[Book] 'Ya Mace Kyautar Allah Complete by Aaashmad

Ya Mace Kyautar Allah

Title: Ya Mace Kyautar Allah

Author: Aaashmad

Compiler: HED Team

Uploader: HED Team

Category: True Love Story

Doc Size: 583KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Ina makaranta? Ku sauke littafin marubuciya Aaashmad mai suna "Ya Mace Kyautar Allah" complete hausa novel, kuma true life love story ne. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Ban kade kofar da'akayi da karfi ne yasa su saurin juyawa don ganin ko waye hka, *Afeefah* ce ta shigo tana zum6ure zun6ure hawaye cike idonta ba tare da ta bi ta Kansu ba ta nufi hanyar daki da sauri, A fusaace ya daka mata mugun tsawa yace "ke xo nan" a sanyaye ta dawo hawayen da ke cike idonta ya shiga gangarowa fuskarta, *Adnaan* dake xaune gefen babban yayan nasu yyi tsaki yace "kedai gabaki daya rayuwarki ba ki da aikin yi sa na kuka koh? A hka nake ga xa ki qare koda yake ma banga laifin ki ba samun waje kika yi wllh, wawiya kawae" muryar *Ma'mee* su ka ji a falon ashe har ta shigo basu sa ni ba, a fusace take cewa " ke wllh idan baki dinga kama kanki a gidan nn ba sae kin dinga shan mamaki na, hka kawae xa ki sa mutane gaba da kuka a gida, ke yarinya ce ko uwarki ce ta mutu ko uban ki?" Adnaan yace "tambayeta dae Ma'mi, shegantaka kawae don ta ga ba a dukanta, ni da ma xa ki ban izini in saita mata xama a gidan nn" Aliyu kam shiru yyi don kwata kwata bayaso yaji ana wa yar kanwartasa fada shima bada son ranshi yai mata ba, bai ankara ba yaga ma'mee ta daga hannu xata kaiwa Afeefah da ke tsaye gun tana kuka har da shessheka duka, aikam yai xumbur ya miqe yana fadin "ma'mee don Allah kiyi haquri karki daketa kibarni da ita kawai," Adnaan da ransa bae masa ddi ba yace "haba yaya aida ka bari ta kai mata koda daya ne xata maida hankalinta," A tsawa ce Aliyu yace "shut up" ba'shiri kam ya maida sauran maganganunshi ciki yana hararan Afeefah, Aliyu na juyawa yaga babu ma'mee a gurin, janyota yayi ya shiga lallashinta dakyar ya samu ta haqura snn yace ta wuce daki, adnaan kam banda ta6e baki babu abinda yake, miqewa tai tanufi sama tana share hawayenta tashiga dakinta ta kwanta tana maida ajiyar xuciya tana tunanin abinda xata yi ma yayyin nata don rama abinda suka mata taji ddi, bude kofarta da akayi ne yasa ta dago kai don ganin ko waye *jiddah* ce tashigo tana dariya tana fadin "yar lelen yayan mu yau de mun ganku a raana muna labe mun ga duk abinda ya faru, aikam charaf afeefah ta dauka " to sai me? Bai isa yamin fadan bane? kuma ai gwara ni koda munyi fadan a ranar xamu shirya ku fa?, kuma kan ya doke ni ko ya min fada sau daya ku ya maku sau hamsin, xa ki xo kina wani gaya min maganar bnxa sae kace ba ku ku ka ma janyo min ba, kuma wllh sae na rama kmr xata yi kuka ta kare maganar, Daga mata hannu jiddah tai alamar ya isheta "ya isheni haka futsararra dama indai gurin fitsara ne ke gwanace," anyi fitsarar cewar *afeefah* ai ban gayyaceki dakina ba daxa kixo kidinga gaya man magana.A fusace jiddah ta bude qofar tabar dakin, tana fita Afeefah tabi bayanta don ta san inda xa ta, dakin Mami suka nufa gaba daya, Jiddah tace "Mami kina ganin Afeefah daga na mata mgna sae ta kama yi min rashin kunya ko" Mami ta daga kai tana kallon Afeefah, Afeefah ta fashe da kuka tace "Mami wllh su suka fara tsokana na daga mutum yyi min fada a hanya sae su kama min dariya dukansa" Jiddah tace "to Mami tafiya fa take bata kallon hanya saura kadan machine ya bugeta shine wani mutumi ya fara mata fada....." Tsawa Mami ta daka masu tace "duk ku bar min daki na" suka juya suka fita har lkcn Afeefah na hawaye.    

