[Book] Jaruma Yazila Complete by Nasiru Muhammad Tijjani

Jaruma Yazila

Title: Jaruma Yazila

Author: Nasiru Muhammad Tijjani

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Adventure Story

Doc Size: 162KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Littafin yaki, wanda marubuci litattafan yaki Nasiru Muhammad Tijjani ya rubuta mai suna "Jaruma Yazila" complete hausa adventure story. Download it now.

Book Teaser: A WANI ZAMANI can baya mai tsawo da ya shude a kasar kisra an yi wani karamin kauye mai suna himsarul aswad ya wanzu a yammacin birnin kisra kuma shi ne gari na karshe wanda yayi iyaka da birnin rum. mutanen birnin himsarul aswad manoma ne wadanda suka sami albarkacin kasa domin agaba daya garuruwan dake kar kashin birnin kisra babu inda ake da arzikin noma kamar himsarul aswad acikin wadannan kauye akwai wani mutum da ake kira hukairu wanda asalinsa dan uwan hakimin garinne amma saboda bambancin ra'ayi da halayyarsu sai hukairu yahakura dazama tare dan uwansa hakimi yakoma daji inda yayi gidansa kusa da gonarsa yaci gabada rayuwa a wajen tare da matarsa guda daya jal wacce akekira humaira shidai hakimin kauyen himsarul aswad wanda ake kira da suna barzuk yakasance azzalumi kuma make taci mai danne hakkin talakawa kamar yadda sarkin kisra ya zamo na wannan lokaci dalilin dayasa kenan ma yadade akan mulkin yana tayin abinda yakeso zanci gaba. Hukairu da barzuk sun kasance hassan da usaini kuma suna matukar kama da junansu tamkar antsaga kara wani abin mamaki shine matansuma yan'uwan junane kuma suma hassana da usainane. 

Sunan matar barzuk nuzaira. Humaira da nuzaira sun shaku da juna ainun kuma har aka yimusu aure basu rabuba tunda agidadaya suke zaune lokacan da hukairu da humaira zasuyi hijira subar cikin kauyen himsarul aswad da kyar hukaira da nuzaira suka rabu domin kankame junayi suka fashe da.matsanancin kuka A wannan lokaci shima Hukairu kuka yake koda yakama. Humaira yana kokarin banbareta daga jikin yar uwarta nuzaira saita dubeshi alokacinda Fuskarta ta jike sharkaf da hawaye tace "yakai mijina saboda me zaka rabani da yar uwata alhalin tunda aka haifemu Bamu taba rabuwaba Nikam da dai ka rabamu gwara ka barnina zauna anan gidan koda kuwa zan zama baiwar sune. ". 

Sa 'adda hukairu yaji wannan batu saiya dada kamuwa da tausayin Humaira "yace yake matata ki sani cewa ba a sonraina zan raba ki da 'yar uwarkiba, sai domin mugayen halayen mijinta Nassey ke magana Tabbas bazan iyaci gaba da kallon irin rashin imani da yake yiwa talakawaba tunda banida IKon Hanashi. Ni a rayuwata bantaba marin wani mutumba bare ma muyi kace nace amma shi dan uwannan nawa ba a kwana ba kwai sai yasa ankewa wani hannu kokafa. Sannan yana kwacewa mutane dukiyarsu ko matansu ya maishesu bayinsu. Kituna cewa ahalin yanzu kina da ciki tsawon wata hudu yaza ayina tafi nabarki acikin wannan hali alhalin ina son nakula da lafiyarki da kaina kuma naga abin dazaki haifa. " 

Sa adda Hukairu yazo nan azancensa sai hukaira ta kara fashe da matsanancin kuka da kyar tayi shiru sannan tace yakai mijina kasani cewa itama 'yar uwata nuzaira a halin yanzu tana. Dauke da juna biyu tsawon watanni hudu dai dai da nawa. Ita haihuwa abuce mai hadarin gasKe. Zan iya rasa rayuwa yayin haihuwar itama zata iya zata iya rasa rayuwarta saboda haka bana son rabuwa da 'yar uwata awannan lokaci, zan so naga ranar da zata haihu. Don haka ina rokonka daka barni na zauna tare da ita har izuwa ranar haihuwarta" hmm soyayya kenan

NA ZAUNA TARE DA ITA HAR IZUWA RANAR HAIHUARTA. Har Hukairu ya budi zaice wani abu sai nuzaira ta tari numfashinsa ta dubi humaira tace yake 'yar uwata kada ki guji mijinki saboda ni domin shima ba shi da kowa face ke, idan babu ke akusa dashi zai iya shiga mugun hali. Ina son ki bishi kutafi tare, kada kidamu dani nayi miki alkawarin komai rintsi bazan haihu ba sai agabanki." Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube humaira takara kamkame nuzaira tafashe da kuka. Haka dai ta hakura sukayi bankwana suka rabu. Tun da hukairu da humaira suka koma daji basu kara ganin mutum ba daga cikin Himsarul Aswad saboda sunyi nesa da garin kimanin tafiyar sa'a bakwai,saidai suna ganin tafiyar fatake. 

Wani iko na allah yanzu Hukairu da Humaira sunsami tsawon Nassey ke magana wata hudu A wannan daji inda shi dakansa yagina musu wani narkeken gida. Harda garken dabbobinsu dasuke kiwo da rumbu na ajiye kayan amfanin gona amma ko sau daya 'yamfashi. Ko 'yan sumame basu taba kawo musu hari ba. Dalili kuwa shine akwai layar sihiri da wani boka yabashi. Wadda ya binneta a tsakiyar gidansa. 

