Bayan ta Kashe Aurenta, Jaruma Zarah Diamond ta dawo Kannywood

Zarah Diamond

Jaruma mai tasowa ta masana'antar Kannywood, Zarah Muhammad (Zarah Diamond), wacce ta yi aure a asirce a cikin 2021, ta dawo ruwa, domin kuwa alamu sun nuna tare da tabbatar da cewa auren ta ya mutu.

Saboda tun daga irin hotunan da ta ke ɗorawa a shafinta na Instagram da kuma bidiyon da ta ke yi a shafinta TikTok ya sa mutane su ka fara tunanin babu auren.

A ranar 4 ga Yuni, 2022 jarumar ta ɗora wani bidiyo inda ta nuna su na aikin wani fim mai dogon zango mai suna‘Amaryar Shekara’, wanda darakta Ibrahim Bala ke bada umarni, inda ita kuma ta fito a matsayin likita mai suna Dakta Ameera.

Jarumar ta ɗora hotuna aƙalla 11 da bidiyo ɗaya na wannan aikin da su ke yi. A lokacin ne mutane su ka tabbatar da auren ta ya mutu.

Haka kuma kwanan nan Zarah ta shiga Instagram ta rubuta cewa: “Ni ba aure zan ba, aiki ne na waƙa da fim wanda su ne sana’a ta, pls.”

To, ga dukkan alamu ta shigo ta fita gashi kuma ta kara komowa.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post