[Book] Akan Aikina Complete Hausa Novel by Ummu Maher

Akan Aikina

Title: Akan Aikina

Author: Ummu Maher

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Real Life Story

Doc Size: 194KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2021

Description: Sauke littafin marubuciya Ummu Maher mai suna "Akan Aikina" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu cikin sauki.

Book Teaser: Malam!Malam!!Malam!!fito kaga i'kon Allah yarinyar nan ta suma,Malam ya fito da gudu yana kallon yarinyar ya kalli Inna Majaifiyarta yace maza ki d'auki Mumtaz ki  ku fito bari in kirawo Alhaji mu tafi asibiti,Sunan yarinyar kenan Mumtaz.

   Kafin Malam ya dawo Inna ta kalli k'afar Mumtaz sai taga jini yana malala kamar ruwa da gudu ta fito k'ofar gida tana kiran Malam.

  *Wacece Mumtaz*

Mumtaz dai shine asalin sunan ta wanda Mahaifinta ya saka mata saka makon sunan Mahaifiyarshi ne ya saka wa Mumtaz, Asalin Malam Abdullahi Mahaifin Mumtaz y'an jihar Bauchine wanda sun kasance y'an kasuwa ne sosai gidansu suna siyar da kayan masa rufi ta hanyar ne suke samun na cin abinci kuma i'tace hanyar abincin su.

     Kwatsam sai karayar Arzik'i ta samu mahaifinsu Malam Wannan abun ba k'aramin tada musu da hankali yayi ba.

  dalilin da yasa karayar Arzik'i ta same shi shine Mahaifinsu su Malam Wato  Alhaji Jibrin shine yanada wani aboki d'an asalin Maiduguri Alhaji Bukar kusan ma Amininshi shi ne sana'ar Alhaji  Bukar shine siyar da dabbobi daga wannan gari zuwa wannan gari.

    Kwatsam sai wataran Malam Bukar yakawowa abokinshi Alhaji Jibrin ziyara yaga yadda ya bunk'asa da kasuwancinshi na siyarda kayan masa rufi.

    Abun ya tsayawa Alhaji Bukar har yaushe Jibrin zai zama haka a kasuwanci bayan ya fishi tunda ga nan Alhaji bukar ya kafawa abokinshi Jibrin tsana mai tsanani Ya fara bin bokaye don ya raba shi da dukiyarshi,Har yayi nasarar rabashi da komai nashi ya zamo duk abunda ya tab'a sai yayi asararshi tun daga wannan lokacin Alhaji jibrin Mahaifin Abdullahi ya shiga wani mummunan talauci ya zama na koda kayan da zaisa ma sun fara lalacewa sai ya shiga wanka sun bushe sannan ya saka su.

 Also Download: A Sanadin Abayar Salah Complete by Ummu Maher

  Ana haka wataran Alhaji jibrin ya fita neman tai mako gidan wani mai kud'i kawai sai ya jiyo kukan wata jaririya cikin bolar kusa da k'ofar wani gida kamar zai wuce kuma sai ya dawo ya duba yaga jaririya ce aka yar kyakkyawa da'ita kamar y'ar larabawa ya d'auketa hannunshi yana kakkarwa ya nufo gida,yana zuwa gida ya nunawa matarshi Adama mahaifiyar Abdullahi da yake ita kad'ai ce matarshi kuma Abdullahi shi kad'ai ne D'an ta don haka koda Alhaji jibrin ya kawo mata wannan jaririya ba k'aramin jin dad'i tayi ba sosai don haka ta rik'e yarinyar da hannu bibbiyu.

     Abdullahi kuwa duk duniya ya nuna ba shi da wacce ya keso sai Wannan yarinya wacce Alhaji ya saka mata suna Maryam,Tun tana k'arama yake sonta duk abunda ya samo to na k'anwarshi ne Maryam koda ta girma sai abun ya koma soyayya sosai koda iyayen suka gani sunyi murna sosai.

    don haka da taimakon y'an uwa da mak'ota aka hahhad'a akayi musu Aure.

     Ranar bikinsu ne wani mummu nan labari ya samesu'cewae Mota ta buge Alhaji Jibrin ya mutu Har lahira.

      Sunyi kuka sosai da mutuwar mahaifin nasu mai son Su da nuna musu k'auna.

       Koda akayi Auren Inna Adama mahaifiyar Abdullahi tace su zauna agidan tunda gidan yana da girmanshi haka kuwa akayi suka zauna agidan.

      Ana haka wataran Inna adama ciwon ciki ya kamatq cikin dare ko kafin a kaita asibiti tace ga garunku nan ta mutu har lahira tashin hankali sosai Abdullahi da Matarshi Maryam suka shiga,Ana hakane kuma Maryam ta samu Ciki watanshi biyar ya zube saboda rashin kulawa don har yanzu suna cikin talauci sosai.

