[Book] Akan Kanwata Complete Hausa Novel by Ummu Basheer

Akan Kanwata

Title: Akan Kanwata

Author: Ummy Basheer

Compiler: HED Team

Uploader: Zugson

Category: Love Story

Doc Size: 167KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2022

Description: Sauke littafin marubuciya Ummu Basheer mai suna "Akan Kanwata" complete hausa novel a text document kamar yadda aka saba. Za ku iya daukarsa yanzu cikin sauki.

Book Teaser: *Gudu* take yi sosai fatan ta d'aya ta isa gida, da alama daga makaranta take, Dan Uniform ne a jikin ta, shiga gidan tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, da sauri ta d'auki buta ta shiga bayi.

 Wata datijuwa ce ta fito daga wani k'aramin Kitchen tana cewa"Yanzu haka y'ar banzan yarinyan nan ce ta shigo da gudu, kamar...." Maganar ta ne ya katse lokacin da taga ta fito.

 Kallon ta tayi tace" *DEEJA* Allah ya shirye ki, dama nasan kece zaki shigo haka"

Yarinyan da aka Kira DEEJA ta rik'e k'ugu  tace" Ameen shiriya ta addinin musulunci" tayi fari da ido.

Tsaki tsohuwar taja tace" idan kin gama rangwad'a sai ki wuce ki d'auki abinci kici"

DEEJA tace"Cab ai Ina yanzu gidan su lantana zanje, tayi gulma na inji mairo dan haka dole inje inyi maganin ta" 

Tsohuwar tace" Kai wannan yarinya akwai jaraban tsiya, wuce ki cire kayan makarantar tukuna"

Tsaki tayi take" ke fa *INNA* kin cika takura" tana fad'in hakan tayi waje da gudu, Dan dama fitsari ne ya matse ta shiyasa ta dawo gidan.

Sallati INNA tayi tana cewa"Allah ya shirye ki DEEJA"

Gidan su lantana DEEJA ta nufa tana zuwa ta aike wani yaro ya Kira ta, Lantana na fitowa DEEJA ta cakumi wuyan rigar ta tace" Wa na kama, magulmaciya kawai, to Mairo ta fad'a min gulma na da kukayi"

Zaro ido Lantana tayi tana had'iye yawu da k'yar ta hau rantsuwa akan ba ita bace Dan tasan halin DEEJA, yanzu sai tayi mata duka, gashi ita ba k'arfi.

Tsaki DEEJA tayi tace"ki bar wani rantsuwa ne yarinya yau sai kin gane kuren ki" ai Nan ta hau kokuwa da Lantana, sai dambe suke, Lantana da taji a zaba sai ta fara kuka tana ba DEEJA hak'uri, amma Ina ko sauraran ta Bata yi ba, can sai ga wani mutum ya zo wucewa, Nan ya daka musu tsawa amma DEEJA bata bari ba, sai da yayi magana yace" Kai kun ci gidan ku ba magana nake muku ba?"

Rik'e k'ugu tayi tace"yo ai ita ce ta fara tsokana ta"ta murgud'a Baki.

Ganin DEEJA ce yasa mutumin wucewa ba tare da yace komai ba, tsaki taja tace"Shigigi plus gad'are = bitazaizai, ko Ina ruwan shi da mu" juyawan da zatayi sai taga ashe Lantana ta shige gida da gudu, tsaki taja irin zamu had'u d'in nan.

Gida ta koma tana zuwa ta tarar da INNA tana daka, samun guri tayi ta fara murza ido cikin fuskar tausayi tace" INNA yunwa nake ji, Zan mutu"😔

Hararan ta tayi tace"to sai ki mutu in gani"

Kuka ta rushe da shi da k'arfi ta fara cewa"wayyo Zan mutu, jama'a INNA zata kashe ni"

D'aukar mafici INNA tayi ta jefa mata tace" rufe min baki ja'ira"

Da k'arfi tace"wayyo yunwa, *YAYA NA* zan mutu kazo ka cece ni"

Mik'ewa tsaye INNA tayi tace" Yi shiru in d'auko miki kar ki Kira min Yayan Nan naki"

 Da sauri ta mik'a mata abincin, karb'a tayi ta fara ci, can tace"Kai INNA ta kin iya girki fa sosai, sai dai kin cika massifa"

 A fusace tace" Uwa ki ce mai massifar, kiyi min shiru kar ki ishe ni tohm"

 Dai-dai lokacin ne wani Kyakyawan saurayi, fari ne amma ba sosai ba ya shigo gidan, DEEJA na ganin shi ta mik'e tsaye da sauri ta Isa gurin shi tana cewa"oyoyo YAYA NA"

 Murmushi yayi cike da k'aunar k'anwar ta shi yace"oyoyo *K'ANWA TA*, mene ne ya same ki naga idon ki ya canza?"

 Juyawa tayi ta kalle INNA tare da nuna ta da hannu cikin shagwab'a tace"ga ta Nan wannan INNA, sai da taga dama ta bani abinci" ta murgud'a Baki.

Rik'o hannun ta yayi suka zauna kan tabarma yana cewa"INNA ki bar min *K'ANWA TA* ta huta please"

Da sauri DEEJA tace"to kin dai ji koh tsohuwa?"

Dariya INNA tayi tace"naji naji 'yan mata Kuma takwara ta HADIZA"

B'ata fuska tayi tace"YAYA NA kaji ta ko wai nice HADIZA" ta fara kukan shagwab'a.

Da sauri ya fara lalashin ta yana cewa"A'a ba haka sunan ki yake ba, INNA ki gyara kinji INNA?"cikin lalashi.

Murmushi INNA tayi tace" Kai Dan Allah k'yale ni haka, yo idan ba sunan ta bane sunan wace ce haka?" Tashi tayi ta shige Kitchen Dan kawo mai abinci.

DOWNLOAD BOOK


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post