[Book] Abunda Ka Shuka Complete Hausa Novel by Zainab Usman Kumurya

Abunda Ka Shuka

Title: Abunda Ka Shuka

Author: Zainab Usman Kumurya

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Fiction

Doc Size: 1.1MB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Gara ma ka shuka haira, ko hanza ka girbe kayarka cikin salama. Sauke littafin Zainab Usman Kumurya mai suna "Abunda Ka Shuka" complete hausa novel a text document daga nan shafin.

Book Teaser: "Darmanawa,kumbotso local government,kano Nigeria."

...........kiran sallar farko na asuba,a kunnena.ahankali na tashi zaune  ina salati tare da karanto addu'ar tashi Daga bacci.yunkurawa nayi na mike,na lalulubi makunni kwan dakin danake,saboda da akwai wutar nefa.tabarmar Dana tashi Daga kai na nannade bayan na kunnan kwan,haske ya gauraye dakin.jingine tabarmar nayi agefe,na ninke zanin dana lulluba dashi,akan jakar kayada na ajiyeshi.tatsatstsen filon danake kwanciya akai na matsar gefe.dakin fess yake bawani datti,kafin na kwanta seda na share simintin tass.fitowa nayi madaidaicin tsakar gidannamu,iskace take kadawa,kadan_kadan dama lokacin sanyine.kitchen dinmu na nufa, Wanda yake cike da uban shirgi. Kayan hadin fanke na dakko na kwaba,ajiyeshi nayi agefe kafin gari ya waye ya kumburo. Dankalin Hausa dake cikin bugu na fara kwasowa,ina zubawa a wani faranti,Medan girma.seda na cika faranti sannan na fito,tsakar gida.ruwa na jawo arijiya a cikin bokiti tare da dakko wuka na fera ferayewa.seda na ferayeshi duka sannan na fara masa yankan biyar_biyar kamar yadda muke siyarwa.

Kafin nagama feraye dankalin,har masallatai sun shiga sallah.wasuma sun idar.bandaki na shiga nayi tsarki tare da dauro alwala,na koma dakina natada na shimfida kodaddiyar dardumata na tada sallah.ina idarwa na mike da sauri,saboda kar gari yayi haske bangama ayyukanaba.lazimun sallarma sena aikin inayi haka nakeyi kullum.awarar dana dafa tun Daren jiya na dakko nafara yankawa.ina gama yanka awarar,na dakko barzazzen waken kosai na wanke shi,tattasai da attaruhu da albasa na zuba akan waken na nufi kai markade.ba kowa alayin,amma ba'abun danaji saboda na saba fita a irin wannan lokacin. Kofar gidan abude take sedai karota da'akayi. Dasallama na shiga cikin gidan,matar gidan tana bakin rijiya tana Jan ruwa.bokitin hannuna na'ajiye,na tsugunna har kasa ina gaisheta.da fara'arta ta amsamun tare da fadin. " *Maryama* ta babangida,har kin fito kenan,sannunki Allah ya miki albarka. "Ameen mama nagode,bari naje idan aka markada nadawo nadauka. " A'a maryam nasan akwai ayyuka da yawa agabanki,kibari zan turo salihu ya kawo miki,idanna markada. "To mama nagode,idan yazo seya karbi kudin." Toh badamuwa maryama.sallama na mata,na koma gida.sauri_sauri na fito da kaskon suyata,da murhu tsakar gida,inda nake suyata kulkum,itace na hada na saka Leda na kunna. Kafin ya kama na tattare bawon dankalin dana bare.komai danake bukata na aikina na kawoshi gaban murhu.mai na zuba akasko nasa masa albasa,yana soyuwa na fara saka fanke.gari harya fara haske.amma har lokacin matar gidan bata tashiba,tana daki tana bacci,dama kullum sekunsan karfe tare take tashi daga baccin asara.har fanken ya soyu,na kwasheshi,na zuba dankali.salihu ne yashigo gidan da bokitin markade akansa,dasauri na tashi na sauke masa.ina masa godiya,daki na shiga na dakko kudin markaden na bashi,fanke na zuba masa atakarda,ya karba ya juya.gishiri da maggi na zuba a kullin kosan,dankalin yana soyuwa,nafara sakin kosai,saboda anfi siyansa shiyasama munfi yinshi da yawa........

