[Book] Abunda Ke Boye Complete by Feedom

Abunda Ke Boye

Title: Abunda Ke Boye

Author: Feedom

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: True Life Story

Doc Size: 434KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Feedohm mai suna "Abunda Ke Boye" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu daga shafin nan.

Book Teaser:   "Ayyiriri yiriri!Buwale!Asibi!Baraka!Lanto!Kande!kai dukkan Jama'an garin ga ku fito ku gane mani sabon lamari a gidan MALAN LADO………"Cewar wata yar tsamurmurae tsohuwa da ta fito kofae gidan da daurin kirji a jikinta……

  Kamar ana angazo mata da kananan yara daga gidanjen su !haka sukayi dandazo gabanta ko wace sae wurga ido take tana jiran taji me zata fadi Wasu da daurin kirji wasu ma ko dankwali bassu dashi……

 "Kundum lahiya kika tara mutane haka?ko dae tsohun Haukanne ya motsa……"Cewar wata yamutsatstsar tsohuwa da ta iso lokacin dauke da bahon Tafasa a kanta……

  Kundum ta sake rafka guda tana fadin "Yau de Hafsatu ta haihu!Mai tafasa an samu dad'in jika Sae dae mu bamu san waye Uban yaron ba……"ta karashe maganar tare da kecewa da dariyar mugunta har da rike cike……

  Sauran matan dake tsaye suka dauki wani bahaggon salati tare da taba hannunawa suna kiran "Hafsatu kam an cuci Malan lado……"

 Maitafasa kam aje bahon tafasar tayi tana fadin "Watsatstsan Zance kundum!Dama wagga rana nake jira ranar da hafsatu zata haihu wallahi sae ta bar gidan Lado……"

Shiga tayi gidan tana fadin "Ke Hafsatu fito nan munafuka dama yau nake jira sae kin fada man cikin uban waye kika haife a gidan d'ana……"

 Matan garin suka mara mata baya har cikin gidan tare da yaransu ……wasu har bisa katanga ……

  Hafsatu dake duke tsakar dakinta ……ta janyo wuka ta langa langa ta yanke cibiya da kyar sannan ta janyo wani yamutstsan tsumma ta goge jaririyar tare da nadeta cika sannan ta janyo wani tsumma ta shinfida saman lomatsatstsar katifar dake tsakar dakin ta kwantar da jaririyar……

  Jin Mai tafasa na kiranta yasa ta gabanta ya fadi ta mike idonta cike da kwallah ta fita ta tsaya bakin kofar dakin tana sadda kai kasa……

  Gabanta maitafasa tayi birki tana watsa hannu baya "Da kwarankwatsa kinci amana Hafsatu!kin ci amanar lado da aurenki kije kiyi cikin shege sannan ki haife a gidan mijinki……Ke Hafsatu kwarankwatsa da kudi gareni da kotu na makaki a birni a kasheki kowa ya huta da wannan abun kunyar……Fadan Cikin uban waye kika haifa ……?

  Cikin kuka Hafsatu tace "Wallahi inna Cikin lado ne kuma d'iyar lado ce na haifa……!

  "Lado!badae ladon mai tafasa ba……"Matan garin suka dauka tare surutai kasa kasa……

  Maitafasa kam watsa bakaken hannunta tayi saman fuskar Hafsatu tana fadin "Ubanki!Uban lado!nace Uban ladon!D'ana zaki wa sharrin Hafsatu?Ladon dake kwance tsawon Shekaru takwas kamar gawa sae yarda akayi dashi shine zaki haihu ki lik'a mashi ruwan sharri don kinga baya iya magana ……to Uwarsa Maitafasa nanan kuma ban karba ba……"

  Yar matashiyar yarinya ta shigo rike da kwaryar nono ganin gidan a cike ga maitafasa tana ta bala'i yasa ta bata fuska ta matsa tana fadin "Maitafasa lafiya aka cika mana gida haka……?

  "Ina fa lafiya Uwarki ta janyo mana abun kunya……"cewar mai tafasar tare da matsawa kusa da wata bukka tana fadin "Lado!kana ina……?

  Yarinyar ta sake bata fuska tana fadin "Shine dan rashin mutunci zaa cika mana gida haka ……inace uwar tawa tana da miji ……"

  Kundum tace "Da mijinta amma munsan ba cikinshi bane……"

  A Fusace tace "Zanci mutunciki kumdum!ku kuma ku jira har in shiga daki na fito wallahi sae,na fasawa duk shegen da na gani kai……"

  "Wa yace tayi abun kunyar……"Cewar wata mata dake tsaye bakin katanga

 Bata ce masu komae ba ta shige dakin ……ganin jaririyar tana kuka yasa ta dauketa tana jijjigawa ……

Maitafasa kam tana shiga bukkar lado ta rushe da kuka tana fadin "Lado Hafsatu ta cucemu !An cucemu lado anci amanarmu ……wallahi yai Sai na saki Hafsatu lado……"

  Kuka yake mara sauti yana kokarin daga mata hannu amma ya kasa……ido yake rufewa yana budewa da karfi hawaye na fita kamar an bude famfo ……

  "Nace kayi hakuri lado ……Dan cuta an cuceka kamarka a garinnan ace matarka taci amanarka ,to wallahi sae ta bar mana gida yau dinnan ……"

  Zata fita ya zabura ya kife tare da sakin kukan da muryar bata fita ……

Juyowa tayi tana fadin "Ka bar kukan lado nasan yarda kake ji amma,in dae ina raye lado baran,bari a ci mutuncinka ba ……"

  Fita tayi ta iske Har lokacin Hafsatun na tsaye inda ta barta tana kuka……

Kundum tace "Dan cuta an cuceku Maitafasa kamar lado a garinnan don anga baya lafiya sai na ci mutuncinsa……?

  A Fusace maitafasar ta juyo tana fadin "Ke Kundum bansan munafunci……"ta karashe maganar tana watsa hannu gaba

  Matan gidan suka dauki dariya tare da sowa ……Maitafasa kam ture Hafsatu gefe tayi ta fada dakin tana fadin "Yau zaki,bar gidannan,wallahi ……ni maitafasa uwar lado na saki Hafsatu saki uku!ke kwarankwatsa da ana saki Hamsin da yau shi na maki Hafsatu……"ta karashe maganar tana wullo jikkunan,bakon dake tsakar dakin ……

 Yarinyar dake rike da jaririyar ta mike tana fadin "Wane irin wulakancine haka wae……Wannan,rashin adalcine Ummana tana da mijinta amma dan ta haihu shine zaa mana haka?

  Rike haba maitafasa tayi tana fadin "Owo Lauratu rashin kunya zaki man ,To kema wallahi sae kin bar gidan !Uban wa ya sani ko kema ba diyar tashi,bace……"

  Ta karashe maganar tare da turota waje ……Zatayi magana Hafsatun ta rufe mata baki sannan,taja hannunta suka fita daga gidan ba tare da sun dauki komae ba ……

  Mai tafasa ta bisu tana fadin "Shegu gayyar tsiya……"

  Yayin da matan garin da kananan yara suka bisu da ihu da jefa har suka bar garin 

DOWNLOAD BOOK


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post