[Book] AbdulKadir Complete Hausa Novel by Lubna Sufyan

Abdulkadir

Title: Abdulkadir

Author: Lubna Sufyan

Category: Fiction

Doc Size: 866KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2018

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya Lubna Sufyan mai suna "AbdulKadir" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: *SHIMFIDA*

Alhaji Ahmad Bugaje shine yaro na farko a wajen Alhaji Auwal Bugaje da Hajiya Sa'adatu da suke kira da Daada. Asalinsu yan garin Bugaje ne da yake karamar hukumar Katsina, tsatson su Fulani ne, duk da ba sai an fada maka hakan ba. Yanayin jikin su da hasken fatarsu ma kawai idan ka kalla ya wadatar. Cirani ya kawo kakanninsu garin Kano, da niyyar siye da siyarwa, kafin daga baya su fada harkar canji, harkar da ta zame musu kamar gado a cikin zuri'ar su, dan kuwa itace silar arziqin su. 

Shi kanshi Alhaji Auwal itace sana'ar shi, kafin rasuwar shi kuwa, Allah ya azurta shi da samun yara takwas da tilon matar shi Hajiya Sa'adatu. Ahmad, Sani, Hamisu, Talatu, Sadiya, Maryama, Ali, sai Hafsatu. Sun sami wadattaccen ilimin addini dana boko, wanda a cikinsu daga Sani sai Ali ne suke aikin gwamnati, dukkan su sana'ar canji sukeyi, ko bayan da sukai aure suka hayayyafa. 

Bayan rasuwar Alhaji Auwalu, an raba musu gado a bisa tsari na addini. Ya kuma bar musu tarin dukiya mai yawa, dan a lokacin da wahalar gaske ka kira Bugaje ba'a samu wanda yasan shi ko ya taba jin sunan shi ba, saboda ana damawa dashi a cikin attajiran dake garin Kano. Ita kanta Hajiya Sa'adatu bata rasu ba sai bayan ta aurar da yaran ta mata gabaki dayan su. 

Gidan shi da yake nan Gadon Kaya, a garin Kano, Alhaji Ahmad ne ya gaje shi. Gidane babba, musamman daya kara gyara shi, manyan bangarori ne guda hudu a cikin gidan, sai wani bangare daya shima da yake daban. Ko harabar gidan kanta abin kallo ce. Ya kuma ji dadin kasancewar gidan mallakin shi, dan duk a cikin yaran Alhaji Auwalu shi kadaine ya auri mata har hudu, dukkan su tazarar shekara bibbiyu a tsakanin su, gashi yayi auren wuri saboda tashen kudi da yakeji a lokacin. 

1. Matar shi ta farko, uwargidan shi Hajiya Hasiya da duka yaran suke kira Hajja tana da yara takwas tare dashi:

 1. Muhsin
 2. Yazid
 3. Khadija 
 4. Mubarak
 5. AbdulKadir
 6. Zahra
 7. Nazir
 8. Zainab

Halayyen Hajiya Hasiya sun hada da son girma tamkar ita ta yanke wa kasa cibiya, yawan fada, daukar zuga da son yaranta da kuma matsananciyar rowa. 

2. Hajiya Saratu: Itace matar shi ta biyu, sannan duka yaran gidan suna kiranta da Mama. Tana da yara biyar da Alhaji Auwal dukkan su maza. 

 1. Ahmad (Babangida) 
 2. Yasir da Yazid (Yan biyu) 
 3. Salim
 4. Khalid

Halayen Hajiya Saratu, tana da fuska biyu, a gabanka baka da mai kaunarka kamarta, a bayan idonka kuwa baka da makiya kamarta, tana da gulma da hadin husuma, ga jarabtar cin bashi da Allah ya dora mata. 

3. Hajiya Sakina: Itace matar shi ta uku da yaran suke kira Mami, wadda kuma ita kadai ce ya aura a bazawara, dan shekararta daya da wata uku, Allah yaima mijinta rasuwa bayan yar gajeruwar rashin lafiya dayai fama da ita, ya kuma rasu a lokacin yabarta da cikin wata shidda, ta haifi yarinyar ta mace, bayan ta yayeta ne suka hadu da Alhaji Ahmad Bugaje. Bai aureta ba sai da yai mata alkawarin rike mata yarinyarta, kasancewar mijinta Mahmud maraya kuma tilon namiji a wajen iyayen shi, dan haka sauran yan uwan nashi duk matane, babu wanda yai yunkurin karbar yarinyar da tasaka ma suna Wahidah, dan shine zabin mahaifinta a cewar shi indai ya samu ya mace. Bayan Wahidah ta haifi yara uku da shi

 1. Sa'adatu (Amatullah) 
 2. Aminu
 3. Habib

Halayen Hajiya Sakina, macece mai yawan hakuri da kau da kai, tana da sanyin hali da ko surutu bai dameta ba. 

