Cikakken Bayani Akan Kogin Nilu (River Nile) Daga Saliadeen Sicey

Kogin Nilu

Babban Kogunan Afika, shi ne kirarin da ake yi wa Kogin Nilu sunansa River Nile a Turance, a Larabce kuma بهر نيل Shi ne kogi mafi tsawo a duniya. Tsawonsa ya kai kimanin kilomita 6,650 daidai da milamilai 4,132 Yana kwarara daga arewa zuwa a arewa-maso-yammacin Afirka.

Ya ratsa ƙasashe goma sha ɗaya da suka haɗa da Tanzania, Uganda, Rwanda, Burundi, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango, Kenya, Ethiopia (Habasha), Eritrea, Sudan ta Kudu (South Sudan), Jamhuriyar Sudan (Republic of the Sudan), da kuma Ƙasar Masar, Shi ne masamar ruwa mafi tasiri a duk faɗin ƙasashen Masar da kuma Sudan.

Mafari da Ƙarshe

Asalin Kogin Nilu yana farawa ne daga Tafkin Ɓictoria (Lake Victoria) da ke ƙasar Tanzania Sannan kuma ya ƙare a cikin tekun Meditareniya.

Rassa.

Kogin Nilu kogi ne mai manya-manyan rassa guda uku waɗanda suke bashi ruwa; Shuɗin Kogin Nilu (Blue Nile River); Kogin Atbara, wanda yake gangarowa daga tsaunukan Masar; da kuma Farin Kogin Nilu.

Shuɗin Kogin Nilu

Kogi ne da yake malalowa daga daga Tafkin Tana (Lake Tana) da ke tsaunukan Ƙasar Masar Yana da tsawon kilomita dubu ɗaya da ɗari huɗu (1400) zuwa Kartun, babban birnin Ƙasar Sudan inda yake haɗuwa da Farin Kogin Nilu.

Shuɗin Kogin Nilu shi ne reshe mafi yawan ruwa duk da cewa ruwan nasa yana gudana ne kawai a cikin watannin Juli (July) da kuma Nuwamba (November), Yawan ruwansa ya kai riɓi biyu da ɗigo tara (59%) na yawan ruwan Farin Kogin Nilu waɗanda suke haɗuwa su samar da asalin Kogin Nilu.

Kogi ne da yake da asali daga Sudan ta Kudu sannan ya runtuma zuwa Kartum babban birnin Ƙasar Sudan inda yake haɗuwa da Shuɗin Kogin Nilu. Shi ne reshe mafi tsawo a dukkan Kogunan da suka haɗu suka yi Kogin Nilu.

Kogin Atbara

Kogin Atbara, kogi ne da yake tasowa daga Ethiopia, wanda ke ɓuɓɓugowa daga arewa da Tafkin Tana (Lake Tana). Yana da kimanin tsawon kilomita ɗari takwas (800).  Shi ne yake tsirge wa cikin Tekun Meditareniya.

Mahaɗa

Kogin Nilu yana da mahaɗa guda biyu; gurin da Shuɗin Kogin Nilu yake haɗuwa da Farin Kogin Nilu, da kuma gurin da yake haɗuwa da Kogin Atbara.

Shuɗin Kogin Nilu yana tasowa daga Tafkin Tana ya yi tafiyar kilomita dubu ɗaya da ɗari huɗu zuwa Kartun, babban birnin Ƙasar Sudan sannan ya haɗe da Farin Kogin Nilu wanda shi kuma yake tasowa daga Sudan ta Kudu. Kenan, kogunan biyu suna haɗuwa a cikin Kartun, babban birnin jamhuriyar Sudan.

Bayan sun haɗu sun zama abu guda, daga nan kuma sai kogin ya runtuma ya yi arewa zuwa kilomita ɗari biyar, sai ya haɗu da Kogin Atbara wanda shi kuma zai ɗauka daga nan ya yi tafiyar kilomita dubu ɗaya zuwa cikin Tekun Meditareniya inda yake ƙarewa.

