[Book] Za Ki San Ko Ni Waye Complete by Ummu Maryam

Za Ki San Ko Ni Waye

Title: Za Ki San Ko Ni Waye

Author: Ummi Maryam

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 810KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Tirkashi, kai da jin sunan labarin ka san akwai zafi. Sauke littafin marubuciya Zuwaira (Ummu Maryam) mai suna "Za Ki San Ko Ni Waye" complete hausa novel a text document.

Book Teaser: Wata babe ce zaune cikin wani katafare falo wanda girmanta zai yi 100by100, fadin tsarin falon is a waste of time amman kuyi imagining kyawun falon masu hannu da shuni, budurwan sai kada kafa take da alaman ba gidan ta bane, kaman mai gidan take jira. Wasu hadaddun designer english wears ne jikinta, sai kamshi take, da ganin ta kaga wayayyun babe masu aji. 

Bayan kaman minti talatin aka bude kofa, wata kyakyawa babe ta shigo, aikam afusace wacce ke zaune afalon tamike fuskanta daure, ta nuna wacce ta shigo  da dan yatsa sannan tace

"wato mimi baki ji ko.." bata karasa ba wacce aka kira da mimi ta tuntsure da dariya sanna tace

"ke uban wacece da zaki nuna ni da dan yatsa...ko kin manta ni fina na fiki tunda ubana ba hannun efcc yakeba..banza karuwa.." bata karasaba taji saukan mari

"dan uwarki ni mate dinkice dazaki gayamin magana?...sau nawa nake gaya maki ki rabu da slim...

." itama bata karasaba aka dauke ta da mari

"ke har kin isa ki rabani da slim..uban wa ke baisan ke kike binshiba?..kuma kowa yasan duk big boys din abujan nan ke kadai ke binsu ...kariya" haba nan suka shake junasu.

Sunfi minti biyar suna dukan junansu at the same time suna gayawa junansu bakaken magagganu. Ni kam mamaki nake wanene wannan guy din da kyawawa yanmata ke dukan junansu sabodashi. Fina rike gashin mimi tayi da niyyan janta waje amman weavon din dake kanta ya cire, afusace mimi ta juyo tare da cire designer shoe din dake kafanta ta wullawa fina, da sauri ta kauce ya sami wani katon canema dake jikin bango nan take ta tsage. Itama fina cire nata takamin tayi ta wullawa mimi itama ta kauce ya sami wasu glass decor dake kan dinning nan take suma sauka tarwase, dukkansu babu wacce ta kalli barnan datayi suka cigaba da fadansu fina na cewa

"wallahi bari slim ya dawo....yau sai ya zaba tsakanina dake.." mimi da kanta babu wani gashin kirki kuma fina ta  cire karin datayi ta rike a hannunta gam, mimi sai kokarin amsan brazilian hair dinta take tana cewa

"dalla bani weavon dina, don kudinta ya fi karfinki...." 

"bazan badaba..ki tsaya ahaka har slim ya dawo ya ga kwalkwalin kanki". Itama mimi kaman kan fina tayi ta fixge nata karin gashin. Nan  take itama kanta ya bayyana. Dukkansu biyu babu mai gashin kirkin amman kansu kyare suke . Da weavon mai suna brazilian hair wanda kudinta yakai 600k suke amfani. Kowannesu klokarin amsan karin gashinta take.

Afarfajiyan gidan wani katafaren gate ya bude, wasu manyan motoci kiran bentley guda uku suka shigo gidan, wurin parking suka nufa, suna gama parking da sauri wasu guys guda uku suka fito daga cikin motan gaban at the same time guys biyu suka fito daga cikin motan baya suka nufi motan tsikiya, ahankali daya daga cikin guys din ya bude murfin motan tsakiya. Wani hadadden kafa  nagani sannan  mai kafan ya fito, wooooow, kawai nace don fina da mimi basuyi laifiba da suke cin abun junansu sabodashi, don guy din tamkar shi ya hallici kanshi, wani suitmai tsada ne kwance jikinshi , ahankali ya mika hannu ya amshi  briefcase din dake hannun daya daga  cikin guards dinshi sannan ya sakar masu murmushiai bayyana hakora, wow nasake cewa don wasu fararen hakora nagani tare da wushirya tsakiyansu. Nikam ban taba ganin mutum mai kyau har cikin hakoraba don komai nashi wonderful 

