[Book] Dr. Bobby Complete by Aysha A. Rano

Dr. Bobby

Title: Dr Bobby

Author: Aysha A. Rano

Category: Love Story

Doc Size: 227KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Maziyarta barkanku da zuwa. Ku sauke sabon littafin marubuciya Aysha A. Rano mai suna "Dr. Bobby" hausa novel complete document a text format. Littafin fa da alamu zai yi dadin karatu.

Book Teaser: Dogon building ne mai matukar kyau da tsaruwa...sannan yanada girman da baka isa kace ga iya inda ya tsaya ba...daga ciki akwai makeken surrounding mai daukeda shukoki iri daban daban da sukayi matukar qawata wajen...ga wani tafkeken titi da ban samu ganin iya inda ya tsaya ba a shimfide hadda roundabout kamar dai normal hanya...kallo daya zakayima makarantan kasan bana 'ya'yan kananun masu kudi bane domin tun daga yanayin gini da yanda akayi tsarinta ko university albarka...a takaice dai kallo daya zakayima FCNM kasan makaranta ne daya amsa sunanshi makaranta...kuma makaranta ne da duk wanda ka gani a ciki zakasan iyayenshi manya manyan attajirai ne...ko ina yayi tsit sai few students dake kaiwa da kawowa kasancewan duk students suna classes dinsu sai securities da masu gadi da kowa ke various post dinshi...ana wangale gate wata Hadaddiyar Range Rover ta shigo ciki baqa wulik daidai da glasses dinta baqin tint ne a jiki hakan yasa baa iya ganin wanda yake ciki...ta karasa parking lot da aka rabashi biyu tareda indicating staff and students parking area...kai tsaye staff parking area motan ta nufa tayi parking cikin wani babban car park da yafi duk sauran na wurin girma...securities da some of staff da sukaga shigowan motan sukayo inda tayi parking da sauri kamar yanda suka saba duk proprietor yazo har rige rigen zuwa tarbanshi sukeyi snn su take bayanshi har zuwa office dinshi...driver na gama parking ya bude ya fito saidai kafin ya zagaya ya bude motan wadan nan mutanen sun rigashi nan take mutumin dake cikin motan ya bayyana...legs dinshi yafara saukowa waje kafin shima ya fito a hankali yana kallon mutanen...matashi ne da ak'alla bazai wuce 31 to 32 years ba...dogo ne sosae don cikin maza goma da kyar zaa samu guda daya wanda tsayinsu zaizo daidai dashi duk da cewa yanada dan jiki kai tsaye bazaa kirashi da siriri ko kuma mai qiba ba...komai tsawon namiji duk ya jera dashi sai yaga ya zama gajere kusa dashi...sannan yanada wani irin haske mai daukan ido wanda kallo daya zaka mishi ka gane ba full blood bahaushe bane...ko hannunshi ya daga zakaga tarr sbd tsabar farinshi...sanye yake cikin three piece suit dark blue dayayi matching da jikinshi sosae...tun daga gashin kanshi har zuwa sajenshi sun kwanta luf gashi sai shinning suke as a result of gyara da sukesha...yanada round face mai daukeda dogon hanci da matsakaicin baki...sai eyes dinshi da duk ya ware maka su a kanka saika tsorata sbd tsabar girmansu and su kansu eyeballs dinshi abun kallo ne..fararene tas sai wajen bakin kuma nashi ya kasance golden brown...sune irin idanun dake ladabtar da mutum komai rashin mutuncinshi...sune kuma irin idanun da suke sanya mata kware mishi domin kallo daya zakayi musu ka gane ba kowane irin ordinary eyes bane...they are kind of special kaman yanda mamallakinsu shima ya kasance special...hannu yaketa faman mikawa staff din nashi suna gaisawa domin bai son durkuson da suke mai sam...yafi gane suyi musabiha kmr yanda addinin musulunci ya tanadar...bayan sun gama gaisawa suka shiga binshi a baya har zuwa office dinshi as always driver na rikeda brief case dinshi...secretary na ganinsu ta mike da sauri ta bude office din suka shiga...bayan ya zauna ya dauko kudi ya basu suka fita suna zabga mishi godia as always...Obi driver ya ajiye mishi briefcase shima ya fita...Ngozi(his secretary) ta shigo itama ta gaisheshi snn ta mika mashi schedule dinshi tareda wasu files kmr yanda ta saba...bayan ya karba tasake mika mashi wani envelope tana fadin"Sir you have a message from Kinana Hospital"...baice komai ba ya sake karban envelope din ya ajiye...ganin har yanxu tana tsaye yace"is there anything else?.."da sauri tace"Ss..Sir its Doctor Bukar...he said.."bata karasa baya katseta da fadin"hold it... how many times do i have to tell i dont want to hear about him?.."kai a kasa tace"Sorry Sir"...yace"this should be your very last warning...if you dare repeat this mistake again you are fired"...jikinta har ya fara rawa tace"am very sorry sir... i will never do that again"...ba tareda ya sake kallonta ba yace"you can go"..

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Darajar Yayana Complete by Halima K/Mashi

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post