Muhimmanci

Kogin Nilu, yana bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban rayuwar al’ummomin da ke cikin waɗancan ƙasashe goma sha ɗaya da aka ambata a sama. 

“Kogin Nilu, ya kasance wata maɓuɓɓugar rayuwa a Arewa Maso-Gabashin Afirka sama da dubbunan shekaru. Kuma har zuwa yau, al’ummu suna zuwa ɗiban ruwa a gaɓoɓin tekun waɗanda suke zagaye da ɓaraguzan irin kayayyakin amfani na mutanen da suka shuɗe”, Amma duk da haka, ƙasashen Masar da Sudan su suka fi kowace ƙasa cin gajiyar wannan kogi. sun ta’alaƙƙa cigaban Ƙasar Masar da wannan kogin tun zamani mai tsawo da ya shuɗe; zamanin da ake yin komai da dutse suna masu kafa hujja da cewa, dukkan wasu gauruwan ƙasar Masar masu tarihi da kuma ababen tarihi a gaɓoɓin wannan kogi ake samun su. Su kuwa, cewa suka yi: “A wannan zamani da muke ciki, kashi casa’in da biyar cikin ɗari (95%) na Misirawa (Al’ummar Ƙasar Masar baki ɗaya), suna rayuwa a ‘yar tazarar kilomitoci kaɗan da gaɓar kogin Nilu”.

A dukkanin waɗancan ƙasashe da kogin ya ratsa yakan zama kafar samar da ruwan sha; maɓuɓɓugar noman rani da ma na damina; samar da dausayin kiwon dabbobi; haɓɓaka harkar cinikayya; kafar sufuri ta hanyar amfani da jiragen ruwa; samar da hasken wutar lantarki “Madatsan ruwa kamar babban madatsin ruwa mai suna Aswan da ke Masar, an gina shi ne domin cin gajiyar kogin da kuma samar da makamashi ta hanyar amfani da ruwa.

Haka nan wannan muhimmin kogi na Nilu shi ne tsohuwar mahaɗar ‘yan kasuwar Afirka da kuma sauran sassan duniya da suka haɗa da Turai, ƙasashen Larabawa da sauran sassan duniya. Duk kuma da ci gaban fasar sufuri da aka samu ta hanyar jiragen sama da sauransu, wannan tafarki bai mutu murus ba. Ana iya cewa, har gobe ruwa yana maganin dauɗa.

“Kogin Nilu ya ci gaba da zama muhimmin tafarkin kasuwancin da ke sada tsakanin Afirka da kasuwannin da ke Turai da sauran sanna”.

Muhimmancin da wannan kogi yake da shi bai tsaya iya waɗancan ƙasashe goma sha ɗaya da aka ambta a sama ba, “Sananniyar magana ita ce  cewa Kogin Nilu, yana daga cikin fitattun koguna ba wai kawai iya Afirka ba, a’a, da ma duniya baki ɗaya”, kamar yadda ya zo a ruyawar Answes Africa (2020). A wani bincike da McGinnis da Mugira (2019) suka wallafa a shafin Intanet mai suna Water Journalist Africa, sun ruwaito cewa ƙasashen irin su Qatar, Egypt, Lebanon, Kuwait, Saudia Arabia, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Syria sun karɓi hayar filin a gaɓar kogin na Nalisu da faɗinsa ya kai kadada 762,208 (762,208 hectares) a Ƙasar Sudan domin samar da kayan amfanin gona na sayarwa, abincin dabbobi kamar alfalfa da kuma sinadaran mai. 

Hakan ma kuma ɗaiɗaikun ‘yan kasuwa da kamfanoni daga ƙasashen Jordan, Turkey, Egypt, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), da kuma Saudi Arabia suna nan suna kan tattaunawa domin samun hayar ƙasar da faɗinta ya kai kimanin kadada miliyan uku da ɗigo huxu (3.4 millions hectares) amma har Yau ba a kai ga kammala yarjejeniyar ba.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post