana kenan Baba ya k’olla ma Ibraheem kira.

   “Ibraheem! kazo nan kai da k’annenka” anan duk suka tabbatar da maganan A’ee gaskiya ne, “shikenan mace ce, wallahi mace Mama ta haifo mana” Mariam tayi maganan tare da dafe kanta. Omar yaja ‘yar tsuka “mace ko jaraba Adda Mariam?” Yasmeen wacce takaici yabi ya ratsa ta tace, “Adda Mariam yanzu banice auta ba??” Ita abinda ke damunta kenan sau dayawa friends nata a school sukan ce mata da zaran an mata k’anwa ko k’ani shikenan nata ya k’are, Mama da Baba zasu bar sonta se new baby. Ganin Mariam batada niyyan amsata yasa Yasmeen  karkato da kallonta gareda A’ee cikin sauti cike shakwab’a tace, “Baaba wai Baba da Mama zasu bar sona yanzu se baby?” Dogon sumanta A’ee ta shafa a hankali tana mata murmushi “inji wa? Yasmeen d’in Baba? Har a kullum Baba ze cigaba da sonki keda sabuwar k’anwarki Zeezee kinji?” Badan ta yarda ba ta gyad’a mata kai.

    Omar ya miqe tare da fad’in “yanzu duk sallolin daren da muka tayi a iska kenan?” A’ee ta dafe baki in suprise _wato yaran nan har Sallan dare suke kar Mamansu ta haifi ‘ ‘ya mace? Lallai ga dukkan alamu Alhj bareyi adalci tsakanin yaran nan ba._ Tayi tunanin haka a ranta.

    “Wai ina kuke neh?” Baba yayi maganar wannan karan a fusace. Firgit duk suka miqe Ibraheem ne a sahun gaba k’annensa na a bayansa suka fice zuwa d’akin Mama inda suka hango Baba ciki suka shige ciki A’ee na mara musu baya. Akan kujerar 3 seater dake d’akin sukayi lining suka zauna according to girmansu suna me kallon Baba dayayi banza da shigowansu se wasa wa ‘yar jaririyan da bata ma san yana yi ba yake.

👉 Download Now{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post