    Saida Maryam tayi shekara Goma sannan ta haifi Mumtaz wann.

Malam kazo da sauri Mumtaz tana zubar da jini da sauri "Alhaji yace to Mumtaz d'ince babu lafiya yanzu Malam yake fad'amun bari muyi sauru mu tafi Asibiti kiyi sauri ki fito da'ita.

    Umma tayi saurin komawa gida ta fito da Mumtaz suka tafi Asibiti,shan kwanarsu kefa wuya su hancin motarsu Amal ya kawo kai Amal tace Mama kamar Motar Dadyne naga yafita daga gidan kuma naga yana sauri sosai Allah dai yasa lafiya Mama tace to Amin.

   Amal da zumud'inta ta nufo gidansu Mumtaz tana son ta nuna mata kayan da ta suyo akasuwa sai taga gidan Arufe an saka kwad'o ta ce Afili to yau kuma ina su Umma suka tafi dukkansu Allah dai yasa lafiya tayi saurin komawa gida don gayawa Mamanta.

   Likitan tace Alhaji munyi iya k'ok'arinmu don ganin cikin jikinta ya tsira Amman hakan ya faskara sakamakon maganin zubarda ciki da tasha.

   Malam da Alhaji harda Umman Mumtaz saida abun ya tab'asu sosai sakamakon jin wai Mumtaz ce take da ciki ne da'ita to waye yayi mata cikin? suka had'a baki wajen fad'ar hakan likitan kuwa har tayi tafiyarta ta barsu anan sunata sambatu su kad'ai.

   Banko k'ofar da'akayi ne yasa Mumtaz bud'e idonta da k'er don jin yadda sukayi mata nauyi sosai kamar ba jikinta idon yake ba.

    Umma tace Wallahi Mumtaz kin cuceni yanzu daman cikine dake kika d'aukomun abun kunya kinsan kuwa abunda kika Aika ta,yanzu duk i'rin tarbiyyar da muka baki abanza saida kika zubar mana da mutunci yanzu sai ki fad'amun waye yayi miki ciki,eyeh dake nake kike kallona munafuka,Kuka na shigayi ina cewa Wallahi Umma ban zubar muku da tarbiyyar da kuka bani,k'addarace tafad'amun Umma ta k'ara sha k'o Mumtaz tana tambayar cikin d'aga murya wanda duk wanda ke kusa zai iya jin ta.

    Su Alhaji ne da Malam mahaifin Mumtaz suka shigo cikin d'akin saboda yadda suka jiyo hayaniya cikin d'akin,Alhaji yace haba Umma kiyi hak'uri ki k'eleta tayi mana bayani da kanta,Umma ta saki Mumtaz tana haki tare da hararar Mumtaz.

     Alhaji yace Mumtaz ki fad'i tsakani da Allah Muntaz ki fad'a mana waye yayu miki ciki,domin idan kika b'oye mana Allah yana sama yana kallan ki don haka ki fad'ama na kinji.

   Mumtaz  ta share hawayen da ya b'ata mata fuska tace hak'ik'a zan gaya muku gaskiya,Alhaji yace to Mumtaz muna jinki?Muntax tayi shiru tabbas tana son gayawa i'yayenta gaskiya Amman tana tsoron Abubda zaije ya dawo domin tasan Iyayenta baza su tab'a i'ya jayayya da iyayen wanda yayi mata wannan Aika Aikar ba saboda nesa ba kusa ba sunfi duj yadda kake tunani kud'ine dasu kamar Bankin CBN saboda suna da kud'in da ko shugaban k'ada bazai had'a k'afa dasu ba,koda Kuwa Alhaji ne Mahaifin Aminiyarta Amal.

    don haka sai tayi k'arya dacewa,Don Allah Umma ku ya feni hak'ik'a wadannan mutanen da suka saceni wata biyu da ya wuce har nayi tsawon wata biyu agidansu sune suka yimun wannan Aika Aikar mu biyarne y'an mata kuma duk saida suka lala ta mu.

    Alhaji yace to meyasa Mumtaz baki gaya mana ba don mu d'auki mata ki kinga yanzu gashi sun sakaki cikin wani hali muma sun saka mu tabbas biri yayi kama da mutun tabbas  nasan Mumtaz ba mazina ciya ce ba bazata tab'a Aikata abunda kuke zarginta dashi ba.

    Malam ya shard'e wata zufa da ta tasomai yace hak'ik'a nafi kowa sanin halin Mumtaz yarinyace kamila maijin tausayin iyayenta akoda yaushe gata da Addini,hak'ik'a mungodewa Allah da yasa cikin ma ya zube saidai muce Allah ya bata lafiya dukkansu suka Amsa da Amin.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post