Duk wani mugu idan yazo gidan bazai ganshiba koda da ranane tsaka. A ranar da cikin Humaira yacika wata takwas ne laulayi yayi mata yawa har ya zamana takasa yin komai. Ka wai saita zauna. A tsakar gidan tana kallon hukairu alokacin da yake baiwa dabbobi acikin garkensu. Koda ta dan jima tana kallonsu sai idanunta suka ciko da kwalla, Hawaye ya fara zuba. Yayin da Hukairu juyo yaga halin da take ciki sai hankalinsa ya dugunzuma yabar garken da sauri yazo gareta ya tsuguna ya rike hannunta yace matata ina dalilin kukannan naki shin jikin kine yake ciwo. Kokuwa ninayi miki badaidaiba ?"Lokacinda humaira taji wannan tambayar sai ta gyada kai tace Ba wani abu bane yasa kaga ina zubar da hawaye ba face tunanin cewa abune mawuyaci na sake ganin ranar dani kaina zanyi I rin wannan aiki dakakeyi yanzu domin ina ji ajikina abune mawuyaci na rayu daga hadarin wannan ciki danake dauke dashi." Kodajin haka sai Hukairu yayi murmushi yace. 

Ki daina wannan tunanin naki kisani dawo wata nan bisa umarnin boka nane domin ya tabbatar min dacewa idan kika haihu acikin gari zamu rasa abinda zaki haifa kuma zamurasa duk abinda muka mallaka. Saboda a shekarar daki haihune za ayi mugun fari da cututtuka acikin garin amma mu damuke anan wannan annoba bazata shafemuba. Koda jin haka sai Humaira tayi murmushi cikin karfin hali tace "idan zancenka ya tabbata Nassey ke magana haka ina fatan "yar uwata nuzaira tazo ta haihu tare dani domin kada annobar ta shafi abinda zata haifa." Hukairu yayi ajiyar zuciya yace "nima ina fatan haKan tafaru duk da cewa nasan halin "yar uwarki macece maicika alkawari. Lailai zata zonan ta haihu tare dake cikin kowane hali. Daga wannan rana hukairu yaci gaba da kulada humaira har cikinta ya tsufa sosai harma ranar da nakudarta tazo. 

A wannan ranane hankalin hukairu ya dugunzuma ainun domin basu da makota bare yasamo mace wadda zata karbi aikin ungozoma. Amma dayake dama can Yasami cikakken bayani a wajen wata tsohuwar mace tunkafin subaro cikin gari sai yayi sauri ya shigar da Humaira cikin daki ya kwantar da ita akan shimfida ya shiga taimakamata. A wannan lokacine hadari yagangamo aka fara walkiya da tsawa kafin ajima ruwan sama ya kece kamar da bakin kwarya kuma asannane humaira tafara kwalla ihu sakamakon nakudar data zomata.

Duk da cewa Humaira nacikin tsananin shan wahala duk sanda ta kwala ihu tayi shiru saita kuma kirawo sunan "yar uwarta nuzaira. Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalin Hukairu kenan domin yana tsoron cewa idan nuzaira bata zoba har bayan haihuwar Humaira zata iya shiga cikin wani mugun halin dazata zamo sanadin salwantar Hankalinta ko rayuwarta.Kwatsam ba zato ba tsammanisai hukairu yajiyo sukuwar doki a wajen gidansa kuma adai dai lokacinne kan jaririn yafito daga jikin humaira. Namfa Hukairu yarude yarasa abinda zaiyi shin zai rabu da humairane. Ya ruga waje yagano ko nu zairace tazo. Kokuwa zai tsayane har sai yaga humaira ta haihu lafiya. Yana cikin wasu wasinne yaji humaira ta damki hannunsa da kyar, tace ya kai mijina maza ka ruga izuwa.kofar gida domin ina ji ajikina 'yar uwata ce ta iso kuma na tabbata kodai ta haihu kukuma tana cikin i rin halin da nake ciki. Karka damu dani zan iya kara sa haihu wa da kaina. Cikin matukar damuwa hukairu yace menene tabbacin hakan? Humaira tace shinna taba maka karyane? Hukairu ya girgi za kai yace baki tababa kuma ina gasgata maganarki kamar yadda nake gasgaga maganar ma haifiyata marigayiya. " Koda gama maganar sai ya mike da sauri yaruga da gudu yana fita ya arba da keken doki. Kwance acikin keken dokin nuzairace kaca-kaca da jinin haihuwa gefe kuma ga jaririn data haifa ko motsi bayayi. Itama a kwai a lamun dogon suma tayi cikin razani hukairu ya ruga gareka ya dauki jaririn ya girgiza shi kuma ya kara shi akunnuwansa yaji ko numfashi bayayi. Sai tausayi yakamashi. Adai dai wannan lokacinne kuma yajiyo kukan jarirai acan dakin da ya baro humaira nantake nuzaira tabude idanunta tayi arba da gawar jaririnta data haifa kuma taga hukairu tsaye akanta. Saita fashe da kukan bakin ciki amma da ta jiyo kukan jariri adakin humaira. Sai ta fashe da dariya cikin hanzari subiyun suka ruga izuwa cikin gidan.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post