[Book] Masarautar Mayu Complete Hausa Novel by Ummuh Hairan

Masarautar Mayu

Title: Masarautar Mayu

Author: Ummuh Hairan

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: Fiction

Doc Size: 210KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Tirkashi, ita wagga masarauta ba abar zuwa ba aradu. Ku sauke littafin marubuciya Ummuh Hairan mai suna "Masarautar Mayu" complete hausa novel document.

Book Teaser: Farfajiyar gdan sarautar cike yake maqil da mutane da aljanu harma da wasu halittu Dana kasa fahimtar menene, tambura ne algaitu da bushe bushe suke tashi a kowacce kusurwa ta masarautar.

Wani bangare da naga kowa ya mayar da hankalinsa nima nan na nufa na kurɗa na kutsa na shiga tsakiyar taron mutanen dake gurin, ai bankai ga qarasawa ba naji fitsari ya qwacemin saboda sabuwar masifar da idanuna suka ganemin.

Ba komai bane face wani gunki girke tsakiyar filin wanda girmansa ya kere misali, sake ja nayi da baya ba girmansa ne yake kadamin hantar ciki ba aa yanda wangamemen bakinsa yake budewa yana aman jini da wuta a lkc guda shine yafi girgiza imanin ruhina, ban gama shiga wannan tantamar tashin hankalin ba naga wani shirgegen tsuntsu me kama da hankala ya fado tsakiyar filin tik, tare da daga bakinsa sama ya fara wani irin kuka me tayar da tsigar jiki.

Gani nayi kowa dake gurin yana faduwa qasa sumamme kafin wani lkc gurin yayi fetal babu wata halitta me numfashi ciki kuwa har Dani,

Shudewar wani sa'o'i da bazasu wucce uku ba kowa ya fara farfadowa dukkanmu muka tashi tare da yiwa wannan gunki sujjadar girmamawa.

Wata murya ce me amo da hargowa ta fara mgn kamar haka “Sanhu Sanhu ya shugaban allolin duniya haqiqa mun fuskanci matsin rayuwa ta hanyar yunwa qishirwa da fari haɗi da mutuwar dabbobinmu wanda mun sani a duk lkcn da wannan abu ya faɗo cikin birnin Jawal, to shakka babu akwai wata mummunar qaddara da take tunkaromu wanda kake kangemu daga gareta ya shugaban allolin duniya shakka babu cikin qaddarorinmu akwai abinda ya fusata shugabanmu...."

Wata kururuwa gunki Harsan ya saki wacce ta sanya kowa zubewa muka rinqa juyi a qasa, ita kanta qasar girgiza takeyi tana darewa wasu bishiyun suna shigewa cikin qasa.

Dakatawar wannan hargowar yasa wata iska me qarfi tashi tayi sama da wata yar qaramar halitta ta nutse cikin gajimare, iskar ta shude kowa ya miqe ya tsaya cak tare da daga kansa sama,

An dauki kusan rabin saa kafin mu jiyo wani qugi ya fara tunkaro tsakiyar birnin kowa ya toshe kunnensa tare da runtse idanunsu abin ta'ajibi manya da yara maza da mata kowa sai kayan jikinsa ya fara sabulewa suka tsaya tsirara haihuwar uwarsu suka fara gabatar da rawar Jawaleey.

BIKIN JAWALEEY wani bikine na al'ada da ake gudanarwa a masarautar jawal wanda ya samo asali tun farkon kafuwar masarautar shekaru dari tara da suka shude, 

Wannan biki ba qaramin shagali ne a gurin al'ummar wannan birni ba dama maqotansu na kudancin Bahrain saboda  saboda kasancewarsa bikin sheqe aya sannan bikin masoya Kuma bikin nuna bijintar kowanne mutum da irin baiwar maitarsu ta gado tun kakanni.

Sukanyi kwanaki bakwai suna gudanar da wannan shagalin biki ta hanyar kade kade da bushe bushe yammata da samari zasuyita rawa da juyi tsirara dasu, a wannan biki abinda yake bambamta tsakanin matar aure da budurwa guda dayan, matar aure zata sanya baqin qyalle ta rufe al'aurarta sannan zatayi zanen kudan zuma a saman nononta.

