[Book] Jinkirin Alkhairi Complete by Mugirat Musa

Jinkirin Alkhairi

Title: Jinkirin Alkhairi

Author: Mugirat Musa

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Love Story

Doc Size: 162KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Ku sauke tare da daukar littafin marubuciya Mugirat Musa mai suna "Jinkirin Alkhairi" complete hausa novel text document daga shafinmu na HausaeDown.

Book Teaser: Abakin k'ofar wani gida ginin k'asa na hango wata matashiyar budurwa tsaye da saurayinta ya parker motarsa jeep, saurayin sanye yake da k'ananan tufafi kansa yasha askin samarin zamani kallo d'aya zakayi masa ka gane d'an hamshaki'n mai kud'i ne.

  Saurayin mai suna Ridwan ya jingina jikinsa akan motarsa sai kallon soyayya yake jifar budurwarsa dashi , murmushi ya sakar mata yace"Raihana ki sani ina sonki ina k'aunarki tabbas soyayyarki ta riga tayimin mugun kamu azuciya, aduniya babu abinda nafi muradi sama dake masoyiyata".

 murmushi Raihana tayi tace"soyayyarka tayimin dashe acikin zuciyata ka sani har abada babu mai iya rushe ginin da kayi cikin rayuwata,na riga na baka ragamar rayuwata da amanar zuciya da gangar jikina".

  "karki damu azamantakewar soyayyarmu babu cuta bale cutarwa, nayi miki alk'awarin idan mukayi aure zan baki farin ciki na har abada".

 "dako nafi kowace mace sa'ar samun masoyin gaskiya".

 Ridwan ya kalleta cikin shauk'in so da k'aunarta yace"nima nafi kowane namiji sa'ar samun mace k'yak'k'yawa d'iyar mutunci,yanzu dai ki gayamin abinda kike buk'ata in siyo miki idan zan dawo wata rana".

 Raihana tayi rau rau da idanunta ta shagwab'e fuska kamar zatayi kuka tace"tun yanzu zaka wuce gida habibi?".

 Langwab'e kansa yayi cikin alamar lallashi da tarairaiya yace"eh yanzu zan tafi kiyi hak'uri zan dawo kinji banason ganin b'acin ranki".Bud'e gaban motarsa yayi ya d'auko babbar leda ya mik'a mata ta amsa .

 Zaro kud'i yayi cikin aljihunsa ya bata kud'i dubu talatin ta amshe babu kunya kamar ba budurwa ba, cikin fara'a ta sakar masa murmushi tace"nagode habibi".

 Ridwan ya girgiza mata kai yace"ki daina yimin godiya kinfi k'arfin komai awurina".

  "uhmmmm godiya nake".

 "ki rik'e godiyarki nizan wuce aiki companyn mahaifina".

 "ubangiji ya kaika lafiya".

 "Amin my Raihana".Yana rufe bakinsa ya shige cikin motarsa ya tadda motar ya fice daga bakin k'ofar gidansu Raihana. 

  Raihana tana tsaye tana kallonsa har saida ya b'acewa ganinta, sannan ta juya ta shiga cikin gida hannunta rik'e da ledar daya kawo mata.

 Tana tafiya tana rangaji har ta iso tsakiyar filin gidan ta iske Rayyanatu zaune saman k'aramar kujera tana wankin kayan Raihana dana Inna Zulai, Raihana ta isowa wurin Rayyanatu ta tofar da miyau tace"aikin kenan haka zaki tabbata babu aure tunda kin dauk'i girman kai kin sanya arayuwarki, kece kullum Inna take sawa aiki kamar jaka bazaki tab'a wayewa ba har abada kanki yana cikin duhu! ".

 Rayyanatu taji zafin kalamanta har cikin zuciyarta cikin takaici ta d'ago idanunta ta kalli Raihana tace"naji ni jaka ce babu komai tunda yayar mahaifiyata nakeyiwa biyayya keda yake itace ta zuk'unna ta haifeki baki mayarda ita abakin komai ba, sannan wayewa kuma da kike magana idan ta wuce misali ubangiji ya kareni da irin wayewar zamani".

 Raihana ta hasala sosai domin maganar Rayyana tayi mata rad'ad'i da zafi azuciya cikin masifa da hargowa tace"keeeee lallai wannan yarinyar kin rainani ki kalli tsabar idanuna kicemin ban mayarda Innata abakin komai ba, hmmmmm zaki gane kurenki wata rana idan kika kai hak'urina bango saina fasa miki baki ".

  "duk abinda nace miki ai ke kika fara tsokanata sannan babba jan girmansa yakeyi awurin k'arami,karki manta duk tsoho baiji kunyar hawa jaki ba jaki bazaiji kunyar kayarda tsoho ba".

  "eh tabbas Rayyana kin zama 'yar iskar yarinya amma zan nuna miki ko gaba da gabanta".

