Tirkashi: An Kori Minista a Ghana Sakamakon Rashin Zuwa Aiki

Sarah Adwoa Safo

Wata minista a kasar Ghana ta ci taliyar karshe, bayan fadar gwamnatin kasar ta koreta sakamakon share lokaci mai tsayi ba tare da ta je aiki ba.

Tsohuwar ministar, Sarah Adwoa Safo, ministar jinsi, an koreta ne daga aiki bayan rahotanni sun bayyana cewa ta share fiye da shekara guda ba tare da ta je aiki ba.

Also Read: 'Yan Kasar Ghana na Zanga-Zanga Kan Tabarbarewar Tattalin Arziki

Sai dai kawo zuwa yanzu, fada gwamnatin kasar ba ta bayyana da dalilin da ya sa ta kori ministar ba. Amma dai ana rade-radin kan rashin zuwanta aiki ne.

Sai dai kuma BBC ta ruwaito cewa tuni aka nada ministan rikon kwarya a ma’aikatar.{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post