Ita Kuma budurwa zata sanya wani jan ganye a saman kan nononta sannan zata sanya jan qyalle ta rufe gabanta, wannan jan ganye da aka lika mata a kan nononta shine yake nuna ta isa aure saboda haka yammatan zasuyi ayari su rinqa zagawa a cikin garin suna raye raye da kade kade, fa'idar hakan shine a wannan zagayen ne idan yarinya taje gaban saurayin da Gunki Harsan ya zaba Mata a matsayin miji wannan ganye da suke Kira sutura zai fadi a gabansa  koda ace sunkai su dari shi wannan saurayi shine zai fara ganin faduwar ganyen to yana ganin haka zai taso ya cire kamfen daya rufe gabansa dashi ya sanya Mata ya rufe mata qirjinta shikenan sai a daukesu akansu gaban gunki Harsan su fadi suyi sujjada wannan shine yake tabbatar da cewa Ubangiji Harsan ya sanya musu albarka, to daga wannan lkcn ta zama matarsa zata bisa gdansa shikenan anyi aure.

Idan kuwa wannan ganyen sutura ya fadi batare da kowanne namiji ya gani ba to wannan budurwa ta barranta da kanta zata tafi inda iyayenta suke tana kuka taje ta fadawa iyayenta abinda ya faru,

Sukuma iyayen da yan'uwanta zasu dauketa su tafi suna kuka su kaita gaban sarki Jamal su fada masa ganyan suturarta ya fadi batare da bayyanar miji ba saboda haka sun sadaukarwa da ubangiji Harsan jinin wannan budurwa.

A gaban danginta da yan uwanta zaa dauketa a jefata dakin ubangiji Harsan da yake cikin gdan sarautar tana kuka tana komai haka aljanun tsafi zasu tsotse jininta sannan a fito da gangar jikinta a gasa a rabar da namanta wa mutane amma banda danginta.

To wannan shekarar ma haka bikin yake kasancewa amma na wannan shekarar ya bambamta dana kowacce shekara saboda kasancewar fara bayyanar Yarimah Isham wato da daya tilo a gurin sarki Jamal wanda ya kasance shine shugaban jaruman masarautar, tsantsar rashin Imani da tausayinsa ta buwayi yankin Zamhar inda anan yankin ne masarautar jawal take, 

Shekarun Yarima Isham Ashirin da bakwai da haihuwa amma bai taba fitowa wajen masarautar ba wannan umarni ne na gunki Harsan, Yarima Isham ya kasance sadaukin jarumi da buwayarsa a duniyar tsafi take neman danne buwayar ubansa sarki Jamal da a zamaninsa ya gagari sarakunan duniya face sarki daya tak a duniya wato sarki Lussar na yankin nahiyar Yamen daya gagareshi bugawa a duniya.

*A WANI* bangare na masarautar jawal kuwa a qarshen katangar gabas da garin akwai wani magidanci me suna Uddatu wanda ya kasance maharbi ne Kuma matalauci ne sosai saboda ya kasance bashida cin yau bashida na gobe amma kullum zai fita daji yayo farautar naman dawa ya kawowa matarsa me suna Uddura  ita Kuma ta sarrafa musu suci ita da mijinta da yarsu qwaya daya tal a duniya wato

 *NAJMAH* wadda itama tunda take a duniya bata taba fita sararin gdansu ba kasancewarta kyakkyawar da duk yankin Zamhar babu kamarta, wannan dalilin ya sanya mahaifinta Uddatu yake boyeta saboda tsoron bayyanarta ga wannan azzalumar masarauta tasu yasan komai zai iya faruwa.

Ya kasance Najmah tanada shekaru goma sha biyar a duniya mahaifinta ya yanke shawarar zai fara fita da ita daji saboda gwajin jarumtarta daya dauki shekaru yana bata horo akanta tare da bata kariya da surrukan tsafinsa wanda yakeda tabbacin matsawar tana tare dasu burin manyan aljanun duniya bazai taba cika akanta ba, 

Ta kasance duk takunta tanayinsa ne cikin halwar tsafin mahaifinta sannan a duk lkcn da zai fita da ita zuwa daji yakan shafeta da wani baqin shuni ya nade dogon gashinta ya sanya mata hula ta yanda duk wanda zai ganta zanyi zaton tsohuwa ce kasantuwar yanda fatarta take yamushewa a duk lkcn data shafa wannan baqin shunin tsafin.

