[Book] Abadan Complete Hausa Novel by Safiya Abdullahi Huguma

Abadan

Title: Abadan

Author: Safiya Abdullahi Huguma

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 966KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Safiya Abdullahi Huguma mai suna "Abadan" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu complete dinsa.

Book Teaser: A hankali ta tsallako tatitin kai tsaye kuma ta shige dogon layin dake gabanta,ta dubi tsahon layin duk da yawan al'ummar da yake da shi a dade yake babu kowa tankar anyi shara,hakan baya rasa nasaba da irin ranar da ake kodawa kamar mutum yaa dora hannu akansa yace wayyo Allah

sannu a hankali take ci gaba da tafiya tamkar mai tausayin qasa,a zahirance idan ka ganta sai kayi tsammanin ranar bata dameta ba saboda yanayin yadda take tafiya,saidai sam tana daga cikin wadanda rabar ma tafi gallaba,don har Allah Allah take taga ta isa gidansu,saboda leshin dake jikinta dinkin riga da skert da kuma dogon hijabinta mai hannu dake qara mata zafi wanda ya zamo too match ne da kaya jaka da 'yar jakar swagger dake maqale a kafadarta

babu wata doguwar tafiya ta iso qofar gidan nasu wanda ke rukunin gidajen marasa wadata,duk da ginin bulo da bulo ne saidai bai samu arziqin fulasta ba bare a kai ga fenti,ta cire jakar kafadarta tana shirin shiga soron gidan idanunta ya sauka kan hauwa wadda ta cakare cikin kwalliyar atamfa,wani matashin saurayi ke fiskantarta wadda yanayin tsaiwar tasu kawai zai fahimtar da kai zance suke,dauke kanta tayi tamkar bata gansu ba don wannan dabi'a ta hauwan bama ita ba duka yaran gidan na bata haushi

ta tsakiyarsu ta raba zata wuce kasancewar babu wata hanya sai ita taji saurayin na fadin‘’barka da dawowa antyn mu‘’

‘’yauwa sannunku‘’ta amsa masa ba yabo ba fallasa tare da shigewa cikin gidan

hauwa dake binta da harara kamar qwayar idonta zai fado ta ja wani matsiyacin tsaki

''gaskiya haruna kana bada ni wallahi,wai ksi me yasa kullum baka da,burin da ya wuce ka yarfani a gun wannan matar ne,me ma kake nufi ne ni fa ban gane ba''

''yanzu laifi ne kulu don na gaisheda yayarki,kuma fa kin sani tana da kirki wlh,uwa uba ilimi da nutsuwa''

cike da masifa hauwa ta qwalalo ido

''iyeee,to ko zaka koma gurinta ne haruna,a gabana zaka dinga yaba wata uwar mata da ta shekare gaban iyaye aka rasa mai dauka?''

Also Download: Daurin Boye Complete by Safiya Abdullahi Huguma

ganin hauwan ta hau da yawa yasa ya sassauto''haba kulu na,wata kai yake a gurina ai kema kin sani,ni mai zanyi da wata mace a duniya indai ba ke ba?''

duk da koda tan da yayi ta dade a kumbure kafin ta sauko ta yarda suci gaba da tadinsu

sallama tayi tsakar gidan kamar yadda ta saba duk da ta san babu mai amsa mata matuqar ba mamanta bace a tsakar gidan ko hindatu,ile kuwa bata samu kallon arziqi ba bare na tsiya duk da inna hadiza dake zaune gabas da tsakar gidan nasu tana kasa wake da shinkafar siyarwarta cikin samirun da duka suka sha lamba,zaune kusa da ita kuma huwaila ce ke nata zarafin na qulla kunun tsamiya cikin farar leda tana lodawa a botiki

bata fasa ce musu sannunku ba kamar yadda basu fasa ja mata tsaki ba tare da binta da harara har ta cire toms dinta ta kwashesu a hannunta don gudun samun sabani ta shige rumfar mahaifiyarsu ba da sallama,tana iya jiyosu sun fara sana'ar tasu wato yada habaici da baqaqen maganganu

''hmmm idan da ranka kasha kallo,kaje ka gama yawon dandinka ka dawo dakin uwa kayi zamanka''

''kema huwaila idan banda abinki a banza suka qi aurar da ita?ba ana fasa musu kai da cewar kyakkya wa,bace 'yarsu?,ai dole su maisheta jari''

''hmmm,Allah wadaran naka ya lalace kuwa,wataran kuwa za'a dire abun kunya cikin gidan nan,a juri,zuwa rafi da tulu debo ruwa''

duk sunajin abunda suke fada daga ita har maman tata,wanda idan da sabo tuni sun saba,saidai babu mai tanka musu,kan dadduma ta taradda maman tata,da alamu sallar azahar take abatarwa,saboda haka ta sabule jakarta ta ajjiyeta saman kujera hade da hijabinta ta sake yowa tsakar gida don,dauro alwala,har ta gama,alwalar tata basu fasa muna nan maganganganunsu ba,babu wadda ta daga kai ta kalla a cikinsu duk da irin suyar da zuciyrta ke mata da radadi,ta ajjiye,silifas,din da ta daura alwalar tana niyyar shigewa rumfar tasu

isyaku dan wajen inna,hadiza ya tawo a guje hannunsa dauke,da kwanonsha cike da kunu,bata ankara ba taji shi yana bin skert dinta ziwa qafafunta,da,sauri ta kalli yaron dake tsaye qerere ya zuba mata ido tace''haba isyaku me yasa baku iya tafiya ne a hankali?''

baki ya murguda ya galla mata harara

''eh din,ba sai a koya min ba,ban iya ba,aikin banza taqi aure ta damu mutane cikin gida''

ranta ne yayi masifar baci,yaron da a qalla ta bashi shekaru kusan goma sha biyar shi zai tsaya a gabanta yana gaya mata haka,hannunshi ta,finciko ya qaraso gabanta,kafin ta aiwatar da komai ta jiyo muryar inna hadiza cikin kaushi da haya gaga tana fadin

''ke,kada ki kuskura ki taba min yaro wallahi,idan kuwa kika sake hannunki ya kai kanshi to zamu kwashi 'yan kallo dake wallahi''

DOWNLOAD BOOK

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post