"alhajis na gode" naji yace, nikam wooow na kara cewa don muryanshi so cool and gentle. Suma guys din murmushi suka sakar mashi,  juyawa yayi yafara tafiya, yana daga kai yaga wani range rover sport tare da hummer tsaye, nan take ya hada giran kasa dana sama, don yasan masu motocin. Girman gidan yayi hecter daya, da akwai manyan flat a farfajiyan gidan, amman wanda yafisu girma ya nufa, su kuma guys din sukayi wani bangare daban.  

Yana zuwa bakin kofan falonshi ya taddata bude,  afusace ya shiga falon,  adaidai lokacin da su mimi da fina sukayi wa karin gashinsu kacakaca a falon,  suna ganin shi kowa yasha jinin jikinshi

"kam babban burouban nan!!!!! " saurayin ya fada a fusace,  wanda yasani rasana don yanda yayi magana sai ya firgita duk wanda ke saurarenshi, yacigaba dacewa

"who the fuck gave you bitchies permission to enter my house? " dukansu shuru sukayi, ahankali mimi tace 

"slim ni kake kira bitch? " ta fada tana nuna kanta, a fusace yace 

"aa sugar badake nakeba da uwarki nake... I said uban waye ya bude maku falona? " fina na gani ya watsawa mimi bakar magana ta saki murmushi tare da nufoshi tana cewa

" habibi welcome " harara ya watsa mata tare dacewa 

"gidan ubanki nazo?  Banza yayan barayi" itama fina cewa tayi 

"are referring to me" dan girgiza kanshi yayi sannan yace "da lankwaceccen ubanki nake... Bazaku gayamin ubanda ya baku izinin shigowa gidanaba kafin insa guys dina suci uban da ya haifeku? " fina tace 

"ni na bude" 

"who gave you my password? " ya kara daka mata tsawa

"last weekend  da mukazo b day dinka na rike passwords din... Kasan am smart " 

"kika rike passwords dina don in bana nan  kizo kiyimin sata ko" ido mimi ta bude 

"sata kuma slim... Ni kake cima mutunci haka? " 

"eh mana... Ba sata ubanki yayi efcc suka kamashiba?  Nasan ko kin gada?"  fina bata kara cewa komaiba ta koma baya, takalminta ta dauka da niyyan sakawa, itama mimi designer hand bag dinta ta dauka, ajiye briefcase dinshi yayi gefen inda yake tsaye tare da harde hannuwanshi kan kirjinshi yan kallon yanda fina ta duka ta saka takalminta, mimi zuwa tayi zata wuceshi, ya fixgeta tare da wullata cikin falon

"where did you think you are going?... Ubanwa kuka barwa gashin doki chan" ya nuna weavon din dake sakar falon sannan ya kara cewa

"in kun bar gidan nan sai kun gama gyaramun falona... Banzaye second hand bitchies" irin fixgan da yayiwa mimi yasa batayi gardamaba ta koma tafara kwace karin gashinta tare da maida tro pillows din da suka wullawa junansu. Magananshi kara batawa fina rai yayi, bata kalleshiba tazo zata wuce inda yake, wani irin damka yayi mata tare da turata baya 

"safina kina son nuna min taurin kai ko?... To wallahi in baki gyaramin falonaba dukan tsiya zansa ayi miki  kuma kisan nothing will happen " murtuke fuska tayi kafin tace

" gaskiya ko agidanmu ban aiki so yanzu ma bazanyiba" wani irin dariyan rainin hankali yayi wanda ya kara bayyana kyauwunshi

"ai yarinya kwanda ki fara koya don satan da ubanki minister yayi aka kamashi...bailing shi zai maidaku matsiyata..." bai karasaba ta yaji tace

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Raina Kama Complete by Billyn Abdul

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post