        ***************

Yana tsaye gaban mudubin dakinsa,bayan ya gama shirinsa,tsadadden agogo,me matukar kyau da daukai ido, yake daurawa a tsintsiyar hannunsa. da alama,office zeje.wata kyakkyawar budurwace ta turo kofar dakin tashigo,fara Tass da ita,doguwa Medan madaidaicin jiki,doguwar fuska gareta,medauke da dogon hanci har baka dara_daran idanuwanta farare tass, bakinta dankarami,abun sha'awa.taci kwalliya cikin wani tsadadden yadi,maroon colour ya kara haskaka,farar fatarta.takafa daurin dankwali na zamani akanta tashin kamshi takeyi,me dadin gaske.fadada fara'arta tayi,ganin masoyinta muradin zuciyarta.fadawa kirjinsa tayi tana fadin "morning my baby" lumshe idonsa yayi,ya bude,alamun ya amsa.batare da yace komaiba.murmushi tayi domin tasaba da miskilancinsa. Pink Lips dinsa dayake matukar burgeta ta sumbata,tare dan shashshafa wuyansa,zuwa bayansa.behanataba kuma betayataba,ita kadi tayi abunta ta gama.kuma dama ta saba da hakan.hannunsa ta kama tare da fadin"our breakfast is ready,kowa ya hallara kaikadai ake jira shine mommy tace inzo inkiraka.ko kallonta beyiba balle tasa ran ze amsa mata.binta kawai yayi suka fice daga dakin.part din gaba daya suka bari,suka nufi wani shashen daban agidan.samarine guda hudu a zaune akan dinning din.sewata 'yar dattijuwa,wadda saboda gayu da kudi idan kaganta zata zakayi 'yar 40 years ce.kallonsu takeyi cike da sha'awa aranta tana addu'ar Allah yanuna mata ranar auransu.kallon matashin tayi fuskarta dauke da fara'a tace"my son sannu da fitowa.kai kawai yadaga mata batare da yace komaiba.kujerar gefenta yaja ya zauna,gaggaishesa matasan dake kan dinning din suka shigayi,hakan yana nuni da duk kannensane.hannu kawai yake daga musu. Matarce ta dubi,budurwar tare da fadin " *suhailat*, serve us pls. Bata fuska tayi alamun bataso hakanba,nandai babu yanda zatayine.serving din kowa tayi sannan ta koma ta zauna.cike da nutsuwa kowa yaken cin abincinsa.

Kadan yaci kayan breakfast din,sedan tea dayasha ya mike alamun ya gama.kallonsa mommy tayi tace"son" badai katashiba,me kaci anan. Yamutsa fuska yayi,kamar anmasa dole  yace" am ohk mom" ya fada kasa_kasa.bejira mezataceba yayi hanyar barin falon. Suhailat ta bishi da kallo,yanda yake tafiya cikin takunsa na cikakkun maza.hakan bakaramin kara burgeta yakeba. Haidar ne yakalli dan'uwansa dake gefensa,zannurain harnaji sa'ida amma da ambarmu da ciwon baki,baka isa kayi maganaba,sannan seyace zaka saka masa ciwon kai.dariya zannurain yayi,ai yaya *musty* akwai takura turo baki suhailat tayi tace"ai hakan shine daidai dama Ku takuratace da Ku,surutunku yayi yawa."sadiq ne yace"kadai kina kare masoyinkine amma ai gaskiya suka fada. Mommy ce ta dubeta,kyalesu daughter kici gaba da break dinki,karsu makarar dake keda zaki school, sukuma suna gida. Itama Kadan ta karaci ta mike.sallama ta musu.sama ta haura,ta dakko hangbag dinta me matukar kyau wadda tashiga da kayan jikinta.ko mayafi bata yafaba tayi waje. Direban yana ganinta ya taso da sauri,"hajiya sannu da fitowa dafatan kin tashi lafiya. Wani banzan kallo ta wurga masa tana yamutsa fuska tamkar taga kashi. "Malam kayi sauri nika saukeni,ka tsaya kanamun surutun banza daban tashiba zaka ganni. " tuba nake hajiya yafadi hakan yana bude mata bayan motar.tsaki taja,tana harararsa ta shige motar.jiki a sanyaye ya shige gaban motar,yabata wuta  megadi ya wangale musu makeken gate din gidan suka fice.........