Yauma hakace ta kasance bayan dawowarsu daga bikin Jawaleey suna zaune a farfajiyar gdan nasu sunacin naman gada suna hira tayi wanka ta wanke wannan baqin shunin sunata hirarsu cikin nishadi da iyayenta maharbi Uddatu ne ya dago idanunsa da  suke zubar da hawaye.

Hankalin  Uddaru da yarta Najmah yayi mugun tashi suka dago suka kalleshi Najmah ta matsa kusa dashi tasa zara zaran yatsunta tana share masa hawayensa tace “haqiqa a iyakar tsayin rayuwata dakai ya mahaifina bantaba ganinka cikin irin wannan yanayin tashin hankalinba wanda har ya sanyaka kake zubar da hawaye"

Ajiyar zuciya yayi ya dago fuskar yar tasa yace “yake sarauniyar kyawawan yankin Zamhar! Haqiqa lkc yana gaf da qurewa lkc ya kusa da abubuwa da dama zasu faru a wannan bikin Jawaleeyn da akeyi Yarimah Isham zai fara fitowa sarari kowa ya ganshi, kuma kema ubangiji Rundatu ya umarceni da ki fara zuwa bikin Jawaleey na wannan shekarar"

Dagowa tayi cikin matsananciyar damuwa idanunta na kawo ruwa tace “Amma ya Abbana me hakan yake nufi nasani iyakar sanina baka barina zuwa bikin Jawaleey Kuma ma bayan hakama bazan iya yin irin shigar da sukeyi wajen bikin ba kasani wajibine a gurin duk wanda yaje bikin Jawaleey sai yasha jini sannan sai ya rinqa fita rawar maita da dare nikuma a qa'idar madubin tsafina bai bani damar fita da dare ba sannan ya haramtamin ta'ammali da jini kowanne iri ne idan har hakan ta faru tsarin jikina zai karye zan kasance kamar kabewa kowanne irin qaramin sihiri zai iyayin tasiri a jikina"

Miqewa Uddatu yayi batare da ya bawa yar tasa amsa ba ya nufi dakinsa itama miqewa tayi ta nufi nata dakin tana shiga ta zauna a gefen gadonta ta dauki wata kumfa ta watsa saman wani baqin madubi, wata iskace me qarfi ta taso daga cikin madubin ta kewaye dakin sannan tazo tayi tsiri a gabanta miqewa tayi ta shiga tsakiyar iskar kawai sai ta rikide ta koma wani qaton basamude ta kece da dariya ta sake rikida ta komo asalin kamanninta ta tsaya gaban mudubin tsafin tayi wasu surutanta sannan ta bude manyan lumsassun idanunta akai kawai saiga hoton Yarima Isham ya bayyana yana kaiwa da komawa a tsakiyar dakinsa ta zuba masa ido tana kallonsa kyakkyawan gaske me cikar zatin halitta qirar jarumta ta gama bayyana a jikinsa asalin rashin imaninsa ya bayyana a kwanjinsa, kallonsa kawai takeyi tana murmushi har ya qarasa gaban wata qwarya ya bude ya debi wani ruwa me kama da jini ya kurba ya furzar ya nuna wata katanga da yatsansa wani farin haske ya fito ya kewaye katangar sannan hasken ya rikida ya zama ita, murmushi tayi masa shima yayi Mata murmushi ta nunashi da yatsa tace “dama baka wahalar da kanka da zuciyarka wajen son sanin wacece ni ba nice zan mulkeku da sannu Kuma nice sirrin nasararka idan naga dama zan iya kwace duk wani qwanjinka da sirrikan tsafinka cikin abinda bai wucce qiftawar ido ba, am kada na cikaka da surutu yau zamu hadu dakai a bikin Jawaleey bisa sahalewar ubangijin da nake bautawa wanda yake kareni daka sharrinka da sharrin sauran matsafan duniya...."

Tana gama fadin haka ta daga hannunta ta shafe fuskarsa dagakan allonta ta yanda duk yanda zaiyi bazai iya ganinta ba kuma duk binkicensa bazai iya gano daga wanne yanki na duniya tayi masa mgn ba.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post