Yadda Za Ka Gane Budurwarka Kudinka Take So Ba Kai Ba

Abu ne mai wahala mutum ya fahimci shin soyayyar da budurwarsa ke masa ko bazawararsa ta gaskiya ce ko kuwa dai kawai rodi take buga masa a ka.

Bisa wannan dalili na ga ya kamata na yi tattaki don leka Tsangayar Malam Tonga domin nemo ilimi da karin haske. Kun san an ce shi ilimi kogi ne, sai ka gama iyonka za ka ga a bakin gaba kake.

Malam Tonga ya jero tare da lissafo alamomi kwarara guda 8 da ke bayyana cewa budurwarka ko bazawararka fa kudinka ta ke so ba kai din ba.

Gasu nan;

  1. Za ta sa ka rinka kaita shagunan cin abinci masu tsada.
  2. Za ta rinka yin fushi idan ba ka biya mata bukata ba.
  3. Samunka shi ya fi damunta.
  4. Ba za ta iya kashe maka kwandala ba.
  5. Za ta rinka daura maka nauyin da bai da amfani.
  6. Za ta maka barazana ka mata ciki idan kana zina da ita.
  7. Za ta daura maka nauyin gidansu da na ‘yan‘uwanta. 
  8. Ba ta nemanka sai dai idan tana da wata bukata.

Wadannan su ne alamomi kwarara guda takwas da Malam Abdul Tonga ya bayyana. Kuma ga duk wanda ya ke soyayya ya san wadannan alamomi.

Saboda haka, sai ku ankare da kaska, rabi mai jini.


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post