   Afeefah 'ya mace ce ta biyar ga Hajiya Zuwaira snn kaninta uku su ma duk matan, Alhaji Umar mai gidanta dan kasuwa ne da ke xaune Kano da iyalan nasa, mutum ne shi mai rufin Asiri sosae tunda ya wadata 'ya yansa da komae bbu abinda suka rasa na rayuwa, Hajiya Zuwaira da suke ce ma Mami ita ce matarsa ta biyu, bayan  rasuwar Uwargidansa kuma uwar 'ya yansa Maza wato Aliyu da Adnaan, a lkcn Mami na amarya bata fi watanni biyu a gidan ba don da cikin Adnaan ta xo ta sami uwar gidan tasa, Aliyu kuwa na da shekaru biyar a lkcn, tunda ta shigo gidan bata taba samun matsala da matarsa ta farko ba Hajiya fateema har xuwa lkcn da Allah ya karbi ranta bayan ta haifi Faisal da ake ce ma Adnaan da kwana biyu, ssae mutuwar Hajiya fateema ya girgixa Alhaji Umar da amaryarsa Mami, Mami ce ta yi rainon Adnaan da madara har yyi wayo ya fara cin abinci, sae dae har lkcn ko bari bata taba yi ba, dai dai da rana daya bata taba cutan 'ya yan mijin nata ba ta rike su da amana tamkar uwarsu, bata taba barin sun yi rashin uwa ba a duniya don Mami mace ta gari ce, kowa yaba halayenta yake barin mai gidan nata, sae da tayi shekara dai dai har takwas kafin ta samu cikin 'yar ta ta fari wato Nusaiba sae sauran 'ya yan nata shidda duk mata suka biyo baya, Alhaji umar mutum ne me tsattsauran ra'ayi da ya rike policyn cewar sae 'ya yansa  sun yi karatu me xurfi kafin su yi aure, don 'yar sa ta fari Nusaiba sae da ta gama karatun ta na Mass com tayi service snn ya aurar da ita ynxu hka tana xaune gidan mijinta a Katsina, hka ma 'yar sa ta biyu Safiya sae da ta kare karatun ta na Microbiology snn ya aurar da ita, ynxu su shidda mata suka rage, Sadiya, Jiddah, Rahma snn Afeefah, sae Fadila da Sumayya. Jiddah na shekara ta biyu a Jami'a ita da Sadiya suna karanta Biology, Afeefah kuma shigarta Jami'a knn tana karanta Bio Chem,  Sumayya Fadila da Rahma basu kare secondary ba, Afeefah yarinya ce kyakkyawa don duk tafi 'yan gidan kyau da komae ma ka rantse kace ba gida daya suka fito ba idan suka jera da 'yan uwan nata, ga haskenta me daukan ido ga ta doguwa, komae nata daban ne daga na yan gidan nasu, Duk gidan Abbansu ya fi ji da ita, ka rantse kace ita ce auta, komae take so shi yake mata, ga son Duniya da babban yayansu ya Aliyu ya dauka ya dora mata sae dae hkn bae hanasa bata mata ba idan tayi ba dai dai ba hkn yasa take abun da ta ga dama a gidan, sae dae Mami bata daukan shagwaba da kukan da take addabar mutane da shi a gidan.

👉 Download Now

👉 You Might Also Like: Daurin Boye Complete by Safiya Abdullahi Huguma

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post