  "babu abinda zaki nunamin in banda tara samari a k'ofar gida idan shege yazo yau gobe d'an iska zaizo jibi b'arawo zaki jawo ,kin mayarda bakin k'ofar gidan nan kamar tacin kasuwa ki gyara rayuwarki kafin lokaci ya k'ure miki".

 Raihana ta fashe da dariya sannan ta tsagaita tace"kice hassada kikeyimin saboda inada farin jinin da za'a soni shiyasa idan akace ana sallama dani kike jin bak'in ciki kamar zuciyarki ta fashe,kona tara samari na isa ne shiyasa nake tara samari idan fitsari banza ne kaza tayi mana mu gani".

 Rayyanatu taji rad'ad'i da zafin soka mata magana da Raihana tayi bata sake cewa k'ala ba, saboda tasan idan ta biye mata itace da wahala cigaba da wankin tayi tana shanyawa saman igiyar shanya tufafi. 

 Jin hayaniyarsu yasa Inna Zulai ta fito daga cikin d'aki ta iso wurin Raihana tana k'are mata kallo, cikin alamar mamaki tace"lafiya nake jin kamar ana fad'a keda waye Raihana? ".

 Raihana ta zumb'ura baki kamar zatayi kuka tace"nida wannan 'yar hassadar ce mana".

 "wa cece 'yar hassada kuma ban gane inda maganarki ta dosa ba?".

  Cikin sagarci da shagwab'a ta bud'i baki tace"Rayyanatu mana".

  Cikin harzuk'a da tsantsar Rayyanatu dake kwance cikin k'wayar idanun Inna Zulai tace"mi tayi miki ne?".

 Gaban Rayyanatu sai bugawa yakeyi fat fat fat zuciyarta ta tsinke saboda tasan halin Inna Zulai akan d'iyarta Raihana, zata iya yiwa kowa rashin mutunci muddin akan Raihana ne,kashe kunnenta tayi domin taji irin k'azafin da za'a k'ulla mata".

 "daga kawai na shigo cikin gida zan nufi d'aki shikenan Rayyanatu taga ganina ta dinga zagina tana cemin karuwa, wai ban mayarda uwata abakin komai ba sannan banda b'arayi da 'yan iska babu wad'anda nake tarawa a k'ofar gida sai su".

 Tsantsar takaici da bak'in ciki ne kwance afuskar Inna Zulai wani irin tururin d'aci da zogi zuciyarta keyi cikin k'unar rai ta dakawa Rayyanatu rikitaccen tsawa tace"Rayyana!Abinda zaki kalli Raihana ki gaya mata kenan saboda bakida mutunci da sanin ya kamata!? ".

 Jikin Rayyanatu ya dauk'i kad'uwa da mazari bak'in cikin k'azafin da Raihana tayi mata ne shimfid'e afuskarta, nan da nan hawaye suka shatata afuskarta bakinta yana rawa tace"wa.....llahi Allah In....na ba...nce ma...ta karuwa ba...".

 "Rufemin bakinki! Tambayarki nakeyi ba kuka nace kiyimin ba shegiya munafukar yarinya!".

 "bance mata ka..... ".

 Kafin ta k'arasa maganarta Inna Zulai ta kwasheta da gigitattun maruka biyu masu zafi wanda asanadiyar haka, saida ji da ganin Rayyanatu suka d'auke na wucin gadi ta fita daga cikin hayyacinta ta duk'e k'asa dafe da kuncinta tana zubar da hawayen takaici da rashin iyaye. 

 Kuka takeyi mai k'unshe da tsantsar damuwa da k'uncin rayuwa. 

 Alokacin ne Inna Zulai ta nunata da yatsa cikin kakkausar murya tace"gobe ki sake zaginta kiga irin hukuncin da zanyi miki sai yafi wannan muni arayuwa, keee dan ubanki idan ba hassada ba yadda kike kifin rijiya gaki da bak'in jini haka kikeson 'yata ta kasance, ki kiyayeni banida k'yau lamarina babu sauk'i  bana d'aukar raini da walak'ancin kowa ".

 Raihana tana kallon yadda mahaifiyarta ke tozarta 'yar uwarta amma ko ajikinta saima wani irin farin ciki da dad'i dake kwaranya cikin zuciyarta, murmushi ne kwance afuskarta tana hararar Rayyanatu cikin tsamgwama da *RASHIN SO*.

  Zasu shige d'aki kenan saiga Baba Iliyasu ya shigo cikin tsakiyar gidan bakinsa d'auke da sallama, daga Inna Zulai har Raihana babu wadda ta amsa mishi sallamar, k'arasowa wurinsu yayi ya kallesu cikin nazari da tuhuma yace"Zulai mi kukeyi ne kukayi tsaye cirko cirko?".

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Aurenta Zan Yi Complete by Mugirat Musa


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post