4. Hajiya Halima: Da yaran duka suke kira Anty. Mata ta hudu kuma amarya a gidan Alhaji Ahmad, yar tsohon Wazirin Kano da Allah yaima rasuwa ce ya aura. Dan a cikin matan shi ita kadai ce take aikin gwamnati, da aikin ta ya aure ta. Allah ya azurta su da yara shidda, saboda tafi sauran matan shi haihuwa gab da gab, kusan abinda akan kira da kwanika. 

 1. Nusaiba
 2. Nabila
 3. Kabiru
 4. Adnan
 5. Barakah 

Kasancewar Hajiya Halima jinin sarauta yasa tana da izza, ko kadan bata shiga harkar kowa, kuma bata daukar raini ko ya yake, zaka iya cewa tana da fada inhar ka shiga gonarta. Sannan tana da matukar kirki da kyauta irin ta saraki. 

*

Duk da karayar arziqin data samu Alhaji Ahmad Bugaje, sanadin yan damfara daya hadu dasu a wajen harkar shi ta canji yana cikin rufin asiri. Duk da abubuwa sun canza mishi sosai da sosai, amman yan uwan shi basu bari ya wulakanta ba, da yake suna da zumunci na gaske. Kuma yana gidan shi na nan gadon kaya har lokacin. 

Sannan har gobe indai zakace Yan gidan Bugaje saika samu wanda ya san wani daga cikin yan gidan, saboda yawan da suke dashi da kuma kasancewar akwai sauran masu arziqi cikin su har zuwa wannan lokacin. 

***

Tafiyar nan zata banbanta da kowacce iri, a karo na farko da SOYAYYA zatai mana jagora a kacokan din tafiyar. Duk da bazai zama dalilin da tafiyar zata kasance babu tangarda ba, banyi alkawari Happily ever after ba, ban yarda akwai shi ba. Sai dai nayi alkawari tafiyar zata kasance irin wadda baku taba cin karo da ita ba. 

Badan alkalamina yafi na kowa ba, sai dan alkalamina daban yake da na kowa. Ku biyo Yan gidan Bugaje a tasu tafiyar da take cike da tsantsar soyayya da cin Amana. 

Tsaye yake jikin bangon wajen, lokaci zuwa lokaci yakan saka hannun shi cikin sumar kan shi, bazai iya tuna ranar karshe da wani abu ya daga mishi hankali haka ba, yanayin yake ji ya zame mishi bako. Kayan da yake jikin shi yabi da kallo, gajeran wando ne na kakin sojoji da ko gwiwar shi bai taba ba, sai rigar wandon mai yankakken hannu, wuyan shi da alamar sarqar da baka ganin kota mecece, sai shi da take wuyan shi, wani dan dogon karfe ne maqale a jiki da yake dauke da sunan shi da kuma lambar aikin shi, dan lokutta da dama idan mutuwa ta gifta, sarqar ce kawai shaidar gane waye da waye ta runtsa da shi. 

Duk da kalar kakin bai hana shi ganin jinin daya bata kayan ba, jinin da kallon da yake mishi yasa wani abu tsinkewa a cikin shi, baida kalmar dazai dora abinda yake ji, saboda jini baya daga mishi hankali, ko kafin aikin shi yana da wata irin dakakkiyar zuciya taban mamaki, yau shine yakejin alamun zufa a goshin shi da ganin jini a jikin rigar shi. 

"Paapi zan sha ruwa..."

Muryar Fajr ta doki kunnuwan shi tana tuna mishi cewar bashi kadai bane a wajen. Dan juyawa yayi yana kallon su, Fajr da yake cikin shekarun shi na biyar yanzun, dan dai yana da girman jiki da tsayin da zaisa kai tunanin ya wuce shekara biyar din da baima karasa ba, yana zaune da kanwar shi da duka watan ta hudu a duniya, yanda ya riketa dam yana sa Abdulkadir leqa yarinyar yaga ko tana numfashi.