         **************

Saleemat ce tayi sallama,amsa mata nayi ina mikawa yaron dake tsaye kosan daya siya.ta shirya abunta cikin uniform dinta,zata tafi school.a kullum naga saleemah,se inji dama nice.inason makaranta inason karatu.amma inaji ina gani anhanani. Kujera ta dakko ta zauna akusa dani kallona takeyi cike da tausayawa. "Saleemat yanaga kin zauna kina kallona lafiya? Girgiza kai tayi tace" babu komai maryam,yanzu ke ahaka zakici gaba da zama,daga bauta se bauta,ba boko ba islamiyya,da kuruciyarki gaskiya ni nagaji da ganin ahaka.murmushi nayi me ciwo,wata kwalla ta tararmun a ido,nace" toya zanyi saleemah,fadan dayafi karfinka seka maidashi wasa,akullum.cikin kaiwa Allah kukana nake,ya kawomun sassauci acikin rayuwata. Saleemah batace komaiba ta mikomun naira darin hannunta gashi ki zubamun kosai da dankali,kuma ni bance ki kyautamunba,kinsan halin *gwaggo ladi* murmushi kawai na mata bance komaiba na zuba na bata.

Karfe Tara na safe,gwaggo ladi ta fito daga dakinta.maganarta azafafece tatabbatarmun data fito.seda gabana yayanke ya fadi,domin kuwa yanzu inta faramun bala'i harse ta kwanta bacci take sararamun.wata tsawa ta dakamun. "Ke maryam! Dan matsiyacin ubanki bakya ganin mutanene kika tsaya kike Abu ahankali,bazakiyi Abu da jikiba.nandanan jikina ya kama rawa,saboda masifar tsoron gwaggo ladi danakeyi. To nikadaice abun yamun yawa ga suya ga sallamar mutane.gashi kuma Allah yasanyawa sana'artamu albarka muna samun ciniki sosai.hakan yasa nake dan Tara layi,amma dazarar gwaggo ladi ta fito zata fara zagina tana tsinemun akan bakin ciki,nake mata shiyasa bana saurin sallamar mutane ita kuma tana daki akwance, koda sallamar mutane bata tayani,kuma innagama ta 'amshe kudinta cas tana zagina.ko biyar bazata barmunba.

Cikin rawar murya nace "kiyi hakuri gwaggo yanzu zankwashe wannan na sallamesu. " da hakurin ta mutu sadakar nawa kika bayar,shagiya munafukar yarinya,kina Abu sum_sum kamar ta Allah.shiru nayi ina cigaba da aikina,idan da sabo,nariga dana saba da halin gwaggo.da masifarta.buta ta dauka ta shige bandaki tana mitarta.

Karfe goma da 'yan mintuna,kamar yadda nasaba kullum,yauma komai ya kare.Alhamdulillah.har nemama akeyi babu.duk wani Abu danasan zan wanke na tattara nakai gurin wanke_wanke.dakin gwaggo,na nufa da sallama.seda taga shan kamshinta sannan ta bani izinin shigowa. Tana kwance akan gadonta.durkusawa nayi abakin gadon  na mika mata jakar danake zuba kudi acikinta.rankwashin kaina tayi Wanda bansan lefin menamata tamun hakanba.hararata takeyi tamkar idonta ze zazzago."munafukar yarinya,me suffar 'yan wuta,kidinga wa mutane wani sum_sum kamar ta Allah,mudai ba'agurinmu kika gado wannan bakin halinba,sedai can agurin dangin ubanki.dauki indomien can guda biyu da akwai biyu kidafomun kikawomun.inda tanunamun na nufa na dauka na fice da saurina dankar nakarayin wani lefin.to yanzu kuma menai mata,ita matarnan komai na mata banmata daidaiba,komai nayi lefine.kullum cikin zagina da aibatani take.hawayen da suka tararmun a idona suka fara zubowa.yaushe zan huta da kuncin rayuwa ni maryam.a hankali nake Jan kafata har bakin murhun,bayana kamar ya balle saboda gajiya.guntun garwashin danayi suya akai na Dora mata indomien. Sharar gidan na kama duk da bawi datti se 'dan kura dayayi. Seda na share gidan Tass,sannan na kwashe indomien a faranti nakai mata daki.tanata faman irga kudin cinikin da mukayi,hakan yasa yanzu bansamu rabon fadaba.saboda gwaggo ladi,idan ta harkar kudi ko magana batayi,shegen San kudi gareta.guntun tuwon danaci jiya da dadaddare shina Dora akan wuta na dumama.bayan ya dumamu na sauke na faraci,saboda matsananciyar yunwar datake addabata.kullum.dama tuwon nishine abincina da safe da daddare.ina cikin ci gwaggo ladi ta kwallamun wani kira, "ke! Ke maryam.dasauri na tashi zuciyata na bugawa jikina ya kama rawa dannasan wannan kiran bana alkhairi bane.

DOWNLOAD BOOK

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post