"Wanne irin riqo kai ma Ikram haka?"

Kallon shi Fajr yayi yana shagwabe mishi fuska, dan shi ya gaji da rikon yarinyar.

"Ni ina so in sha ruwa. Paapi, Omma fa?"

Hannu Abdulkadir ya mika yana karbar Ikram din daga hannun Fajr, bacci take hankalinta kwance, dan daquna fuska yayi yana son tuna ko ya taba jin kukan yarinyar tun dawowar shi, bata da rigima ko kadan. Idanuwan shi yake hangawa ko zai hango inda zai samo ma Fajr din ruwa batare daya bar wajen ba, bayason motsawa daga inda yake ko likitan zai fito da wani bayani. Kasan zuciyar shi yake ji wani abu tamkar bargo da yake ta haduwa yana kara kauri, yasan shi yake so ya lullube da rashin gaskiyar da yake yawata mishi a ko ina na jikin shi. 

"Fajr ina zan ga ruwa anan?"

Ya fadi, yana gyarama Ikram kwanciya akan kafadar shi, yanda ta kwantar da kanta a jikin shi na nutsar da kadan daga cikin abinda yake ji. Daga idanuwa ya sake yi ya kuwa sauke su kan Mami da ta turo kofar glass din wajen tana takowa, yanzun yake dana sanin kiranta da yayi, amman lokacin daya kira din a rikice yake, baisan abinda ya kamata yayi ba, ita tace ya dauko Waheedah din ya kawota asibiti, daya tashi saiya kwaso harda su Fajr.

Aminu ya hango ya rufo mata baya, sai kuma Salim da Zainab. Ya manta yanda yan gidan su suke, yanayin aikin shi ya manta yanda ko kurjewa kayi indai za'a kaika asibiti mota daya tayi kadan, dan kusan rabinsu sai sunje, in kuka jima baku dawo ba zakuga sauran rabin da aka bari a gida sun biyo bayan su, yana tunanin duk wani asibiti da suke da file a garin Kano sun san Yan gidan Bugaje da wannan al'adar tasu, ba'a ma hanasu shiga. Suna karasowa Zainab ta mika hannu tana karbar Ikram daga hannun shi, baiyi musu ba ya mika mata ita. 

"Ya jikin nata?"

Mami ta tambaye shi, idanuwan shi ya sauke kasa yana tsintar kan shi da kasa hada idanuwa da ita. Sai dai kafin ya amsa Fajr ya riga shi da fadin

"Mami Omma ta fadi, jini mai yawa a kanta..."

Hannu Mami ta miqa ma yaron daya taso yana kama hannunta hadi da zagaya dayan hannun nashi jikin kafafuwan ta, daga idanuwan shi yayi yana saukewa cikin na Abdulkadir da yake tsaye, harshen shi yake ji ya mishi nauyi, dan ya kasa amsa ma Mami tambayar da tai mishi. Rashin gaskiya ne shimfide a fuskar shi. Da wani irin yanayi da yake ji ya mishi wani iri Fajr yake kallon shi, sosai yaron yake kallon shi yana kara shigewa jikin Mami, idanuwan shi na cikin na Abdulkadir yace

"Paapi ne yai pushing (Turewa) dinta ta fadi... Mami Paapi ne..."

Wani irin shiru ya biyo bayan maganar yaron, shiru ne da hayaniyar shi tafi ta surutu, dan ko wani yazo wucewa shirun da yake wajen zai iya taba shi, dakuna fuska Abdulkadir yayi yana son nemo kalmar abinda ya lullube shi. 

'Kunya'

Wata murya ta furta can kasan kwakwalwar shi, sai dai shida kunya nada wata irin tazara da bazata misaltu ba, bata taba kamo shi ba ko acan ba, baisan ma ya akan jita ba, kai tsaye yake dukkan al'amuran shi, yau kam ba kamoshi kawai tayi ba, lullube shi tayi ruf, bargon rashin gaskiya mai kaurin gaske na bin bayanta, numfashin shi ma kamar a lissafe yake jin fitar shi. 

"Mami kinga abinda nake ce miki ko?"

Aminu ya fadi yana korar shirun da yake kewaye da wajen. 


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post